ANA BARIN HALAL*..:Fita Ta Biyar
ANA BARIN HALAL*..
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*PAGE* 5
Tun ranan da mukaga abokan Yaya Ahmad bamu sake ganin su ba, kasancewar shima ba a gari yake zama ba, amma rana ɗaɗɗaya ne bamu hiran su nida Habiba, wanda har ta kai mun bawa Maryam labarin su da irin farin su, cikin zolaya maryam ta kalle ni tana dariya, "amma dai Ayshaa ke kike koyawa habiba ganin kyaun farin mutum? Kuma daga dukkan alamu kin ƙyasa? Inaga gara a sanar da yayah Ahmad"'
Hararan ta nayi nace, "ban dake maryam yaushe ma na girma da har zanga wani nace ina so? Soyayyan ma ae bamu kai ba, kuma bani da class ne zan ce ina son su? Kawai ni fararen mutanene bana gajjiya da ganin su, kin san bana son baƙin fata", dukan da habiba ta kai mun ne na hankalta da kwafsin da nayi, don mantawa nakeyi mamie baƙace, haɗa ido mukayi muka kwashe da dariya dukkan mu.
Babu wasa rayuwar tana wani irin gudu, a haka yau muke kammala waec ɗin mu, kowa a cikin mu cike da farin ciki da burika kala-kala a zuciyar mu, ranan dukkan mu huɗun, ni, habiba, maryam, jamilah muna zaune kafin driver yazo ya ɗauke mu, a yanayin mu bamu da hayaniyah dukkanmu, sai dai nida habiba da maryam idan mun haɗu mukan taɓa surutu sosai a tsakanin mu, amma idan wanda bai sani bane bazai taɓa yadda muna da surutu ba, amma ita jamila da wuya kaji maganan ta, sai dai kawai ta biku da ido, jamilah bata da matsala ko kaɗan, shirunta yayi yawa, amma akwai azaban kai, domin kanta yana mugun ja sosai.
Maryam ce ta dubi jamilah tace, "yanzu besty da gaske auren za'a miki? Tou karatun naki fah"? Ta faɗa fuskanta cike da jimami, domin duk munyi shawaran karatu zamuyi a wuri ɗaya, wato ATBU, don ko jamb ɗin mu shine first choice ɗin ko wacce a cikin mu.
"Besty tou an yanke muyi auren saboda na bishi chan na fara karatuna, nima kuma gaskiya hakan yafi mun, don ina tsoron yana tafiyan nan wata ta mun wuff da shi", dukkan mu dariya muka kwashe da shi, ni kuma na zabga tagumi ina duban Jamilah cike da mamakin wai zatayi aure, cousin ɗinta ne, kaman wasu zamu shiga SS 3 yace yana sonta, kuma cikin hukuncin ubangiji yagama masters ɗin shi a London kawai ya samu aiki achan, shine iyayen su suka yanke kawai ayi auren su tafi tare, idan yaso karatun sai tayi achan.
"ikon Allah" kawai na furta ina kallon ta, sannan nace, "jamilah kuma zaki iya rayuwar auren da ɗan ƙaramin shekarunki?" kallo na tayi tana murmushi tace "me zai ban tsoro, yayah nane fah, kuma zai ɗaga mun ƙafa sai na ƙara girma yace mun".
Dariya dukkanmu muka kwashe da shi, habiba ta dubeni tana ɗaga kai cikin salon mu idan zamu zolayi mutum tace, "dogon magana" kwashewa muka sakeyi da dariya, maryam da jamilah na taya mu.
Maryam ce ta dube mu tace tou yanzu me zamuyi na event? Kun san muma yanzu bebs ne, don mun girma ta faɗa tana wani juya idanunta, shiru mukayi na zuwa wani lokaci, sai jamila ta gyara zama tace, "mummy na zasuyi liyafa ne kawai, nima bana son wani event sosai, tunda angon yace shi babu wani event da zaiyi bayan recieption da zasuyi, saboda haka ya kamata mu gwangwaje adon mu a liyafar nan.
Da yake nima bana son wani damuwa sosai sai kawai na bada ƙarfin ayi hakan, babu yadda habiba da maryam suka iya kowa sai ta amince, a haka drivern su yazo ya ɗauke ta, muma babu daɗewa aka zo aka ɗauke mu.
