Hon. Abdussamad Dasuki: Irin Jagoran Da Al'ummar Sakkwato Ke Bukata

Shakka babu a 2023 Tambuwal na bukatar gogaggen dan siyasa irin Hon. Abdussamad Dasuki wanda zai dora daga inda ya tsaya, wanda ke da cikakken ilimi, gogewa da wayewar iya hulda da magana da kowa a ko'ina a duniya wanda ya san ciki da wajen Nijeriya wanda ke da hanyoyin kawo masu zuba jari domin habaka tattalin arzikin Jiha wanda ke da gagarumar karbuwa ga al'umma wanda hatta 'yan adawa sun yadda da zamansa nagari na kowa wanda kuma a ke da tabbacin zai baiwa marada kunya ta hanyar gudanar da amintaccen shugabancin da al'umma za su yaba tare da cewar gwamma da a ka yi. 

Hon. Abdussamad Dasuki: Irin Jagoran Da Al'ummar Sakkwato  Ke Bukata

 

Daga, Magaji Sarki

 

Babban dalilin da ya sa jama'a ke kuka da kokawa da irin jagororin da ke jagorantar su a mabambantan madafun iko tun daga kan matakin Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jiha da Kananan Hukumomi bai wuce rashin samun adilai, jajirtattu kana hazikan shugabanni masu gaskiya, adalci da son ci-gaban jama'a ba wadanda a kodayaushe ci-gaba da bunkasar al'ummar su ne babban abin da suka sa a gaba ba wai arzuta kan su da makusantan su ba.

 
Galibi a Nijeriyar yau talakawa da mafi yawan wadanda a ke mulka na korafi da Allah-wadai da jagorinsu ne a dalilin rashin sauke nauyin da suka dora masu bayan zazzaga masu ruwan kuri'a a akwatin zabe ta yadda a kodayaushe suke kwadayi da muradin samun 'yan siyasar da za su rika shayar da su cikakken romon mulkin Dimokuradiyya. 
 
Idan har siyasa na nufin hanyar da mutane ke bi wajen tafiyar da rayuwa a tare ko a kungiyance domin cimma manufa daya tare da kulla wata yarjejeniyar ci-gaban jama'a; haka ma idan har an fassara Gwamnati a matsayin Gwamnatin jama'a ta jama'a domin jama'a to kuwa ya kamata a rika yi wa jama'a adalci na samun nagartattun shugabanni masu gaskiya da amana wadanda ke fifita ci-gaba da bunkasar al'umma a sama da komai akasin gurbataccin shugabannin da a kullum a ke kukan "Zaben tumun dare."
 
A yayin da mulkin Kasa ya fada hannun da a kullum a ke da-na- sani, shakka babu a Sakkwato tuni Allah ya tafarwa garinsu nono domin kuwa sun yi tsintuwar guru a cikin sudi a bisa ga sa'a da dacen samun mai gayya mai aiki, hazikin Gwarzon Gwamna, Hon. Aminu Waziri Tambuwal a matsayin mutum mafi daraja ta daya a Jihar wanda shugabanci a siyasance tuni ya baiwa marada kunya ta hanyar gudanar da ingantaccen sahihin mulkin gaskiya, adalci da wanzar da ci-gaban al'umma wanda a ke fatar ganin ya hannunta Jihar a hannun da ya dace.  
 
Daga lokacin da jagoran siyasar karni, hazikin Gwarzon Gwamnan da al'ummar Nijeriya suka dukufa ga addu'ar ganin ya samu jagorancin kakkabe gurbataccen mulkin da APC ke gasawa al'umma aya a tafin hannu, ya damkawa Hon. Abdussamad Dasuki ragamar kula da Ma'aikatar Kudi a matsayin Kwamishina an san cewar Tambuwal ya yi farar dubara domin ya zabi nagartacce kana cancantaccen dan siyasa mai gaskiya da amana wanda ya jajirce tare da fafutukar ganin Gwamnatin Tambuwal ta samu nasara a kowane fanni. 
 
Hon. Abdussamad Dasuki wanda Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya karrama da sarautar Santurakin Sakkwato, matashin dan siyasa ne wanda a siyasace gaba da baya cikakken dan siyasar gidan Tambuwal ne wanda ba ya da surki, biyayyarsa 100 bisa 100 ga Tambuwal take, hasalima ba a taba alakanta shi da butulci ko biyayya ga wanin Gwamna ba, haka ma ko kadan ba dan siyasar jari hujja ba ne, a kodayaushe ci-gaban Jihar Sakkwato da al'ummarta ne babban burin da ya sa a gaba.
 
A jiya da yau Hon. Abdussamad Dasuki ya samarwa kansa suna a matsayin dan siyasa nagari wanda bai taba yin kasa a guiwa wajen sauke dukkanin nauyin da aka dora masa ba a cike da cikakkiyar nasara. Hasalima a kodayaushe fadi tashinsa bai wuce yadda za a cimma biyan bukatar da a ke bukata tare da kawar da matsaloli ba. 
 
Hannuntawa Hon. Abdussamad Dasuki babbar babbar Mazabar Tarayya ta Kebbe/Tambuwal da Tambuwal ya yi a lokacin da ya kammala Shugabancin Majalisar Wakilai ta Bakwai a 2015 kadai ya nuna irin gamsuwar da amannar da ya yi da Magajinsa a matsayin cikakken dan siyasa mai ilimi da gogewa mafi dacewa da kujerar wanda hakan a karara ya nuna Hon. Dasuki ba kyalle ba ne babban bargo ne. 
 
