Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.
Karamin kwamitin lafiya na kwamitin Bada Tallafin na Musamman na Gidauniyar Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto ya Kammala zagayen Kananin Hukumomin Jihar Sokoto 23.
Shugaban karamin kwamitin ne Malam Kabiru Shehu Binji ya bayyana hakan jin kadan da Kammala zagayen Wanda akayi a Cibiyoyi Shidda da ke fadin jihar Sokoto , da suka hada da cibiyar yada Addinin musulunci ta IET da ta kumshi kananin Sokoto ta Arewa,ta kudu,Wamakko,Dange Shuni,Tureta,Bodinga da Rabah Yayin da Cibiyar Goronyo ta kumshi cibiyoyin kananin hukumomin Goronyo, Isa, Wurno,da Sabon Birni, Yanyinda cibiyar Tangaza da ke gidan madi ta kumshi Tangaza,Silame,Binji,Gudu, da kware, itakuma cibiyar Tambuwal da ke da Kananin hukumomin Tambuwal, Kebbe,Yabo, da Shagari inda gundumomin da ke kananin hukumomin Gwadabawa, Illela,da Gada sukayi a cibiyar Gwadabawa
A dukkan Cibiyoyin an gudanar da tantancewar cikin nasara, bayan da kwamitin mutun hudu na kananin hukumomin suka zakulo Dalibbai Goma Goma dan rubutawa da fitar da zakarru mutun hudu. Malam Aminu Bello Gwadabawa, Alh Isa mai alewa daga Goronyo da Gwadabawa suka bayyana cewa sun zakulo Dalibban ne biya amanar da aka basu. Wasu Dalibban sun yi godiya da fatar Samun nasara.
Malam Kabiru ya bayyana cewa a daukacin cibiyoyin anyi jarabawar ce ta Lissafi da kuma Harshen turanci. Yayi godiya ga babban kwamitin karkashin Malam lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato da suka ba su damar gudanar da aikin, inda ya yabawa Gwamnatin jihar Sokoto akan hidimar da takewa Addini da Alummah. Shugabannin kananin Hukumomin Goronyo da Gwadabawa da Wakilin Uban kasar Tambuwal,sun yi godiya ga Tsohon gwamnan Sokoto Dr. Attahiru Bafarawa akan wannan aikin.
Kwamitin na Mutun 7 Wanda ya kumshi wakilan Nana Girls, Kungiyar Maaikatan lafiya Musulmi IMAN, da sauran su. Suka gudanar da tantancewar ta tsawon mako daya