Kana Fama Da Ciwo Ƙasan Dunduniya Musamman Da Safe?
Ciwon "plantar fasciitis" rauni ne da yake samun rukunin tantanai da ke shimfiɗe a ƙasan tafin sawu. Wannan rukunin tantanai yana aiki ne a matsayin "shock absorber" da ke shanye jijjiga ko girgiza yayin tafiya ko gudu.
Wannan rauni yana faruwa ne yayin da rukunin tantanan aka ɗame su yayin tafiya ko gudu wanda hakan na iya kai ga 'yar yagewa/tsagewarsu da kumburi bayan nan, musamman a tushensu da suka taso daga ƙasan ƙashin dunduniya.
Wannan ciwo ya fi tsanani da safe yayin da aka fara tattakawa domin tafiya.
Waɗanda ke da haɗarin samun wannan ciwo sun haɗa da:
1) 'Yan tsere / masu gudu
2) Masu juna biyu
3) Masu shimfiɗaɗɗan tafin sawu (flat foot).
4) Masu ƙiba /teɓa sosai.
5) Masu sa takalmi coge ko takalman da ke da mashinfiɗi mai taushi ko tauri sosai.
6) Waɗanda suka sauya salon rayuwarsu daga rashin motsa jiki zuwa motsa jiki da ya ƙunshi sassarfa ko gudu da dai sauransu.
Mene ne abin yi da zarar an ji ciwon?
Yayin da wannan ciwo ya dame ka nemi ƙanƙara a naɗe ta a zani ko tawul sai a ɗora tafin sawu a kai tsawon mintina 15 zuwa 20, sannan a cire. Wannan zai rage raɗaɗin ciwon ne.
Sannan bayan an cire tafin sawun daga kan ƙanƙarar a garzaya asibiti domin gani likitan fisiyo.
© Physiotherapy Hausa