ANA BARIN HALAL...:Fita Ta Huɗu
"kaiiii" naji muryan Habiba tana faɗin, sisto juyo kiga wasu farare tare da yayah Ahmad kaman wasu halfcast, da sauri na juyo ina duban su, nace "hala twins ne, ina Yayah Ahmad ya samo fararen mutane haka? Har sun fishi fari" muka haɗa ido nida Habiba, sbd kowani magana ɗaya tayi tou ɗaya tasan ina maganar ɗayan ya dosa, riƙo hannu na habiba tayi muka ƙarasa wurin Yayah Ahmad, hafsy na binmu abaya tana cewa, "inaga fah inyamure ne, don farin su yayi yawa, ko kyau basu mun ba sbd farin su yayi bauu, amma kukuma nasan sun burgeku, mayun farare kaman ku ba fararen bane", babu wacce ta kula ta muka ƙarasa wurin yaya Ahmad.
ANA BARIN HALAL...:
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*PAGE* 4
Muna shiga SS 1, first term ɗin mu aka fara shirin biki Yaya mohd, wanda bai wuce 2weeks ba ayi,
Wani farin ciki nakeji sbd bikin da za'ayi a gidanmu, gashi Yayah Ahmad ya mana ɗinkuna kusan kala biyar-biyar mu da su Raliya, abun daɗin ma har da Maryam friend ɗinmu, mudai shagali babu kama hannun yaro, gashi dodon mu baya nan, don sai ana satin ɗaurin auren naji ance zaizo, kuma fah Yaya Umar duk zafin shinnan yana mana so na ban mamaki, shidai daga mamie tayi wani rashin hankali ne zaki ga ya wargaza hankalin kowa a gidan, don ni gaskiya bansan wani irin so yakeyi wa Ummie ba.
Biki ya kankama Aunty Asma'u tazo haka ma Adda ta iso, abun farin cikin ma nida Habiba an bar mu zuwa maiduguri wurin event ɗin amaryah, wanda tafiyan mu da Aunty Asma'u ne.
Aunty Asma'u , Adda, da goggo ƙanwar ummin mu duk zasuje, sai kuma wata ƴar ƙawar ummin mu, sai ni da Habiba za'ayi tafiyan, mota biyu zai ɗauke mu, Yayah ishaq zai ja motan Aunty Asmau, Yayah Umar zaija motan Adda, sai kuma gayyan motan abokan ango da zasu ɗauko amare, Yayah Ahmad dai da Abba zasu haɗa hanya, su kuma ana gobe ɗaurin aure zasuje da tawagar Abba.
Maiduguri munga karamci munga kara, an mana karɓa na ban girma, munga shagulgula na har kan arziki da mutunci, a mutunce akayi komai aka gama, ranan ɗaurin aure muka kama hanyar Bauchi cike da farin ciki, ga kyakkyawar amaryar mu Aunty Bintu.
Mun iso bauchi wuraren ƙarfe uku na yamma, haka kuma a gurguje aka shiryah domin buɗan kai da za'ayi a gidan mu.
Aunty Rakiya ne ƙirjin biki, sai kai kawo takeyi a filin gidan mu, inda ake decorating wurin saboda buɗan kai, ana sallan la'asar wurin ƙarfe biyar aka fito wurin buɗan kai, ranan naga washe baki a wurin Yayah Mohd, ashe yana fara'a haka? Mudai muyi nan muyi nan, gaba ɗaya farin ciki cike da zuciyar mu, anyi taro lpy an gama lpy, inda amaryah da ango sunga karamci, su kansu ƴan maidugurin sun yaba da karɓan da aka musu.
