An Gano Abin da ya Kashe Miji da Mata da Ɗiyansu 5 a Sokoto
Mutane bakwai da suka fito dangin guda sun rasa ransu bayan sun ci abinci da aka yi da Rogo a kauyen Runjin Barmo yankin Kajiji a karamar hukumar Shagari dake jihar Sakkwato.
Kwamishinyar lafiya ta jiha Hajiya Asabe Balarabe ta jagoranci tawaga domin tabbatar da yanda lamarin ya faru, anan ne Malam Muhammadu Magajin Runjin Barmo ya sanar da ita cewa mutanen sun hadu da ajalin su ne bayan sun ci tuwon Rogo da dare.
"Mai gida Malam Abubakar da matarsa Aishatu da diyansu biyar sun rasu bayan cin abincin daren, sun hadu da ajalin su a lokaci guda a gida guda"
Ya ce abin ya faru a Laraba data gabata amma har yanzu ma'aikatar lafiya ba ta fitar da rahoton ko Rogon da suka ci yana dauke da guba ba.
Ya ce wasu mutanen sun ci Rogon amma ba su samu rashin lafiya ko rasa rayuwa ba.
Kwamishiniyar lafiyar ta ce za ta sanar da Gwamna domin daukar mataki na gaba.
managarciya