Bikin jamila ya gabato sai shirye-shiryen ashobi mukeyi, inda muka haɗu da wasu friends ɗinta guda 6, sai cousins ɗinta guda 2, muka zama mu 11, muke ta shiri da tsare-tsaren mu, ranan da mukaje sallon a *SHAGARI SHOOPING COMPLEX* Yayanta Aliyu ne yazo ɗaukan mu, shima yadda kika ga jamila da kyau da shiru tou shima haka yake, sai dai ba fari bane, kuma baza'a ƙirashi baƙi ba, saboda yana da haske wanda wasu zasu iya kwatanta shi da fari, amma a wurin wanda basu ganin fari sosai, lecturer ne a Federal polytechnic bauchi, yana Computer depertment, ɗan gayu ne na nuwa, kuma daga ganin shi mai tsafta ne, don motan shi wani irin azaban ƙamsh yakeyi, ga kuma sanyin A.C
Gidan mu aka fara wucewa ya sauƙe mu, sannan suka wuce tare da jamila da wata cousin ɗinta Ummitah, daga kaduna suka zo, kuma sun shaƙu sosai da jamilah, saboda kullum hiranta Ummitah ne.
Muna shigowa gate ɗin gidan mu Habiba ta juyo tana kallona, fuskan ta cike da gulmah tace mun, "sisto naga daga dukkan alamu Yayan jamilan nan hankalin shi yana kanki, duk wani nutsuwar shi ina hankalce da shi, sai kallonki yakeyi, ita kuma ummitan nan inaga sai wani rawan kai take mishi, har da wucewa gaban mota ta wani zauna, bayan duk hankalin shi baya tare da ita,"
Hararanta nayi nace, "ke kuma cutar gulmar ki ta motsa duk kin kafe shi da ido, saidai in kece ya miki har ya birge ki, don ni wnn ba layi na bane, fari nake jira", ina faɗan haka na juyo ina kallon habiba na kama haɓa na, "habiba niko ina dai labarin fararen abokanan yayah Ahmad ɗinnan? Kullum yazo ina hankalce ko zan sake ganin su amma shiru, ko dai aljanune?" na faɗa ina ɗan zare ido.
Dariya ta kwashe da shi tana cewa, "inaga wannan karon idan yayah Ahmad yazo dole ayi cikiyar su, kada naje sun kama kurwar ƙanwata," hararanta nayi nace, "me kike nufi? Kina tunanin sun shiga raina ne? Kuma waye ƙanwarkin?" Allah sarki habiba na, wato Aunty nice kullum kika ga faɗan mu tou akan shekaru ne, kowa bata so ace itace ƙarama, a haka ma habiba da tasan ta ɗan fini da kaɗan wataran ta kance ta bar mun girman, ta ƙara mun shekara uku ma bayan wata ukun, ni kuma na dinga tsokananta ae tunda na fita tsayi tou na rigata zuwa duniya, a haka muke kullum cikin soyayyar junan mu, donni son da nake yiwa habiba ko hafsy da muke ciki ɗaya bana mata.
Washe gari tun safe muka tafi gidan su jamila, saboda wacce zata mana make-up da wuri zata zo.
*EVENT CENTRE* a wurin aka shirya yin liyafan, masha Allah amaryah tayi musulmin kyau ita da ƙawayenta, sai wani jin falli mukeyi irin muma mun girman nan, har mun fara aure, da yake shine biki na farko da muka farayi na ƙawayen mu sai abun ya ƙayatar da mu sosai, sai wanni basarwa mukeyi muna wani rangwaɗa irin ƙawayen nan, Aysha ta faɗa fuskar ta kaman alokacin ake hidiman, ga kuma wani rangwaɗa kanta da takeyi, kaii ni Aunty nice ina ga mata mai yanga kam, don ƙuri na mata ina kallon yatsun hannunta yadda take watsa su kaman wata ɗawisu, ga magana ɗaya tana juya idon nan kaman ka sace ta ka gudu, gaskiya macen da bata da yauƙi ta rako mata duniya ne, na faɗa a cikin zuciyata.
Aunty nice ina baki labari, maganan habiba kuma sai ya tabbata, domin Aliyu yayan jamilah gaba ɗaya ya takura ni, duk inda nayi idon shi yana kaina, tun lokacin da muka fito za'a tafi wurin liyafan yakasa ya tsare dole sai na shiga motan shi, haka ya aiko Fatie ƙanwar su mai bin jamilah ta ƙirani, gashi ba mai son magana ba, ina fitowa yace na shiga motar shi, ido na zuba mishi ina ɗan kame-kame da riƙe gyalen jikina, a haka na daure nace mishi zan bi motan amaryah ne, ya kallo ya bini da shi cikin nutsuwa da kwantar da kai yace, "amaryah ma da angon ta zasu tafi, kema kibi naki angon kawai ku wuce tare", ya faɗa bada wani damuwa ba kaman dama muna tare.
