MAMAYA:Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta Biyar

MAMAYA:Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta Biyar

 

 

 

 Ina matukar godiya gareku masoyan Haupha.

 

 

 

 Shafi na Biyar

 

 

 

Mal. Aminu ya kafe ta da idanuwan sa da ba alamar sauƙi cikinsu ko rangwame.

 

Addu'ar neman tsari kawai take a zuciyarta.

 

Ya jima tsaye kafin ya shigo cikin ajin ,kai tsaye inda take ya nufa numfashinta taji zai dauƙe dan haka ta zabura ta bangaje shi ta ruga da gudu tabar ajin .

 

Ga dai dariyar yanda ta bangaje shi ya faɗi ƙasa ƴan ajin nason yi amma gudun hukuncin mal Aminu ya hana kowa motsin kirki a gunda yake.

 

Gudu take na gaske bata damu da yadda mutane keta binta da kallo ba har ta shigo layin su .

 

Ji tayi kawai taci karo da wani abu wanda yasa numfashin ta ɗaukewa.

 

Cike da tashin hankali Nasir ya sauko daga kan machine ɗinsa ya nufi inda Bilkisu ke kwance shame-shame ƙasa.

Mutane nan da nan suka kawo ɗauki dan wasu kan idanunsu lamarin ya faru.

 

Ba sosai taji rauni ba amma ta suma , abin da ya tada hankalin Nasir kenan duk ya ruɗe.

 

Mal. Ahmad da fitowarsa daga gida kenan zai koma kasuwa yaci karo da   al'amarin .

Bakaramin tashin  hankali ya samu kanshi ba ciki , sai dai ya tabbatar ma da Nasir ɗin ya tabi ba komi Allah ya kiyaye gaba .

 

Shi kuma Nasir sai ya samu kanshi da kasa tafiya balle ya aminta da maganar mal. Ahmad ɗin duk da yanzu ya fahimci shine mahaifin yarinyar da tsautsai yasa ya banke .

 

Sai da mutane suka saka baki sannan mal. Ahmad ya amince suka dauki Bilkisu zuwa asibiti dan duba lafiyar ta sosai .

 

 

 

Inna tunda wancan lamari ya faru sai ya zama ta sake ɗauko wata sabuwar tsana da tsangwama ta ɗora akan Bilkisu ,kwata-kwata bata barin ta ganta cikin natsuwa komi tayi sai ta gwasaleta ,hakan yasa Bilkisun a sabuwar damuwa ainun.

 

 

Ko ina an duba bata samu wani rauni ba wanda zai tada hankali illa kujewa data samu a wasu wuraren ,hakan yasa aka bata magunguna kawai.

 

Tunda yake bai taɓa ganin yarinya natsatstsa kamar wannan ba , yana rayuwa cikin bariki amma bai taba ganin yarinyar da natsuwarta ta shahara ba kamar wannan yarinya da ya banke da machine ɗinsa ba .

 

Kallonta kawai yake yanda duk tabi ta birkice dan ganinsa tare dasu .

 

Gata ga alama jarumace dan ya ga ko gezau fuskarta batai ba da ana wanke ma ta raunuka da magani.

 

Sai Babanta daketa jera mata sannu wani kan wani , ita kam ba ta ko son ɗago fuskarta ma .

 

 

 

Bayan an gama komi ya sake biyo su dan ganin gidansu ,wanda ya karanci fuskar mutunniyar tasa sam bata so hakanba .

 

Yasha mamaki da yaga gidansu a cikin layin su yake ma ashe .

 

Duka gida biyar ke tsakanin su , ko da yake ba abin mamaki bane dan ba nan yake zaune ba yana can gun aikinsa na Soja , aikin da yau shine Niger gobe Kano jibi Maraɗi yanzu haka dai yana Kaduna can aka wullashi dan haka ba kowa ya sani ba a layin nasu kamar yanda ba kowa yasan shiba shima.

 

 

Inna na zaune tana yanke akaifa taji sallamar Babansu Bilkisu , kamar karta amsa ta tuno da yawan mitar da yake mata kan rashin amsa sallamar da bata sonyi idan anyi ,

 

Kanta ƙasa ta amsa  mashi dan ita bata ga abin da zai sa ace dolen doliya sai an dinga amsa sallama .

 

Kallonta kawai yayi ya fahimci matsalaita.

 

Jin wata baƙuwar murya yasa ta ɗagowa dan ganin mai muryai, ganin Bilkisu tayi rungume jikin Babansu ga wani saurayi biye dasu a baya yasa ta saurin kallon fuskar malam dan ganin yanayinsa .

 

Bata fahimci komi ba ,dan haka ta taɓe baki ta gyara zama taci gaba da abin da take yi , sai dai hango malam ya nufi ɗakinta da Bilkisun yasa ta saurin tankawa.

