HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta 25

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta 25
HAƊIN ALLAH
 
   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
            Page 25
 
 
 
 
 
 
Tana zaune ta buga uban tagumi, kowa yasan ta da wannan tabi'ar ta zama ta buga tagumi cikin zuzzurfan tunani, wanda wani lokacin sai dai kaga hawaye sun gangaro daga idanunta.
 
Tun da ya shigo gidan ya ji tsit yasan ta fara sana'ar tata, shi kau da ace yasan yadda zai ya wanke mata zuciyarta daga tunanin baya tabbas daya wanke mata, amma ta ya zai yi? Duk wani abin da yasan zai sata farin ciki da walwala ko da yaushe yi mata yake, ba shi kaɗai ba, kowa na nuna mata ƙauna kowa sonta yake, yanzu ta zama daidai da kowa a cikin mutane amma Alawiyya ta kasa cire tunanin mutane biyu a zuciyarta, mahaifiyarta da ƙawarta Jiddah. Babu ranar da bata zubar da hawaye, kamar yadda babu ranar da bata bin tashar motocin garin Kano don a cewar ta zata haɗu da ko Jiddah ko Mamarta a tashar haka jikinta ke bata a kullum. 
A hankali ya isa inda take yana jin tausayinta na yawo a cikin ilahirin jikinsa, ta bayanta ya zagayo ya rungumeta yana mai saukar da ajiyar zuciya.
 
Saurin goge hawayen idonta tai, don tasan babu abin da ya tsana irin ganinta cikin kuka da tashin hankali. Yana mamakin yadda take da dakiya da jajircewa ace wai ita ce ko da yaushe sai kuka. 
Ita ce mai saka mutane da dama kuka, a kotu amma ita a gida kullum sai ta yi kuka. Ta zama babbar Lauya wadda baki ɗaya jahar Kano ke taƙama da ita, domin babu case ɗin da zata amsa batai nasara kansa ba.
 
Jama'a da dama na jinjina mata wasu na yawan turo mata da wasiƙar rayuwarta na birge su, ina ma ace suma yadda ta taso suke? Da sun ji daɗin sosai domin kowa ya ganta bai taɓa cewa tasan miye damuwa ko matsala, sai hanyar warware su kawai ta sani.
A duk lokacin da taci karo da zantukan mutane a shafin ta na Facebook, IG, Twitter, WhatsApp, sai na ji hawaye sun zubo mata, domin da sun san baƙar wahalar data sha a rayuwarta kafin ta kai wannan matakin sam da babu wanda zai sha'awar kasancewa a matsayin da take ko da wasa. Sai dai daman haka abin Allah yake sau tari sai ka ci baƙar wahala ka shiga muguwar matsala sai kaga lokaci guda komai ya koma maka daidai, ka wayi gari ka ganka cikin ni'ima, hatta mutanen da suka dinga hantararka suka dinga aibantaka sai ka ga duk sun dawo fadawanka. Ikon Allah kenan mai juya lamari a lokacin daya so. Ya azurta wanda Ya so, alokacin da Ya so.
 
Wata gurguwar mata ce ta tuƙo keken guragunta ta isa inda Alawiyya ke zaune tana ta kuka riris, mijinta Dr. Faisal na ta lallashinta tamkar yana ƙara mata ƙaimin kukanta. Cikin sanyin jiki tsohuwar ta dafa kafaɗar Alawiyya tace, "Haba  ke ko, kullum sai kin saka mu kuka a cikin gidan nan, bayan ke ce kullum ke saka jama'ar gari dariya a waje, me yasa kika zaɓi saka mutanen da suke da kusanci dake kuka madadin dariya ne Alawiyya?" 
 