Bayan sallan ishaa akayi rakiyar amarya gidan ta dake *TAMBARI ESTATE* Gida ne mai ɗauke da flat guda uku, ko wanne yana ɗauke da three bedroom da parlor 2, Abba ne ya gina musu su uku ƴan samarin shi, wanda ansha artabu da mamie lokacin da Abbah ya ɗauke su sukaje ganin gidan, don ko gaya musu yana ginin baiyi ba, sai da aka saura 1month bikin ya kaisu, ya kuma shaida musu halak malak ya damƙa su, amma na yayah mohd ne kawai akayi penti, sauran biyun yace kowa ya tashi auren shi ya fente.
Mamie kasa daurewa tayi a lokacin, zuciyar ta kaman zai fashe tana huci tacewa Abba, "amma dai Abban su duk wani dukiyarka anan ka ƙarar ko? haba jama'a idan mutum yace ba'a mishi adalci ace ba haka ba, yanzu namu yaran idan sun tashi aure sai ace komai ya ƙare, kuma ana magana ace kishi ne", ta faɗa kaman zata fashe da kuka.
Tana rufe bakinta, mamah tayi charaf tace," wa na zaice kishi? Sai da ace hassada da jahilci, idan bake kanki baya saiti ba mutum da ƴaƴan shi har kina da bakin cewa wani abu idan ya musu har kan arziki? Wannan hassada naki akanki zai ƙare, naki yara matan cewa akayi ya basu wurin zama idan zasuyi aure ko me?"
Harara mamie tayiwa Mamah ƙasa-ƙasa don tana shakkanta kuma tana tsoronta,
Abba ne duk ya dakatar da su idon shi akan mamie yace, "matsala ta da ke baki da wayo, baki da dabara, huruminane ko kuma dole nane akan ƴaƴana mata? Kinga anyi auren su sun wofinta ne? Don Allah Halima bana son rashin hankalin ki, shiyasa abu dayawa bana son sanar dake sbd ƙorafinki da nuna kishinki akai". Ya faɗa yana barin wurin ya wuce wurin motan shi.
Ummin mu batace komai ba sai murmushi dake sauƙe akan kyakkyawar fuskanta, haka zalika daga Yaya mohd, Ahmad, umar, ni da sauran ƴan'uwa na mata babu wanda tace wani abu, sai duk muka juya mukabi wurin mototi guda biyu da mukazo a ciki, Raliya ce kawai cikin mu take ta wani harare hararenta na banza da wofi, mudai cike da farin ciki.
Bayan ankai amaryah gidan ta, ana ta saka albarka, a gidan da musu fatan zama lpy, kaii Aunty nice gidan yayi kyau, ranan na ƙara tabbatar da ƴan maiduguri ƙarshe ne a wurin ƙyale, gidan nan kaman kada mu tafi ga wani ƙamshi kaman babu gobe, inda muke tsaye nida Habiba da maryam wata yar Aunty Bintu ce tsaye, suna ce mata yah falmata, nidai matsawa da hanci nakeyi ina shinshina laffayanta Aunty nice, tafaɗa fuskanta ɗauke da dariya, nima ina dariyan nake ƙara maida hankalina kanta, sannan nace mata ae Hajjajo ƙamshi rahma ne, tana dariya tace rahma ɗaya ko biyu, ae nidai tun ranan naji babu abinda nake so irin ƙamshi, muna ji muna gani Yayah umar ya tiso ƙeyar mu muka dawo gida, wanda har ga Allah bamu so ba, a wautar mu bamu ƙi kwana a chan ba.
Da safe kuwa bayan sun karya sun shiryah suka biyo gidan mu domin yin sallah ma da mutanen gidan mu, saboda ranan duk zasu juya maiduguri, wurin 11:00am duk sun kama hanya cike da karamci irin namu na ƴan bauchi da iyayen mu suka shiryah musu.
Bayan biki da sati biyu yayah mohd ya kawo Aunty Bintu gidan mu ta gaishe da iyayenmu, murna kaman babu gobe, don muna dawowa gida daga school muka ganta a parlon Ummin mu tana zaune, a gefe ɗaya kuma ummin ce zaune suna ɗan taɓa hira kaɗan kaɗan, tunda dama akwai sabo a tsakanin su, da gudu naje na mata oyoyo baki na kaman zai tsage don murna, itama fuskan ta cike da farin ciki tace, "ae nayi fushi daku Aysha, daga ke har habiba babu wanda ya leƙoni"? Ina dariya nace zamuzo Aunty Bintu, mun koma school ne ga kuma Haddan mu an matsa mana zamuyi sauƙa this year.
