WATA UNGUWA: Fita Ta Takwas
p8
BABI NA TAKWAS
A tsakiyar wani ɗan madaidaicin gida wata ƙatuwar tabarma ce aka shimfiɗa ta a tsakar gidan yara ne 'yan ƙanana ga su nan kamar ƴaƴan ɓeraye a kan yawa, sai ƙiriniya wasu daga cikinsu ke yi.
Daga gefe kuma masu ɗan girma daga cikin su ne ke cin abinci sun tasa kwano a tsakiya sai rige-rigen ci ake.
Can Safiya ta yi saurin wawurar tarin shinkafa da naman da ke gaban Na'eesha.
Na'eesha da saurin hasala ko tsayawa jin ba'asi ba ta yi ba ta katantamo wata ashar ta danƙara "Kan kaza-kaza!" kawai sai ta wanke ƙanwar tata da mari ji kake tas!.
"Lalalala! Ni kika mara?" Cewar Sadiya yar kimanin shekaru goma sha takwas da ke dafe da kunci.
"An mare kin uban wa ya ce ki ci mun abincin gabana....?"
Kafin ta gama rufe bakinta ta ji saukar wani gigitaccen mari da ya kiɗima ta, da sauri ta juya tana waige-waige ko za ta ga gardin da ya mare ta, domin ba ta taɓa tsammanin wai Sadiya ce ta iya aikata hakan ba.
Ko da ta fahimci haka, sai ta harzuƙa ainun ta kama kan yarinyar ta maka da bango tana kai mata naushi ta ko'ina.
Cikin hanzari Inna Halima ta jefar da butar hannunta ta yi gun da sauri ta ƙwace Sadiya a hannun Na'eesha tare da ture Na'eeshar gefe ta ce "Amma ke dai wannan yarinyar akwai halin banza, don zalunci haka kawai ki kama yarinya da bugu, ka ga shegiya mai kama da aljanu?"
"Ban haifi azzaluma ba, haka ban haifi shegiya ba ga shegiya nan a gabanki ita da ta tasarwa zambo, kuma ita ta ja." Mama Rakiya da ke zaune a ɗakinta tana jiyo su ta faɗa tana ƙoƙarin tashi ta nufo wurin.
Cikin masifa inna Halima ta nufo ƙofar ɗakin tana faɗar "Ke Rakiya ki fita idona in rufe, in masifa ki ke ji na fi ki iyawa yanzun sai mu yi namu, ashe ma kina jin su da yake kin ga yarki ce babba shi ne kika zuba ido ana zaluntar 'yata?"
Wata ƙatuwar dariya Rakiya ta saki tare da faɗar "Yaya Halima kenan, kin san ni ban cika shiga sha'anin yara ba kamar ke, barin su na yi mai ƙarfi ta ƙwaci kanta. Sannan faɗa da ni ba daɗi ke kin sani yanzu za ki kirawa kanki ruwan da ba za ki iya tare su ba."
Habawa ko da inna Halima ta ji haka sai ta harzuƙa ainun, nan fa su ka hau cecekuce dama kowa zuciyarsa a baki take.
Sosai suke musayar yawu kamar za su daku, yara masu wasa suka dakatar sai kallonsu suke, wannan na faɗar 'Innarmu tafi ƙarfi, wancan ya ce namarmu tafi zuciya, to ku bari dai mu ga wa za a yiwa kaye." Haka yaran suke ta faɗa a tsakaninsu suna ci gaba da more kallon faɗan.
Suna tsaka da haka ne Sakina ('yar gidan iya mai bakin Aku) ta shigo gidan da sallamarta ta zo siyen lalle wurin Lantai (ɗaya daga cikin matan gidan) sai dai ko da ta zo ƙofar Lantai a rufe hakan ya tabbatar mata da ta fita sai rigima da ta tarar Ana yi.
Talatu (matar gidan) da ke kwance a ɗaki tana jin duk bidirin da ake, sai yanzu da ta ji sallama ta leƙo tana faɗar "Me kike so Sakina?"
"Am Lalle na zo siya." ta faɗa tana kallon ɓangaren masu faɗan.
Da alama gabaki ɗayan hankalinta yana gun masu rigimar tana ɗaukar rahoto.
"Af! Wannan ne dama? To kawo kuɗinki na ba ki, ga shi ta bari a guna."
Ba musu ta miƙa kuɗin lokaci ɗaya kuma tana ci gaba da kallon dramar da ake a gidan.
Can Talatu ta miƙo mata lallen tana faɗar "Ga shi sai ki yi azama, da alama in kika tsaya kallon dramar gidan nan za ki kwana a nan ko kanki ya faɗo." Tana 'yar dariya ta yi maganar tare da shigewa ciki abunta, a cewarta ba abin da ya yi mata zafi da faɗan kishiyoyi balle ta yi katsalandan na rabawa.