A razane na kalle shi nace, "ni kuma? Ni ae banida aure, yana duba na ido cikin ido yace, "ehh kema ae zakiyi tunda ba tabbata xakiyi ba, babu yadda na iya da shi, dole naje na jawo habiba da maryam akan mutafi tare, kafin kuma kiyi haka ummitah ta fito tayi jikin motan Aliyun tana wani rangwaɗa, gata kaman zata ɓalle don rama, "Bro bari nazo mutafi, tun da kaima chan kanufa.
Dubanta yayi kai tsaye yace, " bana son takura ki wuce ki nemi wani motan, akwai wanda zan tafi dasu", kuma bai wani ɓata lokaci ba ya buɗe mun gaban motan fuska a ɗaure ya mun alaman da na shige, sannan ya dubi habiba da maryam ya musu alaman su shige bayan motan, ko takan ummitah da ta buɗe baki tana kallon mu bai bi ba.
Ummin mu da maman maryam da mamie duk sunzo wurin liyafan, mamah kawai aka bari a gids, duk inda mukayi idon ummi yana kanmu.
Bayan an buɗe fili da addu'a an fara programm babu daɗewa ango ya iso da rakiyar abokan shi guda uku, bayan sun zauna babu daɗewa D.J ya basu umurnin fitowa filin, aka saka musu waƙan aure, haba zokiga iyayen zamani, ba uwar amaryah ba bana ango ba, duk ɓarin kuɗi sukeyi, damu abu duk ɗaya, kai ranan naga matan manyan bauchi, kowa ɓarin naira kawai takeyi don ace ita ce tafi burgewa, bayan fili ya ɗan lafah amaryah sun koma sun zauna, sai D.J ya sake bada daman ƙawayen amaryah su fito fili.
Da ƙyar maryam ta riƙo hannu na muka fito, domin ita da habiba suna da son rawa a rayuwar su, ni dai haka na fito na tsaya na ɗan riƙe handbag ɗina ina kallon su, batare da nayi rawan ba, sai dai ina ɗan juya jikina kaɗan, wanda wani zaiyi tunanin nice amaryah, a haka Aliyu ya fito yana mun liƙi kaman bai san daɗin kuɗin ba, ganin haka duk inda na kauce yana biye dani sai mummyn su ta fito tare da wata ƙawarta suka shiga liƙa mun kuɗi daga ni har Aliyun, fuskan mummyn sun cike da fara'a, wanda alamu ya nuna mata Aliyunta yayi kamu, wanda ta daɗe tana fata da kuma burin ganin wannan lokacin.
Daga gefen su ummin mu kuma mamie ta wani matse fuska tana bin mu da harara, a haka bakin ta ya suɓuce taja wani dogon tsaki, babu kunya tace, "shishigi a wurin yaran nan yayi yawa, abu gaba ɗaya babu armashi? Sai wani shishshige musu Aysha ta keyi, ae idan yaro mai rawan kaine idan zaije wuri sai a ja mishi kunnen kamun kai, bawai yaje wuri yana nuna halin rashin kamun kai ba", daga maman maryam har ummin mu babu wacce ta bi ta kanta, a haka aka cigaba da progrmm har magrib tayi, sannan aka fara haraman tashi.
Ummi ana ƙiran sallah sukayiwa mummy sallama suka tafi, sannan ta riƙo hannuna tace ana idar da sallan ishaa Umar zaizo ya ɗauke, sbd haka akula da kai ko". Insha Allahu na amsa mata, ina son umminah Aunty nice, sbd matace mai zuciya mai kyau, bawai yabon kai ba, ban taɓa ganin mai irin zuciyar ummi na ba, tafaɗa tana saka hannun ta tana ɗaukan bottle na ruwa, ni kuma na ƙara gyara zamana ina kallon ta da sauraranta da dukkan hankali na, zuciyata tana son jin yayah labarin fararen abokan yayan ta ya nufa, amma bana so na mata gaggawa.
*AUNTY NICE*
managarciya