"Masha Allah" Aunty Bintu tace, sannan na miƙe nayi ɗakin mu domin na chanja kaya.
Har sao wurin nine na dare tukun yayah mohd ya ɗauke ta suka tafi, nida hafsy da habiba har wurin mota muka rakata, muna mata alƙawarin ɗin zuwa mata ranan friday.
Motan su bai gama fita ba motan yayah Ahmad ya shigo gidan ,muma fasa wucewa mukayi cikin gida domin mun jiran ƙarasowan shi, don yamana alƙawari bai cika ba, gara kafin ya bar garin a san nayi.
Bayan sun gaisa da yayah mohd ya ƙaraso ciki da motan shi, yana buɗewa muka ganshi bashi kaɗai bane ashe, tare da wasu abokanshi muka gansu.
"kaiiii" naji muryan Habiba tana faɗin, sisto juyo kiga wasu farare tare da yayah Ahmad kaman wasu halfcast, da sauri na juyo ina duban su, nace "hala twins ne, ina Yayah Ahmad ya samo fararen mutane haka? Har sun fishi fari" muka haɗa ido nida Habiba, sbd kowani magana ɗaya tayi tou ɗaya tasan ina maganar ɗayan ya dosa, riƙo hannu na habiba tayi muka ƙarasa wurin Yayah Ahmad, hafsy na binmu abaya tana cewa, "inaga fah inyamure ne, don farin su yayi yawa, ko kyau basu mun ba sbd farin su yayi bauu, amma kukuma nasan sun burgeku, mayun farare kaman ku ba fararen bane", babu wacce ta kula ta muka ƙarasa wurin yaya Ahmad.
Hannu ya miƙo mana yana "ƴan biyu Abba yyh kuke? Fuskan mu ciki da farin ciki muka miƙa mishi hannun mu mukayi musabaha, ranƙwashi ya kaiwa hafsy yana cewa, "jerry ina tom"? Baki ta turo tana "Allah sarki yayah Ahmad niƙan a gidan nan kaman kowa bai damu dani ba wlh, kowa Sai ƴan biyun Abbah"? Ta faɗa tana hararan mu nida habiba, mudai dariya mukeyi muda Yayah Ahmad, juyawa yayi yana duban abokanshi cikin shiru-shirun shi da rashin son sakewa da dogon magana yace, M.G, da A.G ga sisters ɗina, yana nuna mu yace waƴan nan sune favourite sister ɗina, suɗin kaman twins suke ga hankali, wannan kuma yana nuna hafsy yace autar mu kenan, ita kuma twin sister nata halin su ɗaya basuji, yadda kasan tom and jerry haka suke, basujin magana basu son zaman lpy", ya faɗa yana riƙo hannun hafsy data turo baki tana hararan mu.
Wanda naji yayan mu ya ƙira da M.G da AG ɗin muka juya muna gaishe su, suma cike da murmushi a fuskansu suka amsa mana, inda ɗayan bayan gaisuwan bai sake cewa komai ba, saidai fuskanshi ɗauke da murmushi yana duban mu, shima ɗayan fuskanshi cike da murmushi yake ƙara mana tambaya akan ajin mu nawa? Habiba ce ta gaya mishi ajin mu da sunan mu, bayan ya sake tambayanta, sannan ya dubi hafsy yace ke kuma kece tom ɗin ko jerryn?
