Shaikh Albani Ya Hango Masifar Janye Tallafin Fetur Shekaru 9 da Suka Wuce 

Shaikh Albani Ya Hango Masifar Janye Tallafin Fetur Shekaru 9 da Suka Wuce 

A wani fai-fen bidiyo da yake yawo a kafofin sada zumunta, an ji yadda Marigayi Muhammad Auwal Adam ya yi maganar cire tallafin fetur.

A wani karatu da ya yi, Legit.ng Hausa ta ci karo da inda Sheikh Muhammad Auwal Adam wanda aka fi sani da Albani Zariya ya fadakar da mutanen Najeriya musifar da za a shiga in aka janye tallafin man fetur.
A wancan lokaci, Sheikh Albani Zariya ya ce muddin gwamnatin tarayya ta daina biyan tallafin fetur, za a shiga musibar tsadar da ba a taba gani a tarihi ba.
Malamin yake fada shekaru kusan tara da suka wuce cewa sai mutanen kasar sun raina kansu idan aka janye tsarin, ya yi kira da masu fada su tashi-tsaye. 
Albani ya ce ya zama dole ‘yan boko da ‘yan gwagwarmaya su hana cire tallafin da ake mora, ya ce idan ba haka aka yi ba, an gurgunta jama’a da tattalin arziki.
Shehin ya kamanta tashin man fetur da zaluncin shugabannin kasashe irinsu Tanzaniya da Masar, har ta kai ‘yan mata na lalata saboda su samu abinci. 
Babban malamin addinin ya zargi gwamnati da kawo manufar a lokacin saboda karya adawa, a cewarsa mutane na cikin kunci a mulkin Goodluck Jonathan.
A cewar Albani, tsohon Shugaba Ibrahim Babangida ya kawo irin tsare-tsaren domin karbo bashi a hannun manyan Duniya, amma wasu su ka taka masa burki. 
"Su talakawan kasar ba su san fassarar wannan abin ba, ba su san ma’anar shi ba sai sun ji a jika. Amma duk ‘dan boko ya san me ake nufi da janye tallafi. Kuma duk Duniya, kowace kasa ta na tallafawa ‘yan kasarta da abin da ke shigowa domin a samu sauki. Balle abin da arzikinku ne, arzikinku a ce ba za a tallafa maku ba. A lokacin da karuwai ne a yau ake kai wa Neja-Delta, ana yi masu kyautar rijiyar man fetur." 
Mashahurin malamin ya bada misali da malamin jami’a irinsu Shehu Umar, ya ce a yau babu tamkarsa da masu kare hakkin Bil Adama da za su kare al’umma. Saboda haka wajibi ne ‘Yan Boko ku tashi, ‘yan boko ne su ka tsara abin da ya faru a kasar Masar, Albani ya zaburar da malaman Najeriya su kawo sauyin yanayi. 
Yau bayan rayuwar Albani an janye tallafin duk abin da ya fadi mutane sun ganshi a fili, saura da mi malamai dake raye su tashi tsaye don ganin an sake mayar da wannan tallafin domin shi kadai ne mafitar da talaka zai samu saukin rayuwa.