Cikin Muryar kuka tace, "Kaka wallahi ko da yaushe ina ganin Jiddah da Mama a mawuyacin hali, duk sanda nayi istihara na kwanta sai na gansu a mummunan hali, shin taya ba zan koka ba? Babban abin da yasa na karanci lauya don kawai na ƙwatarwa yara da mata haƙƙinsu kan mugayen mazajensu na dinga ƙwatarwa yara irinsu Jiddah haƙƙinsu kan iyayensu, amma a banza ban samu damar ganin Jiddah ba alokacin da burin nawa ya ci ka ba, shi yasa kika ga ban taɓa amsar kuɗin Shari'a ba indai ta shafi neman ƴanci ne ta yara ko mata ba, duk saboda Ni kaɗai nasan wace irin rayuwa mu kai a Lagos Ni da Jiddah. Sannan a gabanki na ida rayuwata mai cike da tsana da tsangwama asalima kina cikin mutanen da suka fi kowa nuna min tsana da tsangwama a lokacin. Shin taya ba zan kuka ba idan na tuna cewa mutane biyu da suke da muhimmanci a rayuwata basu tare da ni kuma ban da tabbacin suna cikin aminci ko akasinsa? Don Allah ku dinga min adalci akan dukkan lamurrana Kaka indai... Maganarta ta maƙale lokacin da gidan talabijin suka hasko fuskar wata mata ɗaure da ankwa ana faɗin ta kashe mijinta mai suna Captain Aliyu Masani wanda suke zaune a cikin garin Kaduna, shi dai  marigayi sojan yana da mata uku ne amma Fatima ita ce amarya a cikin matansa, wanda sun yi aure shekaru masu dama da suka shuɗe... Sai dai ganin Alawiyya akai ta sulmiyo daga kan kujerar da take ba numfashi.
 
A daidai lokacin wayar Alawiyya tai ƙara, Faisal ya ɗauki wayar don yaga sunan mahaifin Alawiyya ne ke yawo kan wayar, shima a cikin muryar tashin hankali yake cewa, "Maza ki kunna talabijin ki ga Fatima wai ta kashe mijinta! Wallahi nasan Fatima ba zata taɓa kashe mai rai ba, balle mijin da take aure ba."
 
Shi dai sai ya samu kansa da gayama Daddyn abin da ya faru da Alawiyya sakamakon kallon matar da tai itama.
 
Cikin tashin hankali ya ce, "Maza ka shafa mata ruwa tai waya can Kadunar ta tabbatar da ita ce zata tsaya ma mai laifin." Kafin Faisal yace komai ya kashe wayar ga alama gidanma zai nufo.
 
Alawiyya na farfaɗo wa ta jawo wayarta, bugu biyu aka ɗauka, domin kowa yasan wacece Barista Alawiyya, lauyoyi da dama suna son buga Shari'a da ita, musamman don su samu damar samu sunansu ya yi tambari a duniyar jaridu. Duk da cewa sun san duk wanda ya tsaya kotu buga Shari'a da Barista Alawiyya to tabbas shi ne ke faɗuwa amma ba su damu ba, saboda ita ɗin ta musamman ce a fagen iya aiki da nuna ƙwarewa kan aikinta.
 
Cikin Muryar kuka take tabbatar da cewa ita ce zata kare matar data kashe mijinta. Ba wani ja aka amsa mata don sanin wacece ita.
 
Cikin lokaci kaɗan ta shirya kayan da take buƙata, a bakin gate ɗin gidan sukai karo da motar mahaifinta shima ya zo, don haka a waya kawai su kai magana suka cinna kan motarsu suka kama hanyar Kaduna cike da tashin hankali da muguwar fargaba.
 
