@Ramadan: Ya dace Tambuwal Ya Dauki Nauyin Sanya Kiran Sallah Da Tafsiri A Kafafofin Yada Labarai Na Arewa?

@Ramadan: Ya dace Tambuwal Ya Dauki Nauyin Sanya Kiran Sallah Da Tafsiri A Kafafofin Yada Labarai  Na Arewa?

 

Gwamnatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ta dauki nauyin sanya kiran sallah da tafsirai a gidajen rediyo da talabijin a fadin watan azumin Ramadan ta hannun ofishin mai baiwa gwamna shawara kan harkokin yada labarai.

A wani bayani da mai baiwa gwamnan shawara ya fitar yake sanar da mutanen Nijeriya cewa a watan Azumin Ramadan Gwamna Tambuwal ya amince a dauki nauyin sanya Tafsirai da wasu littafan addini da kiran sallah a wasu kafafen yada labarai. 
 
Gidajen Rediyo da zu sanya kiran sallah daga Azahar har zuwa Isha'i Vision FM Sokoto, Garkuwa FM Sokoto, Royal FM Sokoto, Rima Radio Sokoto, Caliphate FM Sokoto, Vision FM Abuja, FRCN Kaduna.
 

Gidajen Ridiyo da za su sanya  Tafsir FRCN Kaduna Tafsir  Shiekh Dahiru Bauchi,  Arewa FM Kano Mallam Mahmoud Muhammad, Peace FM Maiduguri- Sheikh Modu Mustapha. 

 
Gidajen Talabijin da za su sanya Tafsir da Tarawihi a Makka, NTA Sokoto, Rima TV Sokoto, Farin Wata TV Abuja: Sheikh (Dr) Muhammad Sani Rijiyar Lemo, NTA Kano: Sheikh Ibrahim Daurawa, NTA Kaduna Tafsir by late Sheikh Jafar Mahmoud Adam da Sheikh Sheriff Ibrahim, NTA Jalingo: Sheikh Abdullahi Abbare, NTA Maiduguri: Dr Muhammad Alhaji Abubakar,  Hijrah TV  Sheikh Tukur Sani Jangebe,  Almanara TV- Sheikh (Dr) Abubakar Sani Birnin Kudu, NTA Hausa Tafsir  Prof. Ibrahim Maqari, Central mosque, Abuja.
 
Sai kuma Al’umma TV Gusau, Zamfara  Sheikh Ahmad   bin Umar Kanoma, NTA Channel 5 Abuja, Kaftan TV-  Sheikh Kabiru Haruna Gombe, ARTV Kano: Mallam Mahmoud Muhammad. 
 

Wasu na ganin kashe wadan nan makudan kudi da aka yi a ofishin mai baiwa gwamna shawara abu ne da ya dace domin watan azumi ana son a yi abubuwa na lada da  addini ya aminta da su, wannan kuma karfafawa ne ga gidajen yada labaran.