DALILAN DA YA SA TAMBUWAL YA CE SULHU ZA’A YI WURIN FITAR DA 'YAN TAKARA  A SAKKWATO

DALILAN DA YA SA TAMBUWAL YA CE SULHU ZA’A YI WURIN FITAR DA 'YAN TAKARA  A SAKKWATO

 

A taron masu ruwa da tsaki da aka kammala na jam’iyar PDP Gwamna Tambuwal ya bayyana cewa jam’iyar PDP a jahar Sokoto  zaben fidda gwani wato PRIMARY ELECTION a turance CONSENSUS za'a yi wato SULHU a hausance kenan.

 
Bayanai sun nuna cewa wasu ba su ji dadin wannan matakin ba saboda a tunaninsu idan aka yi zaben fidda gwani wanda ba silhu ba su ne masu yawan delegates.
 
Hakan kuma ya faru ne saboda lokacin da aka yi zaben EXCO na party a mataki na jaha da kananan hukumomi sunci karensu ba babbaka ta hanyar dora wadanda za su iya juyawa kamar waina.
 
Gwamna Tambuwal daga baya ya ankara da manufofinsu da tsare-tsarensu inda ya dakile wani yunkuri da suka so su yi na dora 'yan amshin shatansu amatsayin ciyamomi lokacin zaben kananan hukumomi.
 
A halin yanzu tsarin sulhu ba abunda zai musu daidai ba ne saboda ana su hasashen su ne masu yawan delegate kuma su ne suka fi karfi a jam’iyar, a don haka idan aka yi Primary election na zabe  su ne masu nasara, sai dai sun manta karfin Gwamna ya wuce karfin mutum daya.
 
Tsarin SULHU ya kasance tsarin da idan akwai 'yan takara biyar ko sama da haka za a cimma matsaya  wasu su jayewa wani, wanda a karshe duk wanda yake jayayya ya ce ba zai  jayewa in bai yi hattara ba  zai yi kunya.
 
Wannan tsari zai taimakawa Gwamna Tambuwal yasan ainihin masu yi masa biyayya da kuma wadanda suka yarda da jagorancin sa.
 
Hakan kuma zai kara hada kan jam’iyar, 
 
Ko a musulunci an ce SULHU ALKHAIRI NE!
Daga Yusuf Muhammad Ladan