Dukkan mu dariya muka kwashe da shi, banda ita da tasake turo baki gaba tana cewa, "wallahi sunana hafsy ne"
Kawai dai kowa a gidan yafi son sune shiyasa ba'a ganin laifin su, amma wlh manyan ƴan tawayen gidan mu kenan, kuma basu ji ga iya haɗa munafurci," ta faɗa tana ture hannu na da nakawo kusa da ita, yana dariya yace, "tou nidai banga alama ba, nima ina ga sune favourite sisters ɗina, ke kuma inaga friend ɗina zaki zama" still dai fuskan shi cike da fara'a, daga gani shi yana da ɗan surutu, amma ɗayan tunda ya amsa gaisuwan mu bai sake cewa komai ba, saidai yana bin dukkan mu da kallo, shima kuma fuskan shi cike da murmushin, amma dai bai sake tankawa ba.
Wucewa side ɗin su Yayah Ahmad sukayi, bayan muma mun juya side ɗin Hajiya Ummah, hafsy ko hararan mu tayi ta wuce cikin gida, kaman wasu munafukai, muna shiga parlon hajiya umma muka zauna a kujeranta two sitter muka haɗa kanmu wuri ɗaya domin tattaunawa, kallo ta bimu baki a buɗe tace, "wannan munafurcin da baya sakin ku kuma fah" kudai yaran nan kullum aka ganku cikin nuƙu-nuƙu na gulmah kuke, nidai duk wacce tayi gulma na nabarta da Allah, domin duk abun mutum da gulmanshi nan gidan ɗanane, iko nane, idan ma hassada kukeyi ya kawo ni nan sai kuyi tayi" ta ƙara faɗa tana hararan mu.
Mu dai dariya muka kwashe da shi muna kallonta, habiba ce ta bata amsa da, "in banda ke hajiya ummah gorin na menene? Muma idan muna raye zamu haifi yaran da zasu mana gida gidan sama ma mu wataya, bake da aka miki ɗan akurki ba," ta faɗa tana taɓa ƙafa na, don mun san yau zamusha gori iri-da kala, don hajiya ummah ji takeyi mu kishiyoyinta ne a wurin Abban mu, don ko shigowa mukayi tare da shi ta dinga hararan mu ƙasa-ƙasa, watar tace amma dai kai kan jakin ƴaƴa nane, baka kama gabanka suma su kama gaban su? Amma kullum kana naniƙe da su, su hanaka yin abun kanka?
Aiko kaman habiba ta jefa mata ƙarfe a tsakarka ta zabura tana nuna mu da yatsa, "ahir ɗinku wlh, don babu wacce zata haifi ɗa irin wanda na haifah, don ni ɗana ɗaya ne tamkar da dubu,don ko gwabna bai kai shi kuɗi ba, gwamne me a kusa da a kusa da usmanu nah? Ae inaga idan gwamnaty ta kasa biyan albashi usmanuna zai iya bawa gwamna bashi yayi albashi na wata ɗaya kam, kuma arzikin shi bai taɓu ba, don kaf Tafawa ɓalewa ba'a taɓa haihuwa irin nawa ba, kawai dai ya haɗu da jarabawan tara mata marasa abinyi ne sai abun da ya musu", ta faɗa tana mana kallon banza.
Dariya muka kwashe dashi, habiba tana cewa, "a tafawa mahaifiyar Ɗangoten bauchi" bakuyi gatse ba marasa kunya ni nan da kuke gani nafi uwar ɗangote farin cikin haihuwar ɗa mai albarka,
Hajiya Aysha tana duba na cike da dariya tace, "Aunty nice kinsan kakarmu irin mutane ne masu son nasu, kuma har cikin zuciyarta ji take duk ƙasan nan babu wanda yakai Abban mu sukuni, shiyasa muke manna mata hauka akan Abban mu yafi gwamna kuɗi, kuma ta hau ta zauna," Dariya nayi ina ƙara maida hankalina wurin Hajiya Aysha, ina kuma ƙara jinjina irin baiwar kyau da Allah ya mata, domin murmushi fuskanta ba ƙaramin kyau yake ƙara mata ba
*AUNTY NICE*
managarciya