Rikicin PDP: A Kyale Wike Yayi Duk Abinda Ya Ga Dama----Sule Lamido

Rikicin PDP: A Kyale Wike Yayi Duk Abinda Ya Ga Dama----Sule Lamido
 

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce babu wani laifi da aka yiwa Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike kuma a rabu da shi yayi abinda ya ga dama. Lamido ya bayyana hakan ne a hirar da yayi a shirin Politics Today na tashar Channels TV.

Yace jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP na da kundin tsarin mulki da dokoki kuma zabe akeyi don zaben duk wani dan takara. 
"Mutane na takarar Kansila; wasu su yi nasara, wasu su fadi. Hakazalika na shugaban karamar hukuma da Gwamna. Saboda haka menene matsalar Wike? A ra'ayina wa yayi wa Wike laifi?" "An yi zaben fidda gwani kuma shi Wike da kansa yace zaben na gaskiya ne babu magudi. Saboda haka menene matsalar"
Lamido yace Wike ya daina tunanin yafi kowa karfi a siyasar jihar Rivers don shine Gwamna.