Daga Aminu Amanawa a Sakkwato.
Lamarin tashin gobarar dai ya soma ne a ranar lahadin data gabata 9 ga watan Janairun 2022, a kauyen Tsaki dake karamar hukumar mulkin Kware a Sakkwato.
A cewar daya daga cikin mazauna kauyen na Tsaki Alhaji Mode gobarar ta soma ne tun a ranar lahadi, in da ta tashi a daya daga cikin gidajen dake wannan garin.
“Washe gari tun da safe wutar ta sake tashi a wani gidan, an jima kadan kuma muka sake ganin ta tashi a wani gidan, muna tsaka da kashin wutar ta kuma sake tashi a wanin gidan, in takaice maka a wannan ranar sai da gobarar ta tashi a kalla a gidaje 14 na wannan kauyen na Tsaki, kuma tashin ta ya sanya mu asarar dinbin dukiya, domin taci gidaje, shaguna, da ma danga masu yawa”.
Dattijon mai shekara 60 ya ce, a wayon sa, ana samun tashin gobara amma bai taba ganin gobara mai ban al’ajabi ba irin wannan.
Shi ma da yake magantawa da wakilinmu da ya ziyarci kauyen na Tsaki, uban kasar Tsaki Muhammadu Mai Akwai, ya bayyana kaduwar sa, na samun tashin gobarar da suke fuskanta.
“Abin dake da babban mamaki a wannan gobarar da ake samu a wannan kauyen shi ne, ko wace gobarar da take tashi daga wannan gidan zuwa wancan, sam bata da alaka da ko wace, domin in da wannan ta tashi anan ake kasheta, sai kuma ka ji ta sake tashi a wani wajen daban," in ji basaraken yankin.
Ya cigaba da cewa Kodayake yawaitar tashin gobarar wasu na alakanta shi da Aljannu saboda sarar itace da ake zargin mutanen kauyen ma yi ba bisa ka'ida ba.
Amma uban kasar Tsaki ya ce sam ba haka lamarin yake ba.
“Ba gaskiya ba ne wannan gobarar daga Allah ne, domin haka kawai za’a ga gobarar ta tashi, ba abinci aka dafa ba balle ace shi ne musabbabi, sannan kuma ba wutar a kasa, duk inda ta kama takan faro ne daga sama, don haka wannan lamarin daga Allah ne, kowa na fadar albarkacin bakin shi ne kawai, wai an sari wani icce, sam mu bamu gani ba, dan haka ba mu da tabbaci akai”.
Domin samun saukin lamarin ibtila’in tuni da Uban kasar ya bayyana tara dukkanin Almajirai da Malamai domin sauke Al’kur’ani mai girma domin sauki daga ubangiji, tare da kira ga gwamnatin jihar Sokoto data kawo masu dauki kan halin da suka tsinci kansu a ciki.
Daga ranar da lamarin ya faru zuwa lokacin da wakilinmu ya ziyarci kauye, alkalumma sun nuna da cewa an samu tashin gobara 30, tashin gobarar guda biyu sun faru ne a gaban idon wakilin namu, inda mutanen kauyen ke neman agaji na ruwan da za’a kashe ta, yayin da wasu ke faman buge ginin laka domin kai agajin gaggawa.
Hakama wakilin mu ya lura da yanda kauyen ke da wadataccen ruwa abin da kan taimaka masu wajen kashe gobarar da zarar ta tashi.
Baya ga wannan ma mutanen kauyen tuni da wasu daga ciki suka fara fitar da kayayyakin su waje, domin tashin gobarar da zata iya lakume masu abubuwan amfanin yau da kullum.
Ba kasafai dai ake samun irin wannan ba, koda yake wasu na canfa aukuwar hakan da tsafi da makamantansu.
Sheikh Yusuf Yahaya Alibawa, malamin addini ne a Sakkwato ya ce sabon ubangiji da al’umma ke yi shi kansa na iya zama dalilin samun wannan ibtila’in.
“Idan aka wayi gari da samun irin wannan, to musulman wannan zamanin su waiwayi kansu kan irin ayukkan da suke aikatawa an ya ba su sabawa mahaliccin su ba? Idan ya ba su umarni su yi ko su ki yi, ko kuma ya kasance suna aikata abinda ya hana bayinsa da aikatawa, domin Allah na jarabar ‘yan Adam kamar yanda ya jarabi Annabawa, domin ya jarrabi annabawa dan ya auna karfin imanin su, badan sun aikata zunubi ba, kamar Manzon Allah S.A.W ya tafi wajen yaki yasha wahala duk wannan jarabawa ne, hakama wasu annabawa sun tafi wajen Da’awah sun samu jarabawa irin su Annabi Zakariya, Annabi Nuhu, Annabi Ibrahim AS, to amma mu a wannan lokaci duk abinda yafaru damu to sabon Allah ne yasa hakan ta faru”.
justify;">
Malamin ya ce idan har zamu dawo mubi dokokin Ubangiji to Allah S.W.T zai kuranye mana wadannan bala’oin, kuma duk lokacin da irin wanna ya faru to mu kara komawa ga Allah domin neman sauki a wajen sa.