Ɗas-ɗas kake ji a gwiwarka yayin miƙewa ko lanƙwashewa?
Jin sautin ɗas-ɗas a gwiwa yayin miƙe ko lanƙwashe gwiwa na iya sanya mutum cikin damuwa ganin cewa bai kamata lafiyayyiyar gwiwa take bayar da wannan sauti ba.
Ana iya jin wannan sauti yayin ayyukan yau da kullum. Wani lokacin ma ko da kana zaune ko kwance kana iya jin sautin idan aka miƙe ko lanƙwashe gwiwar.
Sai dai, sau da yawa wannan sauti ba ya zuwa da ciwo. Amma maimaituwar miƙe ko lanƙwashe gwiwar tsawon lokaci na iya haifar da ciwo a wani sashi a gwiwar.
Wannan sauti, ana iya jin sa a gwiwa guda ne, amma wasu lokutan na iya kasancewa a gwiwa biyun dukka.
sabuba da yawa ne ke janyo jin wannan sauti a gwiwa. Sabuban sun haɗa da:
1. Gajercewa ko ɗaurewar tsokokin da ke aiki a kan gwiwa, wato tsokokin cinya.
2. Fashewar gurunguntsin gwiwa.
3. Fashewar gammom gwiwa
4. Gugar ƙashi da igiyoyin tanani waɗanda ke aiki kan gwiwa, da dai sauransu.
Ana iya jin sautin a wurare ko ɓangarori na gwiwar kamar; gefen ciki, gefen waje, ƙoƙon gwiwa, bayan gwiwa ko kuma cikin gwiwar. Kana iya gane daga wanne ɓangare yake zuwa idan ka kasa kunne sosai ko kuma idan ka sanya hannunka a ɓangaren da ka fi zaton daga nan sautin ke zuwa.
To jin sautin na nufin matsala ne?
Kamar yadda aka ambata, sau da yawa sautin ba ya zuwa da ciwo. Sai dai jin sautin na nufin akwai tirjiya a wani sashi na gaɓar gwiwa. Haka nan, sautin na iya zama alama ce ta sonsomin wata matsala a gwiwa.
To ana iya daina jin sautin? Tabbas ana iya daina jin sautin bayan an bincika, an gano, sannan aka magance sababin.
Idan jin sautin ɗas-ɗas ya zarce da ciwo ko kuma kana damuwa da jin sautin, tuntuɓi likitan fisiyo.
managarciya