Matsalar Rashin Wutar Lantarki A Arewacin Najeriya Za Ta Gushe Kuwa?
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Yan Najeriya da sauran masana sun yi ittifakin cewa matsalar rashin cigaban Najeriya na da nasaba da karacin wutar lartarki musammanma a arewacin Najeriya.
A Najeriya ga alama matsalar tsananin karancin wutar lartarki da ake fama da ita yanzu haka a kasar za ta cigaba.
Ana matukar kokawa da rashin wutar lartarki a galibin yankunan arewacin Najeriya a yan tsakanin nan a Najeriya wannan na faruwa ne lokacin da damana ke sauka a wasu sassan Najeriya.
Wanda kawo yanzu gwamnatin kasar tayi ko in kula da wannan rashin wutar da ke addabar jama'a inda masana ke la'akari da girman al'ummar da kuma wutar da wasu kasashe da basu kai girman Najeriya ba ke samarwa.
Yaya abin ke shafar ku a inda kuke? kuma me kuke son ganin an yi domin magance karancin wutar ta lartarki A Najeriya?
Amsar da mutane ke amsawa da kansu Amma gwamnati ta ki aminta ta karbi daya daga cikin amsoshin jama'a domin shawo kan matsalar.
An bar mutane da mitar banza tare da neman bakin zare wanda kowa ya kasa ganowa domin gwamnati ta turmuje abin cikin kasa mai duhun gaske.