Mi Ya Sa Tambuwal Zai Fifita Shekarru Saman Kwarewa A Mukin Nijeriya?

Mi Ya Sa Tambuwal Zai Fifita Shekarru Saman Kwarewa A Mukin Nijeriya?

Gwamnan kwato Aminu Waziri Tambuwal ya shawarci mutanen Nijeriya kar su yarda su zabi tsoho wanda ya haura shekara 60 a zaben 2023 dake tafe.

Tambuwal wanda a yanzu yana da shekara 56 ya nuna sha'awarsa ta tsayawatakarar shugaban kasa a cikin jam'iyar PDP.
Ya maganta a jihar Jigawa a ranar Talata data gabata a lokacin da kungiyar dalibbai na jihohin Arewa 19 suka goyi bayan takararsa.
Kwamishinan matasa da wasanni Bashir Gorau ne ya wakilci gwamnan ya ce matasa ne ke da kasar Nijeriya duk mutumin da ya wuce shekara 60 yakamata ya fuskanci ubangijinsa, ba wai ya rika kallon yanda zai shugabanci kasa ba.
Ya ce akwai bukatar samun shugaban kasa da yake  da kuzarin da zai iya zagaye kasa a yini domin samun sahihan bayanai ba wanda zai rungume hannuwa zaune a ofis yana jiran bayanai wurin mutane ba. 
Karancin shekarru da kwarewa wane ne yafi dacewa da bukata awurin mutane ga shugaban da zai jagorance su, ganin yanda jagoranci yake amana ce.
Managarciya na ganin Kwarewa ce aka fi bukata a wurin shugaba, domin kusan duk wani jagoranci da ya yi kasa ba a samu cigaban da ake bukata ba, kwarewa ce babu.
Da yawan shugabannin da ke da shekarru ana samu biyan bukata a jan ragamarsu a lokaci daya ana samun ci baya a wurin masu kananan shekarrun da ba su da kwarewa. A hakan muke kallon yakamata a rika kallon kwarewa da fifita ta kan shekarru domin samun nasarar jagoranci.