'Yan Bindiga Ba Su Yi Yunkurin Kai Hari A Kwalejin Kiyon Lafiya Ta Gwadabawa Ba----Shugaban Makaranta

'Yan Bindiga Ba Su Yi Yunkurin Kai Hari A Kwalejin Kiyon Lafiya Ta Gwadabawa Ba----Shugaban Makaranta

 

Shugaban kwalejin kiyon lafiya ta Gwadabawa Alhaji Nasiru Gwadabawa ya karyata jita-jitar da ake bazawa a kafofin sada zumunta cewa mahara na kokarin kaiwa makaratar hari har  sau uku ba a samu nasara ba.

Shugaban ya ce wannan bayanin karya ne da kokarin samar da tashin hankali a cikin al'umma ba wani abu mai kama da wannan.

Ya ce wadan da ke yawo da wannan karyar in sun tayar da hankalin mutane miye ribarsu a haka, su fito da zancen karya da ba a yi ba, yakamata su ji tsoron Allah su rika bayar da zancen gaskiya da zai kawo kwanciyar hankali da cigaban al'umma.

Shugaban bai musanta 'yan bindiga sun shiga garin Gwadabawa ba, sai dai ba su je makarantar ba, ya ce suna kokarinsu kwaran gaske tare da jami'an tsaro su tabbatar da kare dalibbai da ma'aikatan makarantar.