 

"Malam kar dai ka shigarmun da ita ɗaki ka nufi nasu ɗakin ,,Kallon mamaki ya bita dashi ya nufi ɗakin nata , ai kuwa ta fara ruwan masifar bafa zata zauna mata ɗakiba ga nasu ɗakin .

 

Juyowa yayi ya nufi ɗakinsu da ita yana fatan Huraira ta gane gaskiya kan lamarin Bilkisun.

 

Nasir dai yana tsaye kanshi a ƙasa yana jinjina faɗan matar gidan a ransa.

Ɗakinsu ya kaita yana ƙarayi mata sannu , ita dai tayi luf jikinta na mata ciwo zuciyarta na fargaban hukuncin da mal. Aminu zai yanke mata ,

 

R̃iƙo hannun Baban tayi hawaye suka zubo mata "Dan Allah Baba kaje islamiyyarmu kaima Mal. Aminu bayanin abun da ya hanani zuwa kwana biyu , dukana zai na rugo dan dukan hauka yake mun Allah ,,

 

Wani sabon tunanin ne ya shigesu su duka biyun.

 

Nasir na maimaita suna mal.Aminu a ransa , sake kallonta yayi dan gane kalai kayan makarantar tasu , ko shakka babu acan ƙanensa Umar ke koyawa, zai kuwa tambayesa waye mal. Aminu mai takurama Bilkisu haka ?

 

Fahimtar faɗan matar gidan sai ƙara ƙarfi yake yasashi yin bankwana ya fito ,

 

Duƙawa yayi dan yima matar bankwana ,wani malalacin kallo ta banka mai taja wata uwar tsuka ta ci gaba da abin da takeyi .

 

Kasan cewarsa shima ɗan zafin kai ya taɓe bakinsa ya fice yana addu'ar kar da Allah yasa itace mamar Bilkisun , dan duk ran da tasake ta ƙara mai tsaki sai ya fasa mata baki .

 

 

Baba bai ƙasa a gwiwa ba sai da yaje ya samu mal. Aminu da maganar Bilkisun amma sai ya nuna masa rabon da yaga Bilkisun ma ya jima.

 shi baiga Bilkisun bama kwata-kwata sannan bashi ke kiran sunayen ajin suba ma ,

 

Haka suka rabu Baba na tunanin ko dai bashi bane ? Dan Bilkisu bata yi mashi ƙarya ga dukkan lamarinta .

 

 

Da dare sai ga Nasir ya dawo dauke da kayan motsa baki ya kawoma Bilkisu ,  a cewarsa jikinta ya sake dawowa dubawa .

Baba ya nuna yaji daɗin dawowarsa amma bai ji daɗin hidimar da yayiba sam.

 

Wannan karon ma Inna kallon kashedi tabi shi dashi, abun ka da soja sai kawai ya dawo rai ɓace ya duƙa yace " ko zan iya sanin dalilin wannan banzan kallon naki gareni ?

 

Nasan dai ke matar Babansu ce dan daga ɗazun zuwa yanzu na fahimci komi na gidan, dan haka ki cireni jerin waɗan da zakima turaja ,,

 

Ya aje mata kuɗi ya fice daga gidan baki ɗaya.

 

Ai saita kama kumfar baki yau mal. da Bilkisu sun kawo wanda yayi mata rashin kunya har gidanta .

Malam da yana hangen su daga ɗakinsu Bilkisun ya fito yana yaƙe yace " yanzu Huraira bakiji kunyar abin da kike cewa ba ?

Cikin rashin kunyar ne ya baki kuɗin nan ko ?

Allah ya ganar dake hanyar gaskiya , ace ƴarki ta samu tsautsai a hanya amma ki gaza tausaya mata ko da sannu ta samu daga gareki ?

 

 

Itama tana daga zaune kofar ɗakinta tace " i ɗin ai ba rokonsa nayiba shi yaban dan kansa kuma wallahi ban maidawa malam,,

 

"Da kake cewa ita kuma ƴa tace ai kai kasan wannan nikam ban san da wannan ba ,,

 

Sanin halinta ya sanya shi shareta yaci gaba da laziminsa .

 

 

Cikin dare Bilkisu ta tashi kamar yanda ta saba ta fita waje dan ta ɗauro alwala , fitowar ta kenan ta hango kamar wani mutum tsugunne yana tsintar wani abu ƙasa yana ci , gashi dai dare ne kuma babu farin wata ko kaɗan amma tana hango abin da yake tsintar yana ci hannu baka hannu kwarya , sake fiddo idanunta waje tayi dan tsutsace yake ci da ranta sai motsi take amma shi kuma sai ci yake tamkar yana cin wani abinci mai daɗi, ɗan matsawa kaɗan tayi dan ta hango tamkar Babansu ne ke cin tsutsar dan kayansa ne daya saka yau a jikinsa hakama yanayin jikinsa sak na Babansu ne .

