Akwai bukatar Sakkwato ta aiwatar da dokar Lafiya ta 2014---Shugaban Gidauniyar Sake fasalin Lafiya Na Nijeriya

Akwai bukatar Sakkwato ta aiwatar da dokar Lafiya ta 2014---Shugaban Gidauniyar Sake fasalin Lafiya Na Nijeriya
 

An sake nanata bukatar da ake da ita  na yin cikakken amfani da dokar lafiya ta kasa ta shekaru ta 2014  a jihar Sakkwato. 

Shugaban Asusun kyautata tsarin kiyon lafiya ta kasa  reshen jihar  Malam Bello A. Bello yayi wannan kiran ne  lokacin wata ziyarar neman goyon baya da ya jagoraci kaiwa ga masu ruwa da tsaki dake  fannin lafiya a Sakkwato a satin da ya gabata.  
Ya ce yin hakan zai taimaka ma masu karamin karfi wajen samu ayukan kiyon lafiya acikin sauki. 
Ya ce wannan ziyarar da suka kawo sun yi ta ne bisa muhimmancin dokar wajen maganin matsalolin da ake samu wajen ayukan kiyon lafiya a tsakanin jama'a. 
Yayinda yake yabama gwamnatin jaha kan aiwatar da wasu sassa na dokar da suka hada da kirkirar  hukumar kula da ayukan kiyon lafiya a matakin farko da Asusun Karo Karo ga ayukan kiyon lafiya, shugaban ya nemi mayar da dokar daidai da karantarwar  addinin al'ummar jiha . 
A nasa jawabi Manajan Asusun daga hidikwata a Abuja Dakta Opeyemi Adeosun ya bada shawarar wakillan kwamitin da gwamnatin jiha ta kafa kuma ta kaddamar da su don   su bibiyi tanade tanaden dokar don ya yi daidai da raayin jama'ar  jiha. Dr Adeosun ya nanata bukatar da ake yi wa majalisar dokoki ta jaha data yi bitar dokar da kuma yimata sunan dokar lafiya ta Sakkwato ta shekara 2022.  
Manajan Asusun ya kuma yi fatar cewa gwamnan jaha zai samata hannu da zaran an kawo masa. 
Da yake jawabi Shugaban Maaikata na jaha Malam Abubakar Muhammd, ya basu tabbacin cewa Gwamnatin jahar a shirye take ta goyi bayansu don samun nasarar bukatar da aka sanya a gaba.  
Malam Abubakar Muhammd, yace Gwamnatin  Sakkwato a shirye take ta goyi bayan duk wata kungiyar dake son taimakawa ga ayukan kiyon lafiya a jahar.  
Ya ce tuni da gwamnatin jaha ta kafa hukumomi biyu masu alaka da hakan.