Tabbas ko a mafarki taga mahaifiyarta sai ga gane ta balle a fili, duk yadda ta sauya ta lalace ta fice hayyacinta hakan bai hana ta gane ta ba, to tsohon mijinta ma ya gane ta balle ita da ta tsugunna ta haifa? Tabbas zata baje duk wata basira da hikimarta tare da ƙwarewarta domin tabbatar da gaskiyar abin da ke faruwa da mahaifiyarta.
"Wallahi ba zata kashe mutum ba Mama." Cewar ta da ƙarfi tana jin tamkar tai wauta data taho a mota inama ace a jirgi ta nufi Kadunar tabbas da ya fi sauri.
Shi ma ta ɓangaren Alh. Bello abin da yake rayawa a ransa kenan, me yasa ba jirgi suka hau ba? Kada fa kafin su je wani abu ya sameta! Fatima har zuwa yanzu kina nan da kyanki duk da tarin wahala da jigatar dake shimfiɗe a jikinki sai da na gasgata kyanki na kuma amince da bake kika kashe mijinki ba sam." Sai surutu yake shi kaɗai, Allah ne kawai ya kai su Kaduna lafiya.
 
Suna isa kai tsaye office ɗin da aka kai ta suka je, har an kaita gidan yarin dake Kabala Custom ajiya kafin a fara Shari'a.
 
Cikin sauri aka tarbi Alawiyya don kowa yasan ta kafin ma tace ga ta an gane ta.  Neman izinin mai laifin tai, nan take aka bata dama ta je ta zauna inda zata gana da ita.
 
Zaune take ita kaɗai a ɗakin cikin duhu kasancewar mijin nata babba ne a gun aikinsa, ba ƙaramin duka da izaya ta ci ba kafin a kawo ta nan wajen ba, addu'a take Allah Yasa ta mutu kafin ma a fara Shari'ar, fata take Allah Ya ɗauki ranta ta huta da baƙar rayuwar da take mai cike da ƙunci da takaici.
Har zuwa yanzu ta kasa cire ɗiyarta da danginta daga cikin zuciyarta rayuwa take kawai tamkar matta, ita daman tasan ba banbanci gareta ba tsakaninta da gawa ba, domin rayuwar da take ciki mutuwa ta fi sauƙi a gare ta... "Ke munafuka maza ki taso an zo gunki. Amma wallahi ban so Barista Alawiyya ta shiga case ɗinki ba, munafukar Allah ta'ala sai wani sinne kai kike kamar mutunniyar arziƙi, amma ta banza ce." Ta dinga ingiza ƙeyarta tana tujara da masifa kamar mijinta ne ta kashe ko ubanta.
 
Tana zuwa ɗakin Alawiyya ta ruga ta rungume ta sai kuka ya ƙwace mata mai  cin rai.
 
"Mamana! Mamana! Mamana! Ina kika shige ne? Wace duniyar kika tafi kika barni? Mamana me yasa kika manta da Ni?"
 
Kamar ko da yaushe haka ta ɗauka Yau mafarkin ɗiyarta take, sai dai Yau kalaman ɗiyarta sun sha bambam dana ko da yaushe da take yi.
 
"Fatimaaa! Ya ja sunan da ƙarfi ya iso daf da su, sai dai ita ɗin ba matarsa ba ce, don haka ya riƙe Alawiyya gam madadin Fatimar.
 
Kamar muryar Bello take ji, namijin da har duniya ta naɗe bata taɓa samun wanda zai ko da kama rabin yatsansa ne a gunta. Mutumin da ya nuna mata soyayya da kulawa ba ƙyama ba mugunta ko da yaushe cikin tattashinta yake. Tabbas mafarkin Yau insha Allah wanda zai tafi da ruhinta ne, don haka ta nemi sulale don kar ta mutu a tsaye.
 
Sai dai Alawiyya ba ƙaramin riƙo tai mata ba, hakan yasa ta fara fahimtar kamar da gaske ba mafarki take ba, kamar fa da gaske jikin Alawiyya take, to idan haka ne muryar Bello da ta ji itama da gaske ne yana gun? Allah Sarki da ace tana gani da taga yadda Alawiyya ta girma ta koma da taga yadda Bello ya koma shima amma babu idanu sam bata gani.
 