 

Cike da fargaba ta matsa gab da mutumin dan tabbatar da abin da idonta yagane mata.

Fuskarsa na duƙe sai cin tsutsocin yake tamkar wanda ya samu wani nama mai daɗi.

 

Cike da fargaba ta isa gab da shi, murya cike da tsoro tace "waye kai ?

 

Yana ɗagowa ta runtse idonta dan ba fuska bace a tashi fuskar gaba daya tsotsine a ramin fuskar tashi ba kyan gani ,

 

Hasbinallahu wani'imalwakin !

 

Abin da ta samu bakinta da maimaita wa kenan .

 

Bat ta ga ya ɓace ma ta amma kuma a bayanta taji ana taba ruwa kamar ana ɗiba.

 

Cike da fargaba ta waiga don ganin wake ɗibar ruwan .

 

Sake fiddo idanunta waje tayi tana mai shafa fuskarta dan tabbatar da abin da ta ke gani gaske ne koko?

 

Sak wata mai kama da ita tagani hatta kayan jikinta irinsu ne jikin waccen ɗin tana ta zuba ruwa a buta ga alama bata ma san da tsayuwar Bilkisu a gunba.

 

Wata tsohuwa ta taho da ƙyal tana kiran Bilkisu kiyi maza ki fara sallar kafin waccen mayatacciyar ta fara naga ta fito da alama kuma sallar zatayi ,, kin san ta da nacin tsiya gun ibada .

 

Wadda aka kira Bilkisu ta ɗago kanta "Yanzu kuwa zan gama ai kinga ta tsaya kallon ƙwab yau ,,

 

Ya Salam !

 

"Hatta muryanmu iri ɗaya ce ,, (cewar Bilkisu )

 

Tana ta kallon ikon Allah gabanta Bilkisun ta gama alwala ta koma kofar ɗakin su ta kabbara sallah.

 

Tsohuwar kuwa gani tayi ta ƙara tsawo kamar ana janta sai tsayi ta ke har bata iya hango iyakar tsawonta .

 

Durƙushewa tayi agun tana karanto duk abin da ya zo mata ga rai na addu'a .

 

Ji tayi an dafata  a razane ta waiga , ido huɗu tayi da yarinyar da ta samu cikin toilet ɗin school ɗin su kwanakin baya .

 

Sai dai yau idanunta biyar ne ɗaya a tsakiya sai biyu-biyu a ƙasan na tsakiyar ,

 

Hancinta sai fidda wani farin abu mai kauri yake tamkar nono kindirmo bakinta sai fidda hayaƙi yake halshenta ya zazzalo riƙe a hannunta tana wasa dashi tamkar tana wasa da wata igiya.

 

Tana ganin haka ta runtse idonta ta buɗe bakinta duka ta fara karanto ayatul kursiyyu muryanta ta karaɗe gidan baki ɗaya .

 

 

 

A wannan lokacin kuma Baba na ta fama da Inna ta daure ko raka'a biyu ta tashi tayi ta nafila ko ta ɗauro alwala taita lazimi .

 

Haka ya haƙura ya rabu da ita ya tada sallah , ita kuma ta koma barcinta .

Sai dai bata jima ta jiyo muryai Bilkisu na rairo karatun Alkur'ani mai girma , ko shakka ba tayi Yarinyar bata tashi karatu dan gulma da son Mal. ya takura mata haka kawai sai tsakar dare .

 

Tsaki taja ,jin sai ƙara daga murya take yi yarinyar dan mal. ya sake samun abin mata gori tun da safe .

 

Ayyanawa tayi ya kamata yau ta je taima yarinyar kashedin karshe kan karatun daren nan , tunda ba dole bane ba ai , sai kuma tayi ɗan jim tana tunano abin da yasameta wancan karon .

Fitsari kawai taji ya zo mata dan haka ta yunƙura tana mitar bata ga abin da yasa mal. ke mata abubuwa kamar wata ƴarsa in dai kan gulmai karatun canne yau anyi na karshe ai na kula kaima baka tashi karatun ko lazimun sai kaji sababbar ta fara ,,

 

Mal. sai gyaran murya yake mata karta fita amma ina ko waigowa batai ba ta fice har dasu jan kofar da karfin tsiya .

 

Ita kam Bilkisu tana jin alamar sun ɓace sai ta sungumi buta da wata roba ta ruga ɗakinsu ta maido ta rufe abin ta tana hamdala ga Allah .