Sakina kuwa tafi mintuna biyar a wurin bayan ta karɓi lallen, sai da ta tabbatar ƙurar faɗan ta lafa. Sannan ta fice zuwa gida sai sauri take kamar za ta wuce ƙafafunta. Alla-Alla take ta isa gida don ta fesawa uwar tata abinda yake faru a gidan Audu mai'iyali.
Da misalin ƙarfe takwas na dare malam Audu ne zaune a tsakar gidansa kan tabarma, da yake yanayin yau akwai damar sanyi, hakan ne ya ba shi damar zama waje.
Mama Rakiya ce ta durƙusa a gabansa tare da ajiye masa kwanon abinci, da yake ita ke da girki a ranar. Bayan ta gaida shi ta shiga gabatar masa da abincin ta hanyar buɗa masa kwanukan.
A daidai lokacin ne Inna Halima ta zo ta zauna kan tabarmar tana faɗar "Ranka ya daɗe Barka da dare." "Yawwa Halima barka dai ya gida ya yara?"
"Alhamdulillah!" Ta faɗa tare da jefa hannunta cikin abincin da Rakiya ta ajiye masa a yanzu, don neman magana.
Ai kuwa ta samu abinda take so domin Rakiya ce ta ƙaraso wurin tare da ture ta tana faɗar "Malama ba ke na ajiyewa abincina ba, don haka wallahi ba za ki ci ba." Malam Audu da har ya yanko loma zai kai baki ya dakata tare da kallon Rakiya da wani yanayi ya ce "Miye haka ne Rakiya? Rashin son zaman lafiya ko me?"
"Malam ba ka ga ita ke neman fitina ba? Ga nata abincin can na saka mata me ya sa ba za ta ci ba sai wannan?."
Karaf Halima ta ce "Ai na ji wannan yafi daɗi ne har da mai fa aka saka don gyara kwanon maigida." Ta ƙarashe tana afa loma ta biyu da gayya.
Cikin Masifa Rakiya ta ce "Kin san Allah yaya Halima ba zan bari ki ƙara ci ba, don ba girkinki ba ne kin zo kin zauna mun a Shimfiɗar miji na ƙyale ki."
Ganin lamarin nasu na neman wuce gona da iri ya saka a kufule malam Audu ya zube abincin hannunsa ya miƙe yana faɗar "Shi ke nan Rakiya ga abincinki nan an bar miki, ni ma ba zan ci ba, tunda abincin ma ba za ki bari na ci a kwanciyar hankali ba, ga shi nan ki ɗauka ki yi ado da shi, Halima tashi mu je." Yana gama faɗa ya karkaɗe rigarsa ya juya. Da har zai shiga ɗakin Halima kome ya tuna? kuma sai ya yi kwana ya fita waje.
Duk da ba haka Inna Halima ta so ba, amma kuma ta ji daɗin hakan sosai ko ba komai ta ƙuntatawa Rakiya, miji kuma ya goyi bayanta.
Ta sani zuwa yanzu Rakiya ta fahimci duk lalacewar matar fari ba a daina yayinta don ita ke da gida kuma da tsohuwar zuma ake magani.
Malam Audu bai dawo gidan ba sai ƙarfe goma da rabi na dare. Yana shigowa ya leƙa ɗakunan sauran matansa ya musu sallama, sannan ya shige ɗakin Rakiya dake kusa da na Inna Halima.
Dama kowanne ɗaki daga cikin gidan falle ɗaya ɗaya ne, a ciki gado da kujeru da sauran tarkacen matan yake, ɗakin ma ba mayalwaci ba. Sannan ba wani wararren ɗaki da aka tanada don yara, balle a yi zancen masaukin baki. Dai-dai da banɗaki guda ɗaya suke amfani da shi tamkar a gidan haya. Gabaki ɗaya a takure gidan yake, saukar baƙi a gidan zai zama takura ga mai gida da yaran gidan saboda su ma ba su wadatu ba.
A yanda tsarin gidan yake idan Malam Audu yana ɗakin Rakiya to ƴaƴan Rakiya za su rarrabu a ɗakunan sauran matan a nan suke kwanciya. Ga shi kuwa bangwayen ɗakunan duka amanne suke da juna, daga ƙofar wannan sai ta wannan ba wata tazara a tsakani, ko me ake a ɗakin wannan makwafciyarta takan iya jiyowa. A taƙaice dai tsarin gidan bai hau turbar koyarwar ma'aiki (s.a.w) ba.
Washe gari bayan fitar malam Audu wajajen ƙarfe goma na safe, wasu daga cikin ƙananan yaran gidan ne ke ta kwarafniyar shiri zuwa makarantar Allo.
Attahiru (ɗan Inna Halima ƙarami) ya matso kusa da mama dake famar daddaƙawa ƴaƴanta karatunsu kafin su fita makaranta, kamar dai yanda ta al'adanta. Ita ke yi wa yaran gidan bitar karatunsu domin duk a cikin matan ita ce kawai ta wadatu da isasshen ilimin muhammadiya.
