Kotu ta yanke wa matashi hukuncincin wankewa matan garinsu tufafi tsawon wata 6
Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin wanke tufafin matan dukkan garinsu har tsawon wata shidda kan ya yi yunƙurin yi wa wata yarinya fyaɗe.
Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin wanke tufafin matan dukkan garinsu har tsawon wata shidda kan ya yi yunƙurin yi wa wata yarinya fyaɗe.
Alkalin kotun dake zamanta a Jihar Bihar na kasar Indiya, ya ce matashin suna Lalan Kumar zai kuma riƙa goge kayan matan su kusan 2,000 a ƙauyen na Majhor dake Jihar ta Bihar.
Kotun ta kuma bayyana cewa matashin mai shekara 20 zai riƙa amfani da kuɗinsa wajen sayen sabulu da duk abin da ake buƙata a wanki da goge kayan matan garin nasu.
Alƙalin kotun ya bayar da umarnin ne a lokacin bayar da belin Kumar – mai ke sana’ar wanki da guga – wanda aka gurfanar a gaban kotun.
Jami’in dan sandan mai kula da yankin Madhubani da ke Jihar Bihar, Santosh Kumar Singh, ya ce an gurfnar da Kumar ne a kotun bisa zargin yunƙurin aikata fyade
Dagacin ƙauyen, Nasima Khatoon, ya bayyana hukuncin kotun a matsiyin mai dimbin tarihin da zai kare martabar mata.
Dagacin ya bayyana cewa matan garin Majhor sun bayyana farin cikinsu da hukuncin.
Matan sun ce hukuncin zai ba da damar mahawara a kan laifin cin zarafin su a cikin al’umma da kuma kare martabar su, kamar yadda jaridar Aminiya ta labarto.
managarciya