Na Yi  Wa Matar Maƙwabcina Ciki Saboda Shi  Raggo Ne'

Na Yi  Wa Matar Maƙwabcina Ciki Saboda Shi  Raggo Ne'
Na Yi  Wa Matar Maƙwabcina Ciki Saboda Shi  Raggo Ne'
'Na Yi  Wa Matar Maƙwabcina Ciki Saboda Shi  Raggo Ne'
Wani mutum ya ɗirkawa matar maƙwabcinsa ciki har ta haihu ya ce makwabcinsa raggo ne
Wani magidanci mai suna Tineyi Lavite Tapfumaneyi ya ɗirka matar maƙocinsa ciki har ta haihu.
Mijin matar mai suna Murambiwa Murangariri ya kai ƙara kotu inda ya nemi a tursasawa maƙwabcin nasa, Tineyi biyan diyyar dala Miliyan $4.5.
Yace abinda maƙwabcin nasa ya yi ya kawo ruɗani a gidansa.
Murambiwa ya ce a baya maƙwabcin nasa ya taɓa yin lalata da matarsa, inda har yake gaya masa baƙar magana ta cewa wai shi ba cikakken namiji ba ne.
Yace ya kai shi kotun gargajiya inda aka ci shi tara ashe bai daina bin matar tasa ba. Yace shi da matarsa da suke da yara 4 aurensu ba zai taɓa dawowa daidai ba.
Wanda ke  ƙarar ya shaidawa kotu  ƙwabcinsa na bin matarsa ne saboda ya ce shi raggo ne.