A Majalisar Wakilai ta Takwas, Hon. Abdussamad Dasuki bai zama kurma ko beben Dan Majalisa ba, domin kuwa an ci-gaba da jin amon Kebbe/Tambuwal da babbar murya, hasalima ya gudanar da ingantaccen wakilci nagari fiye da tsammanin mai tsammanin tare da jagorantar gabatar da dokoki 4 da kudirori 5 a zauren majalisa wadanda duka suka yi tasiri ga al'ummar da yake wakilta da al'ummar kasa bakidaya wanda hakan ya kara daga darajarsa a matsayin irin wakilin da jama'a ke muradi wanda ke da wuyar samu.
 
Santutakin Sakkwato wanda ya Shugabanci Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da Sojojin Ruwa ya nuna kwazo da jajircewa domin yadda ya shige gaba wajen jagorantar dimbin nasarori a aikace-aikacen Kwamitin da suka shiga cikin kundin tarihi ya tabbatar da zamansa a matsayin a- saka- ta- kare ko a-saka a- huta tare da samun yabo da jinjina daga Rundunar Sojojin Ruwa a karkashin jagorancin Shugaban ta a wancan lokacin Vice Admiral, Ibok Ekwe Ibas.  
 
Kwararre kana gogaggen masani tattalin arziki wanda ya samu horo a Jami'ar Abuja da shahararriyar jami'ar Harvard wadda ta ciri tuta a duniya, kafin shigarsa siyasa a 2010 a yayin da yake a matsayin Manajan Bunkasa Harkokin Kasuwanci a Kamfanin Dangote, ya jagoranci samun ribar naira biliyan 10 a kowane wata a sashen siminti. 
 
Yarima a Cibiyar Daular Usmaniyya kana Dan Sarkin Musulmi na 18, Dakta Ibrahim Dasuki (Allah ya ci-gaba da lullube shi da bargon Rahama) a yau a matsayinsa na Kwamishinan Kudi na Jihar Sakkwato, Hon. Abdussamad ya nuna a fili irin yadda ya kamata adalin shugaba nagari ya kasance domin ya dora Ma'aikatar Kudi ta Jiha saman ingantacciya kuma daidaitacciyar hanya wadda za a jima a na ribantar alfanun shukar da ya yi. 
 
Tsaftace tu'ammali da harkokin kudade, toshe badakalar sama da miliyan 500 da a ke yi wa hadiyar kafinol a kowane wata da bankado ma'aikatan bogi sama da 1, 000 a matakin Jiha wadanda baragurbi ke canyewa abin yabawa ne domin sanin kowa ne ma'aikatan bogi babbar matsala ce ga Gwamnati, hasalima bayan kakkabe su ne aka samu damar karin albashin ma'aikata mafi kankanta na naira 30, 000. 
 
Bugu da kari daidata alkulaman albashi wadanda ke cin karo da juna, bunkasa sashen biyan albashi, biyan tarin bashin da ake bin Gwamnati, horas da ma'aikata da sake ba su horon musamman, canza fasalin Kamfanin Saka Jari, bunkasa Hukumar Tattara Haraji da inganta ayyukanta, assasa hanyoyin samun karin haraji, hada kan kudaden haraji waje daya da tabbatar da shigarsu asusun Gwamnati da sauransu da dama duka ayyuka ne da Hon. Abdussamad Dasuki ya aiwatar tare da jajirtattun ma'aikatansa tare da samun jinjinar ban girma wadanda bai kamata a bar su a gurbataccen hannu ba. 
 
Kari da karau a karon farko a tarihin Nijeriya Jihar Sakkwato ta zamo ta farko wajen aiwatar da gaskiya da adalci a tafiyar da harkokin kudade a karkashin shirin SFTAS wanda a kan hakan wannan Jihar ta samu lambar yabo daga Bankin Duniya tare da samun tukuicin Dala miliyan 22 wato Naira biliyan 8.5. Haka ma Ma'aikata Kudi ta Kasa ta biyo baya da lambar girma da tallafin naira biliyan shida ga Gwamnatin Tambuwal kan tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin kudade wanda a baya ba a saba ji da gani ba.
 
A haka kadai za a fahimci Santutakin Sakkwato dan siyasa ne na daban wanda samunsa a matsayin Gwamnan Jihar Sakkwato babban alheri da ci-gaba ne ga al'umma domin tsantsar mai kishin ci-gaba da daukakar al'ummarsa ne wanda ya san ciki da wajen bukatocin al'umma da sanin hanyoyin magance su ta yadda Mai Girma Gwamna Tambuwal zai yi alfaharin hannunta Jihar Sakkwato ga hannun kwarai mafi dacewa, a hannun da aka shaida da kima, dattako da sanin ya kamata.  
 
Shakka babu a 2023 Tambuwal na bukatar gogaggen dan siyasa irin Hon. Abdussamad Dasuki wanda zai dora daga inda ya tsaya, wanda ke da cikakken ilimi, gogewa da wayewar iya hulda da magana da kowa a ko'ina a duniya wanda ya san ciki da wajen Nijeriya wanda ke da hanyoyin kawo masu zuba jari domin habaka tattalin arzikin Jiha wanda ke da gagarumar karbuwa ga al'umma wanda hatta 'yan adawa sun yadda da zamansa nagari na kowa wanda kuma a ke da tabbacin zai baiwa marada kunya ta hanyar gudanar da amintaccen shugabancin da al'umma za su yaba tare da cewar gwamma da a ka yi. 
 
Magaji Sarki ya rubuto ne daga Arkilla, Karamar Hukumar Wamakko, Jihar Sakkwato.