MAMAYA: Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 61---70

Don haka sallama soyayyata ga Nasir domin yaron yana sonta kuma nasan zai iya riƙe ta yadda ya kamata. Saboda da haka zan sauya masarauta daga kusa da nahiyarsu Bilkisu zuwa can gabashin duniya yadda sai lokaci zuwa lokaci zan dinga zuwa gano wani hali take ciki.

MAMAYA: Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 61---70

Last page 61--70

 

 

 

Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash, tana sauka dajinsu ta yanke jiki ta faɗi cikin galabaita.

 

Sarki Zayyanul murrash yana zaune yana ganin dukkan abubuwan dake faruwa, cikin sauri ya ɓace ya bayyana gaban Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash ya yarfa mata wani ganye dake ɗauke da ruwan magani take a suka ɓace daga gun.

 

Can ɗakin tsafinsa suka bayyana, kan wani tsohon gadon kara ya kwantar da Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash, ya ɗauko wasu kayan tarkacen magani ya fara surutui yana yarfawa a jikinta.

Nan da nan ɗakin ya turniƙe da hayaƙin gaske ko tafin hannu ba a gani tsabar duhu.

 

Ya jima yana mata abubuwa sannan sai ga wani haske ya bayyana ya shige jikinta, sai gata wuf ta tashi zaune tana kallon mahaifin nata.

 

"Ya kai Abbana bani labarin abubuwan da suka faru . Shin ya Nasir ya kasance da masoyiyarshi ?

 

Dariya mai amsa kuwa ya kwashe da ita, sannan ya turniƙe fuska yace,

"Ki kwantar da hankalinki domin komi ya wakana yadda kike so, yanzu haka Nasir da Bilkisu suna tare cikin iyayensu."

 

Duban mamaki take ma shi ta ce, "Shin me ya samu Nasir da Bilkisu ne ? Ni da muka je amso Inna Huraira me ya sako Nasir da Bilkisu ciki?

 

A hankali ya bata labarin duk abubuwan da suka faru, bayan komawarta gunki .

 

Sosai abin yayi mata daɗi, don haka ta miƙe ta shige wani ɗaki dake kallon ɗakin da suke ciki.

 

Ko da shigarta ta kira hadimanta data tura gidansu Bilkisun don su zauna matsayin Bilkisu da Huraira.

 

Cikin ƙanƙanin lokaci suka bayyana suka labarta mata yaƙin da sukai da hadiman Abduljalal bin Uwais.

 

Cikin sauri ta ce maza ku koma ki bibiyomin labarin abin da ke faruwa yanzu, domin raina na bani akwai abin da ke faruwa ga Nasir."

 

Cikin lokaci suka ɓace suna mai rusunawa gareta.

 

 

 

 

 

         Abduljalal

 

Tunda suka tafi da Bilkisu yake kuka kwance kan cinyar Suwaibatul Zabbar ya fita daga hayyacinshi duk tausayinshi ya kamata, kuka yake kuka take har ta fara jin cewar ya kamata ta ɗauko Bilkisun ko don kwanciyar hankalinshi .

 

Cikin kuka ta dube shi ta ce, "Jalal ko dai na je na dawo maka da farin cikinka Bilkisu ?

Ka sani ni ba zan lamunci zamanka cikin wannan mugun hali ba.

Ka sani kai ne farin cikina, ba zan iya barinka a wannan yanayi ba sam.

Nasan cewa kai kuma ita ce farin cikinka don haka zan dawo maka da ita don rayuwarka ta tabbata cikin farin ciki."

 

Cikin kukan ya dubeta, "Tabbas ina sonta sai dai ba zan iya maido da Bilkisu a wannan duniyar tamu ba.

 

Nayi alƙawarin sata farin ciki da walwala har ƙarshen rayuwarta.'

 

"Jalal kana nufin cewa ka zaɓi farin cikinta akan naka farin cikin ?