Ɗurkusawa a gabanta yaron ya yi ya ce "Mama ni ma yau ban iya ba, biya mun." Wani mugun kallo ta bi shi da shi.
Sannan ta ce "Dama fa kafi kowa zama daƙiƙi a cikin yaran gidan, kuma wallahi yau idan na maimaita sau biyu ba ka iya ba za ka gayawa mutanen garinku, dolo kawai."
Gyaɗa kai yaron ya yi cikin rashin damuwa da hakan kasancewarsa mai matuƙar naci game da karatun duk da bai da fahimta sosai.
Sai da ta karanta masa sau biyu sannan ta ce ya biya ta ji.
Ba musu ya hau karantawa, sai dai ya ɗan kuskure kaɗan.
Har ga Allah mama ba ta yi niyyar yi masa komai ba, kuma tana jin daɗin yadda yake da nacin karatun a ransa, ɗago kan da za ta yi haka ta ga Inna Halima ta fito daga ɗakinta, nan da nan abin da ta mata jiya ya faɗo mata a rai don haka ta yanke hukuncin yin ramuwar gayya a kan ɗanta da ta fi so.
Sai ji kake ƙwas! Mama ta zuba wa Attahiru ranƙwashi a tsakiyar kai da gayya.
A gigice yaron da bai fi shekara tara ba ya ƙwala ihu, ba ta damu da hakan ba ta kama kunnensa na dama ta mirɗe tana faɗar "Kai wai meyasa kai daƙiƙi ne dolo? Ko da yake gado jini yake bi, mai yiwuwa danginku kwanyar kifi suka rayu da ita." Ta ƙarashe tana taɓe ba ki ba tare da ta kalli sashen da inna Halima take ba balle ta saka ran ta gan ta.
Cikin yanayi na tsananin ɓacin rai Inna Halima ta yo kanta tare da ƙwace ɗanta daga hannunta tana faɗar "Rakiya ki fita idona in rufe, meyasa ne ke jaka ce kullum idan ba ki ja abin da zai taɓa lafiyar jikinki ba ba kya jin dadi?"
Hankaɗe yaron nata ta yi can gefe tana dubansa a kufule "Kai kuma mara zuciya tashi ka ɗauki Allonka ka bar gidan nan kafin na sauke zafin a kanka."
Miƙewa ya yi yana kuka don ya ji zafin faɗuwar ba kaɗan ba. Ya ce "Inna ai ban iya karatun ba, kuma wallahi in na je a haka malam duka na zai yi, ki biya mun."
Tofah! Inna da ta san ba za ta iya tayar da shi ba, saboda ita ma iya karatun sallah ta iya, shi ma dai sama-sama. Don haka ta daka masa tsawa cikin borin kunya ta ce "Ni ɓace mun da gani banza mara zuciya."
Ai Attahiru bai san lokacin da ya ja allonsa ba ya fice gidan a ɗari, domin tsawar ta razana shi ainun.
Matan gidan ne suka bushe da dariya su duka. Rakiya ta shiga jujjuya kai na shaƙiyanci ta ce "Ƙaryar iskanci! Su o'o a dai koma makaranta ko a samu na koyar da yara masu tasowa."
Jin haka ya ƙara harzuƙa Inna ta yi kan Mama a zuciye ta kai mata naushi. Ba tare da ɓata lokaci ba Mama ta ɗauko madai-daicin Allon da ke kusa da ita ta yunƙura daga zaunen ta yo kan inna tana faɗar "Ni za ki daka ki yi tunanin kin ci bulus? Ai ba za ta taɓa saɓuwa ba bindiga a ruwa." Nan suka hau yar tsere a tsakar gidan yara yanmatan da suka rage a gidan da sauran matan gidan sai dariyarsu suke yi don su yanzu irin wannan faɗan har ya daina ɗaga musu hankali.
Na'ila (Babbar yar Talatu) ta ce "Wato ainahin Tom and jerry ga su nan a gidanmu, waɗancan kwaikwayo ne." Ta ƙara bushewa da dariya.
A dai-dai lokacin Mama ta zo dab da Inna don haka ta here iya ƙarfinta ta kai mata rafka da Allon da nufin sauke mata shi a tsakiyar ka.
Tsayawa suka yi cirko-cirko kamar zakarun da suka yi faɗa suka gaji. Kowa da ke tsakar gidan ya zaro idanu waje, a take gidan ya yi tsit kamar ba wani mahaluƙin da ke rayuwa a gidan.
Mama ce ta fara dawowa daga duniyar firgicin da ta shiga ta yada Allon ƙasa tare da matsawa kusa da Malam Audu da kansa ke fitar da jini tana afi da magiya "Wayyo Allahna! na shiga uku! Don Allah malam ka yi haƙuri, wallahi ba haka na yi nufi ba tsautsayi ne ya faɗa kanka."
managarciya