Kuka sosai kowa ke yi gun, abin da yasa Gandurobar da ta kawo Fatima leƙawa, hantar cikinta ta kaɗa ganin yadda Madam da kanta ke kuka ta rungume matar ga wani Alhaji dake tsaye yana share hawaye da gani shi ma mai faɗa aji ne a ƙasar baki ɗaya.
 
 
Sun jima a hakan sannan Faisal ya ɗauko darduma mai girma ya shimfiɗa kowa ya zauna. Ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, lokacin da suka ga Mamar Alawiyya na lalube lokacin da zata zauna,alamar bata gani ta makance.
 
"Fatima yaushe kika daina gani?" Cewar Daddyn Alawiyya yana share hawaye.
 
"Labarin mai tsawo ne Baban Alawiyya, amma waye ya baku labarin ina nan?" 
 
"Cikin talabijin muka ga sanarwar abin da ya faru Fatima." Cewar Daddyn Alawiyya karo na biyu.
 
Alawiyya kuwa har ta fara nazari matsayinta Na lauyan da tasan abin da take yi, taya makauniya zata kashe mijinta? Cikin sauri ta miƙe tsaye ta kalli Daddynta tace, "Daddy bari na je na amshi file ɗin case ɗin naga yadda aka yi kisan."
 
"To ɗiyar kirki sai kin dawo." Cewar Daddyn Alawiyya, Faisal kuwa ya tashi ya bi bayanta, domin duk inda zata je indai bai aiki to tare yake tafiya da matarsa domin ya bata kariya, duk da ko da yaushe cikin addu'ar mutane data iyaye take.
 
Har babban Ofishin ta je, ta amshi File ɗin ta koma cikin mota ta fara karanta wa.
 
"Fatima ta kashe mijinta mai suna Captain Aliyu Masani ta hanyar yanka shi a wuya, sannan kuma ta caka mai wuƙa a ciki har sai da rai ya yi halinsa."
 
Gwauran numfashi ta ja, kafin ta sake nazarin zancen.
 
Taya makauniya zata yanka mutum har kuma ta caka mai wuƙa? A yadda taga hoton marigayin yana suffar sadaukantaka, kuma yafi wadda ta kashe shi karfi ko a kallon jiki nesa ba kusa ba...
Wayarta ce tai ƙara, ganin baƙuwar lamba kamar ba zata ɗauka ba, amma ganin wayarta ce ta wajen aiki sai ta ɗaga kiran.
 
"Ina magana da Barista Alawiyya Bello ne?" 
 Ba tare da wani jinkiri ba ta amsa da cewar, "Tabbas kana magana da ita ne, wane taimako zan maka?" 
 
Wata mahaukaciyar dariya aka saki wadda sai ta kauda wayar daga dodon kunnenta, ya yi mai isarta sannan ya ce, "Ina son ki yi gaggawar ficewa daga case ɗin da kika amsa na Fatima da ta kashe mijinta, idan ba haka ba za ki fuskanci ƙalubale wanda baki taɓa cin karo da shi ba ko a mafarki. Ki sani idan taƙamarki taurin kai to kin zo madakata, domin kin zo fagen da taurin kai bai amfani asalima bai da waje a gurinmu." Kit ya kashe wayar.
 
Wani malalacin murmushi ta saki, tabbas shari'ar irin wadda take so ce, ta jima batai Shari'a irin wannan ba mai cike da wasa da faɗaɗa ƙwaƙwalwa ba.
 
Wani ma ya yi rawa balle ɗan makaɗi! 
 
Tabbas sai ta bankaɗo asalin masheƙin Marigayin indai ta cika ita ɗin ita ce Barista Alawiyya wadda mutane ke jinjina wa baiwa da hazaƙar da take da ita wajen nuna ƙwarewa a aikinta.
 
