2027:El rufa'i da Peter Obi na Shirin Sauya  Jam'iya za su  shiga SDP----Daniel Bwala

2027:El rufa'i da Peter Obi na Shirin Sauya  Jam'iya za su  shiga SDP----Daniel Bwala

A yayin da ake ci gaba da samun rikicin da ke dabaibaye jam’iyyar Labour Party (LP) da kuma takun saka da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, Daniel Bwala, tsohon kakakin kungiyar yakin neman zaben Atiku-Okowa, ya yi wani ikirari mai cike da cece-kuce game da makomar siyasar Peter Obi.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X (tsohon Twitter) a ranar Juma’a, Bwala ya yi zargin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, na shirin ficewa daga jam’iyyar tare da hada karfi da karfe da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. a jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Bwala ya danganta wannan shirin sauya sheka ne da rikicin da ke tsakanin LP da NLC kan kiran da aka yi na tsige shugaban jam’iyyar na kasa Julius Abure.

Jam’iyyar Labour dai ta sha fama da rigingimun cikin gida, inda kungiyar NLC ta matsa kaimi wajen ganin an tsige Abure a daidai lokacin da ake ikirarin rashin iya tafiyar da al’amuran jam’iyyar yadda ya kamata.

Da yake la’akari da rikicin, Bwala ya ba da shawarar cewa yayin da jam’iyyar LP ke kara zage damtse wajen ganin an tsige Abure da shugabancin kasa a halin yanzu, ana zargin Obi na shirin ficewa daga jam’iyyar tare da hada kai da El-Rufai a SDP.