Mutane Sun Kashe Dan Bindiga Tare Da Karbo Dabbobi 150 A Sakkwato

Mutane Sun Kashe Dan Bindiga Tare Da Karbo Dabbobi 150 A Sakkwato

Mutane Sun Kashe Dan Bindiga Tare Da Karbo Dabbobi 150 A Sakkwato

 

Fusatattun mazauna ƙauyen Giyawa a yankin ƙaramar hukumar Goronyo ta jihar Sakkwato sun tura wani hatsabibin ɗan bindiga zuwa lahira. 

Jaridar Leadership ta rahoto cewa mutanen ƙauyen sun halaka ɗan ta'addan ne da sanyin safiyar ranar Lahadi da ta wuce kuma sun kwato dabbobi 150 da aka sace. 
Rahotanni daga bakin mutanen yankin sun nuna cewa mazauna Giyawa sun hana ɗan bindigan wucewa ta garinsu, a hanyarsa ta zuwa dajin Goronyo mai hadari.
An ce ɗan bindigan ya gudo ne daga ƙauyen Samana da ke ƙaramar hukumar Binji da nufin zuwa mafakarsu a dajin Goronyo, da zai ratsa ta ƙauyen Giyawa ya gamu da ajalinsa. 
Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta bayyana cewa a baya-bayan nan, 'yan bindiga sun kashe mutane huɗu, sun yi garkuwa da wasu 18 tare da sace tulin dabbobi a garin Giyawa. 
Yayin da aka tuntuɓi muƙaddashin jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sanda reshen jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa'i, bai ɗaga ƙiran da aka masa ta wayar tarho ba. 
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ba a samu kakakin hukumar 'yan sandan ba domin jin ta bakinsa kan lamarin a hukumance, premium times ta ruwaito. 
Jihar Sakkwato da maƙociyarta Zamfara na cikin jihohin shiyyar Arewa maso Yamma da suke fama da hare-haren ta'addancin 'yan bindigan daji a ƙasar nan.