DSS Ta Bukaci 'Yan Jarida Da Su Sanya Kishin Kasa Yayin Gudanar Da Aikinsu

DSS Ta Bukaci 'Yan Jarida Da Su Sanya Kishin Kasa Yayin Gudanar Da Aikinsu
 
Daga Ibrahim Hamisu, Kano.
 
Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS kwamanda Hassan I. Muhammad ya bukaci  Yan Jarida da su hada kai da hukumar wajen Samar da tsaro da hadin kai da zaman lafiya a Nigeriya,
 
Daraktan ya yi wannan Kiran ne yayinda ya ke karbar bakuncin shugannin da membobin kungiyar Yan Jarida masu yada labarai a shafukan sadarwa na zamani  a ranar a yau Laraba, 
 
Hassan I Muhammad ya ce  kafar yada labarai ta internet kafa ce mai sauki, da ake yada labaran karya da ke haddasa rudani da tarzoma a cikin al'umma,
 
Ya ƙara da cewa samuwar kungiyar ƴan jarida masu gudanar da ayyukan su a shafukan intanet ba na kokonto zai taimaka wajen shawo kan matsalolin tsarom da gwamnatin ƙasar nan ke ci gaba da yaƙi da su.
 
” Dama dai mun daɗe muna jiran irin wannan lokaci da za a samar da wata inuwa da za ta haɗa kawunan ƴan jarida wajen gudanar da ayyukan da ya kamata”.
 
”Ta hanyar wannan kungiya nasan za ku iya bayar da gudummawa wajen samar da sahihan labarai kuma ingantattu ga jama’a.” In ji Hassan I. Muhammad
 
A nasa ɓangaren muƙaddashin shugaban ƙungiyar Malam Yakubu Salisu, ya ce sun kai ziyarar ne domin gabatar da ƙungiyar ga hukumar ta DSS domin yin aiki kafaɗa da kafaɗa wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban al’ummar jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
 
Yakubu Salisu ya ce makasudin kafa kungiyar shi ne tsaftace harkar yaɗa labarai a shafukan intanet tare da yaƙi da labaran ƙarya da kuma kalaman ɓatanci.
 
 
Daga nan Darakta Hassan I. Muhammad ya ja hankalin mambobin ƙungiyar da su zamo masu bin doka da oda a lokacin da suke gudanar da ayyukansu tare da sanya kishin ƙasa domin samun zaman lafiya da cigaba mai dorewa.