 

Cikin ƙwarin gwiwa, yace, "A kanta bazan juri ko da sakan guda ba na ɓacin ranta ba.

 Don haka sallama soyayyata ga Nasir domin yaron yana sonta kuma nasan zai iya riƙe ta yadda ya kamata. Saboda da haka zan sauya masarauta daga kusa da nahiyarsu Bilkisu zuwa can gabashin duniya yadda sai lokaci zuwa lokaci zan dinga zuwa gano wani hali take ciki.

 

Sannan zan bata hadimai masu kula da rayuwarta da duk abin da ta haifa har ƙarshen zuru'arsu.

Haƙiƙa Bilkisu ta mamaye ni domin ban san sadda soyayyarta ta shige cikin zuciyata ba, kawai na tashi ne da ƙaunarta rana guda a cikin raina.

 

Ki sani Bilkisu ta saye min zuciya da son addininta, da kula da ibadarta, ki sani na je mata da suffa kala daban-daban amma sai ta kare kanta da addu'a ga karatun Alkur'ani tana yi da murya mai daɗin cike da hazaƙa.

 

Duk irin wahala da tsoratarwar da nake mata da wadda nake saka hadimai na nayi mata, hakan bai sa rana guda taji a ranta zata yi shirka ba ko kuma ta je gun wani malami ba, sai dai ta kai kukanta ga Allah kawai.

 

Akwai halayenta kyawawa da suka ƙara sawa na kamu da ƙaunarta fiye da tunanina, amma insha Allah na haƙura da ita zan saka ma raina ban taɓa soyayya da ita ba har abada sai dai dole zan zama bawan zuri'arta ni duk hadimai na."

 

Sosai Suwaibatul Zabbar taji daɗin maganar Jalal ɗin duk da ya bata tausayi amma tasan gaskiya ce .

 

Cikin lokacin ya tara kaf aljanun dake ƙasanshi ya basu umarnin su dinga bibiyar rayuwar Bilkisu amma kada wanda ya sake ko da wasa tasan yana tare da ita , kawai su zama masu gadinta da ahalinta har ƙarshen rayuwarsu."

 

Haka kuwa suka amsa suna masu jin tausayin Sarkin nasu domin sun san ba ƙaramin so yake ma Bilkisun ba.

Inna Huraira ta dubi Bilkisu rai ɓace ta ci gaba da cewa, "Tunda kin koma mai zuciyar dabbobi ba sai ki cigaba da soyayya da aljani ba.

Ke yanzu ko kunya baki ji ba, yadda kika dubi yaron nan kika ce baki son shi ba ? Amma dai kam cin cika marar adalci kin ji."

 

Shi kam Nasir tunda ya faɗi numfashinsa ke barazanar ɗaukewa, Malam Ahmad ne ya dafa shi cikin damuwa yace, "Kai haƙuri Nasir har zuwa yanzu bata ida dawowa hayyacinta ba, amma kowa yasan Bilkisu na ƙaunarka sosai."

 

Kallon Malam Ahmad ɗin yake yana jin ƙwarin gwiwa na ratsa zuciya da jikinsa. Tabbas ko da Bilkisu zata ce a maida soyayyarsu baya kamar basu taɓa ganin juna ba ya aminta zai sake neman soyayyarta daga farko.

 

Shema'u Yahaiya kuwa sai ta samu kanta da matuƙar ruɗani, akan me Bilkisu zata guji Nasir ta so aljani ? Lallai ta yadda da maganar Babansu Bilkisun bata dawo hayyacinta ba gaskiya, me zatai da aljani ? Allah yayi masu tsari da aljani to.

 

Sai Bilkisu ta shige ɗakinsu ta rufe ta cigaba da rera kukanta tana kiran sunan Abduljalal bin Uwais cikin kewar ganinshi da ƙaunarsa.

