AMFANIN JIMA'I A JIKIN DAN ADAM GUDA 9

1. KARFAFA GARKUWAR JIKI-
Binciken wasu masana kimiyya ya nuna cewa, mutane (magidanta) masu yin jima'i akai-akai sunfi yawan sinadarin "antibody" a cikin jikinsu fiye da wanda basu yin jima'i kamar yawan nasu. Shi dai wannan sinadari amfaninsa shine kare jikin 'dan adam daga cututtuka (germs, viruses and other intruders) masu kai farmaki a cikin jiki su cutar da lafiyar garkuwa ga
jikin 'dan adam . Toh saidai yana da kyau
mutum ya yawaita cin abincin dazai kara masa
lafiyar jima'i kamar yanda na bayyana a can
baya wajen abubuwan dake kara dadin jima'i. Kuma mutum ya rinka hutawa don samun cikakkiya lafiya da ni'ima da shaawa.
2. GYARA MANIYYI-
Mutum mai saduwa da iyalinsa akai-akai, ilimi ya nuna cewa maniyyinsa na kara inganci da lafiya. Zaya samu sabon maniyyi ya zubda tsohon maniyyi. Hakan zai iya taimakawa sosai wajen saurin samun juna biyu ga iyalinsa. Haka kuma, sabunta saduwa da uwargida na kara mata sha'awa da ni'imar ruwa (vaginal lubrication) domin saduwa da maigida cikin
sauki da santsi. Wannan rahotone daga wata
mai ilimi akan kiwon lafiya (Assistant clinical
professor of obstetrics and gynecology at Northwestern University's Feinberg School of Medicine in Chicago).
3. RAGE CIWO-
Jima'i na rage radadin ciwo kamar irin na ciwon
jiki ko na baya da sauransu. A lokacin da mutum
yayi inzali(releasing), jikinsa na samarda wani irin sinadari (hormone oxytocin), wannan sinadari yana
taimakawa sosai wajen samarda wani sinadarin
kuma (endorphins) wanda keda tasiri kamar na
maganin "aspirin" da "panadol" (pain relievers)
masu rage zafin ciwo. Jima'i magani me mai
karfi na ciwo. Idan kina so ki gane
gaskiyar wannan zance, a lokacin da kike jin
wani ciwo a jikinki, ki saurara kiji idan akwai
ciwon lokacin kike kawowa (inzali).
4. GYARA ZUCIYA-
Masana kimiyya sun bayyana jima'i a matsayin
wani nau'in motsa-jiki (exercise). Motsa jiki
nada muhimmanci sosai ga lafiyar mutum. Yana
gyara lafiyar zuciyar 'dan adam da kuma kare ta daga cututtuka masu kai farmaki. Yana sanya gudanar jini a zuciya da sauran jiki yanda ya kamata domin samun cikakkiyar lafiya.
5. RAGE HAWAN-JINI -
Abisa wasu bayanai masu inganci da muka
tattaro na wasu masana kimiyya, yin jima'i tsakanin ma'aurata na taimakawa wajen rage hawan-jini a lokacin da yake hauhawa.
6. HUCE WAHALA-
Idan maigida ya dawo aiki ya shawo wahalar
aikin ofis, ta kasuwa ko wata wahala mai wuyar
gaske kuma ya naso ya huta, toh sai yayi
wanka, yaci abinci, ya kuma sha ruwa ko lemu,
sa'annan ya sadu da iyalinsa. Ko shakka babu
zai samu wani irin hutu da bacci mai dadi da kuma
debe wahala. Jima'i na rage 'stress' da
'pressure' sosai.
7. RAGE KIBA-
Yawan jima'i nasa rama. Kada mu manta da
cewa jima'i wani nau'i ne na motsa-jiki.Yana kone sinadaran kuzari (calories) wanda taruwarsu da yawa a jiki ba tare da amfani dasu ba ke jaza kiba (weight gain). Jima'i na tsawon rabin awa na kone/amfani da kimanin 75 ko 150 na sinadarin. Anyi kiyasin cewa mutum na kone sinadarin kimanin 129 yayinda yake tafiya a kasa tsawon rabin awa.Yawan kiba nada illa sosai ga lafiya. Yana haddasa ciwuka kamar na zuciya, ciwon suga da ciwon kafafu ko gabbai. Toh masu kiba ga wata dama ta samu -Jima'i hanyace ta rage kiba.
8. GYARA FATA-
Fata tayi kyau da kala mai kyau mai alamun lafiya tana sheki, hudojin gashi suyi yar yar... musamman ga mata, saboda maniyyin da kika samu daga mai gida bama kamar ace yana da yawan maniyi.
9. GYARA MAFITSARA-
Yana gyara lafiyar mafitsarar mata domin rike
fitsari da sauransu dai mutakaita. Allah shi bamu lpia danikon samun jima'i cikin koshin lafiyar....