Ka san me takalminka ke cewa game da gaɓoɓin ƙafarka?

Ka san me takalminka ke cewa game da gaɓoɓin ƙafarka?

Wurin da ya fi ɗaukan nauyi a tafin sawu nan ne zai fi kashe takalmi da wuri. Kuma kowane tafin sawu na iya kashe takalmi daban da ɗaya tafin sawun. Hakan na faruwa gwargwadon bambancin taku da ke tsakanin tafukan sawu. 

Saboda haka, yadda takalmi ke mutuwa na nuni da muhimman bayanai kan yadda gaɓoɓin jiki ke rarraba nauyin jiki.

Wani ya fi saurin kashe takalmin dama, wani kuma na hagu. Kamar yadda wani ya fi kashe dunduniya — gefen ciki ko waje, wani kuma ya fi kashe tsakiyar takalmi ko kuma babban yatsa.

Bambancin kashe takalmin dama da hagu na nuni da bamabancin aikin gaɓoɓin ƙafafu zuwa tafukan sawu.

Cutuka ko tawayar gaɓoɓi kamar  ciwon gwiwa, cassa / gwame, shimfiɗaɗɗen sawu da sauransu na daga cikin matsalolin da ke janyo kashe takalmi saɓanin yadda ya kamata.

Idan ka lura akwai bambanci sosai kan yadda kake kashe takalamin dama da hagu, tuntuɓi likitan fisiyo domin tattaunawa kan lamarin. Domin hakan na nuni da wata gaɓa a jiki na aiki ba daidai ba.