 

Inna cike da mitarta ta sunkuci buta ta faɗa toilet ɗin bakinta ba komi sai azabar faɗa.

 

Ta tsugunna ta fara fitsarin kenan kamar wadda akace kalli nan , ta kalli ƙasan da fitsarin ke sauka ,

 

"Wayyo Ni Huraira !!

 

Wata yarinya ƙarama ta gani kwance kanta daidai saitin fitsarin ta buɗe bakinta fitsarin sai zuba yake ciki .

 

 

Tayi-tayi ta miƙe tsaye ta kasa gashi fitsarin yaƙi tsaiduwa balle ta tsaidashima .

 

 

Muryar wata yarinya taji na cewa " la-la-la ke yanzu Huraira dan kin raina Hirjiyya kanta kike fitsari bayan azumi ta ɗauka ?

 

"To wallahi barta ke koni da akai gabana Idan shamzak yazo sai naci uwata balle ke ,,

 

Habawa ai sai Inna ta ƙara valume ɗin ihunta .

 

"Wayyo Allah na !

"Kui mun rai bansan zan gankuba da ban fitoba kwata-kwata ,,

 

" Na bani na lalace ni Huraira !! Yau na ga Idi zindir.

 

Tana cikin kururuwarta Hirjiyya ta buɗe idanunta masu haske da girma ta watsasu kan Inna .

 

Haba ai sai Inna ta sake dagewa iya karfinta .

 

"Mal. Kazo na shigesu yau na ɗebo ruwan dafa kaina yaka mal. zokai mun ɗauki ,,

 

Mal. dan darajar uwayenka matattu da rayayyu kazo kaimun ɗauki kaji ,,

 

Wadda aka kira da Hirjiyya ta watsa mata harara kafin tace "Tunda kikai mun fitsari yau ba wanda zai hanani wasan ɗanɗam dake a gidan nan ,,

 

Idanu waje Inna ke kallon yarinyar mai kattin idanuwa waje .

 

Tau taji saukar wani bahagon mari tagwaye a kumatunta duka biyun .

 

"Ihu mal. zasu kashe ni ,, (abin da Inna ke ambata kenan cikin kururuwa )

 

Jini ta baka ta hanci ya gwabce mata .

 

Wasu marukan taji bi da bi , ai batai wata-wata ba ta kwasa da gudu ta nufi ɗakin su bakinta bai sarara da kiran ta bani ta lalace ba .

 

Babu irin turawan da bataima kofar ba amma kofa ta datse gam , ga alama daga ciki mal. ya datseta .

 

Sai ihun mal. ka buɗe kofar take amma ko alamar buɗewa mal. baiba , gashi sai ganin abubuwan ban tsoro take na shawagi a tsakar gidan.

 

Ganin mal. bai buɗe mata kofar yasata kwasawa da gudu ta nufi nata ɗakin .

Ba sai an faɗi mata ba tasan yauma fuskarta ta sake hayewa kamar fanke .

 

Runtse idanunta tayi duka tana fatan Allah ya kaita gobe taima mal. rashin mutunci da yaƙi buɗe mata kofar ɗakinsa .

 

A bayyane tace "Ɗakinka na banza ban ƙara kwana ciki ma,,

 

 "Yacin da kin burgemu Huraira ,,

 

Fadar wasu guntayen jarirai guda biyu,

 

"Kinga sai mu dinga kwana anan ko ?

 

Numfashinta ya dauke cak.

 

 

 

 

Washe gari da asuba kowa yayi Sallah Bilkisu tayi ayyukan da take yi ta nufi ɗakin Innar don ta shaida mata zata wuce makarantar boko .

 

Ta isketa lulluɓe da zanen gado ga alama tana jin daɗin barcin da take , kallon gefen gadon tayi taga abin sallah da casbaha dan haka ta fahimci tayi asuba komawa tayi , sai ta juya tabar ɗakin .

 

 

Itakam Inna tana jin komi ke faruwa tsabar takaicin abin da sukai mata jiya shine yasata boyewa dan takaicin mal. yafi na kowa a ranta .

 

Kowa na tafiya mal. yaji shirun tayi yawa ya leƙa ɗakin cike da fara'a a fuskarsa .

 

 

"Huraira nace jiya dai kinyi abin kirki kin kwana aikata abin ƙwarai baki ji yanda najii daɗin abin ba a raina kai Huraira Allah ya taimakeni kullum kiyi ta hakan ai da har sadaka sai nayi dan farin ciki ,,

 

 

 

Hhhhhh tofa mi mal. Ahmad ke nufi kenan ?

 

 

 

Kuyi hakuri kunji ni shiru kwana biyu ko

 

 

 

 *Taku Haupha*