Faisal da duk ya ji abin da ya faru a wayar sai tsoro ya kama shi, cikin damuwa ya dube ta ya ce, Hubby akwai matsala kuwa a wannan lokacin, domin ga dukkan alama akwai mutane na daban dake ɗauke da alhakin ɗaukar mataki kan duk wanda ya shiga cikin shari'ar... "Dakata Faisal! Kana nufin saboda wasu ƙananan ƴan daba da basu san abin da ake kira da Shari'a ba zan yi zaune na kame kaina da bakina tare da aikina na bar mahaifiyata a cikin wannan yanayin? To wallahi tallahi indai ina raye sai na buga Shari'a mai cike da abubuwan al'ajabi da mamaki kai wallahi sai na nuna wa ko su waye cewa sun taɓo tsulayar Dodo, ba zan rangwanta ba, haka ba zan sassauta ba, sai na gurfanar da masu laifin gaban hukuma, sannan na nemi kadin haƙƙinta na ɓata mata suna da akai ba zan gushe ba sai na yi lalalar da zan hambaɗe duk wanda ya yi ma mahaifiyata karan tsaye a rayuwarta ba zan ƙasa a gwiwa ba sai na tabbatar da cewa ko kare ne ya taɓa yi ma mahaifiya ta kukan da bai mata ba sai na nema mata haƙƙinta balle mutum mai ɗauke da ƙafafuwa da hannuwa haƙora talatin da ƴan kai a bakinsa."
 
Zuwa yanzu tantama yake anya kuwa matarsa ce Alawiyya da ya sani macen da bata ɗaga murya gabansa, macen da bata taɓa kiran sunansa amma Yau ga shi har tsawa take mai mai cike da firgitarwa.  Dole ya kama kansa kafin ya yi abin da zai ɓata ran matarsa a banza.
 
 
Can gun ta koma amma sai ka tabbatar mata da cewa lokacin ganawa da Mamar ya wuce sai dai su dawo gobe.
 
Haka suka taho suka bar Mamar a yanayi na ban tausayi.
 
Gidan Alawiyya dake Kaduna suka sauka a nan NDC unguwar Kaji bayan gidan IBB, ko da suka je kowa ba wanda ya kula kowa daga Daddyn har su, da ya yi nufin zuwa ya kama hotel ko cikin gidajensa ya kwana sai Alawiyya tace kar da ya je ko'ina akwai matsala a lamarin.
 
Haka yasa aka ba shi ɗaki guda ya shige shima yana nazari da tunanin wace irin rayuwa Fatima ta yi bayan rabuwarsu.
 
 
Alawiyya kuwa sallah tai ta gama ta zauna kenan zata fara bincike kan lamarin wayarta tai ƙara cike da gamsuwa da kanta ta ɗauki wayar.
 
"Watau ke baki jin kashedi ko? Ina son ki sani idan dai kikai gaggawar binciko gaskiya kamar yadda kika saba to wannan gaskiyar za ki binciko ta ne da tukuicin ran mahaifinki da mijinki."
 
Kamar yana gabanta haka ta daka mai tsawar gaske tace, "Anya kuwa kasan wacece Alawiyya a duniyar Shari'a kuwa? Ina so ka sani ban jin nishaɗi sai ina sauraran waɗannan banzajen maganganun naku masu sakamun nishaɗi a zuciya, kada ka sake ka sake kirana idan dai ba albishir ɗin ka kama mijin nawa ko uban nawa ka kira kai min ba.
 
Amma ina son ka sani nan da kwana kaɗan zan binciko duk wani sirri da kaidin abin da kuka aikata." Kit ta kashe wayarta ta faɗa kan gado tana tunanin Mamarta.
 
 
To masu karatu abin ya ɗauko zafi fa.
 
Alawiyya ta ga mahaifiyarta amma da laifin kisan kai.
 
Wace irin rayuwa Alawiyya tai bayan rabuwarta da Jiddah?
 
Ya Mustapha yake ciki da gidansa? 
Ina Jiddah take da halin da take ciki?
 
Ku dai kar ku damu ku ci-gaba da bibiyar alƙalamin Haupha don jin wannan cakwakiyar gaske data kunne kai.
 
Taku a kullum Haupha!!!!