Jega da wasu manyan ƙasa sun kafa jam'iyar da ake son ta kawarda APC da PDP
RNP: Sabuwar Jam'iyyar Da Su Jega, Pat Utomi, Abdulfatai, Duke, Dakta Bugaje Da Sauransu Suka Kirkiro
RNP: Sabuwar Jam'iyyar Da Su Jega, Pat Utomi, Abdulfatai, Duke, Dakta Bugaje Da Sauransu Suka Kirkiro
Jam'iyyar mai suna 'Rescue Nigeria Project', wadda su tsohon gwamnan Kwara, Ahmed Abdulfatai, Prof. Pat Utomi, Prof. Tunde Adeniran, tsohon gwamnan Cross River, Donald Duke suka kirkiro, ana ganin za ta iya zama babbar kishiya ga manyan jam'iyyu irin su APC da PDP.
Sauran wadanda aka kirkiri jam'iyyar da su, sun hada da Sanata Lee Maeba, Usman Bugaje, Prof. Attahiru Jega, Amb. Nkoyo Toyo, Yomi Awoniyi, Dr. Rose Idi Danladi, Dr. Sadiq Gombe da sauransu.
An kafa jam'iyar da zimmar kawar da APC da PDP kan mulki ganin sun kasa kawo wani cigaba ga talakan Nijeriya.
Manyan da suka kafa sabuwar jam'iyar suna ganin ya kamata a kawar da manyan jam'iyyun domin ba abin da suka kawowa ƙasar Nijeriya sai ci baya, in kuma aka bari suka cigaba da zama a madafun iko ƙasar za ta cigaba da komawa baya.
managarciya