 

Kuka take sosai tana ƙarawa, abin da yasa mutanen gidan suka damu kenan banda Huraira da ta ce, "Gara ta mutu da dai ta koma ga aljani."

 

Haka Bilkisu ta yini cikin ɗakin ba ci ba sha, ga mutane nata zuwa barka da dawowarta amma ba su ganinta tana cikin ɗakin ta rufe .

 

Babu yadda Shema'u Yahaiya batai ba Bilkisu ta buɗe ɗakin ba amma ta ƙi buɗewa. Dole ta haƙura ta tafi gida ta bar Nasir da yace babu inda za shi sai ta buɗe ɗakin.

 

A can gidansu Nasir  ɗin ana ta zuwa yiwa iyayensa barka, da arziƙi Nasir ya dawo, amma ba Nasir yana gidansu Bilkisu, da yake babu nisa sai dai daga can su shiga gidansu Bilkisun su ganshi.

 

 

A cikin ɗaki kuwa Bilkisu da gaske take kuka take tana ƙara wa, ita dai Abduljalal ɗinta take so ta yafe haihuwar su cigaba da zama hakan ta aminta.

 

Duk abin da take Abduljalal bin Uwais ɗin na kallonta shi da Suwaibatul Zabbar, yadda take kuka haka yake kukan, ya tabbatar da Bilkisu na ƙaunarsa, amma ya zatayi ? Shi ma yana sonta ya haƙura ne don ta samu cikar burinta, bayan haka babu abin da zai raba su ai.

 

Ganin ta yini ɗaki babu ci babu sha yasa ya buɗe ɗakin.

Ko da ta ga ɗakin ya buɗe ta fara kiran sunansa.

 

"Tabbas nasan kana tare da ni, domin zuciyata ta samu natsuwa sai dai ban san abin da yasa ka ƙi bayyana gareni ba masoyina.

Na rantse da Allah ba da wasa nake ba nayi alƙawarin ba zan sake yi maka maganar haihuwa ba kai min uzurin wadda nayi maka a baya don Allah mu koma rayuwarmu mai daɗi."

 

Sai yanzu yayi mata magana.

 

"Haƙiƙa ina sonki haka ina ƙaunarki, amma hakan ba zai sa in tauye maki rayuwaba.

Ki sani nayi alƙawarin kulawa da farin cikinki tare da duk wani jin daɗinki amma aka wayi gari ko da yaushe sai kin zubar da hawaye a gabana, tabbas ina shakkun anya na cika alƙawarin nan kuwa ma?

 

A yanzu na zo gareki ne don in yi maki bankwana, domin daga yau ba za ki sake jin murya ta ba, sannan inyi maki nasiha akan ki bi mijinki ki yi ma shi biyayya ki zauna da shi lafiya, sannan ki zama abar alfahari a gare shi, don Allah ki manta kin san Abduljalal bin Uwais a rayuwarki, kamar yadda ni ma zan manta ki a rayuwar tawa baki ɗaya.

 

Ki sani aurenki da Nasir shi ne kawai zai baki damar samun abin da kike muradi wato yara, don haka ina mai baki shawarar ki amince da Nasir domin nasan yaron yana sonki haka zai maki komi don ki ji daɗi.

 

Sai wata rana Bilkisu na barki har abada."

 

Nan take ta fasa ƙara tana ihun kiran sunan shi amma ina ba ko alamar ƙamshin turarensa a ɗakin.

 

Huraira ce ta shigo ɗakin a fusace da abin duka sai ga Nasir da gudu ya riƙe abin dukan yana bata haƙuri.

 

Malam Ahmad shima abin na Bilkisu ya fara ba shi haushi don haka ya fice kai tsaye ya nufi gidansu Nasir ya shaidawa iyayensa yasa ranar bikin Nasir da Bilkisu nan da sati guda.

 

Sun yi murna da farin ciki, domin sun san abin da yaron su ke buƙata kenan.

 

Ko da ya dawo gida ya gayawa Huraira da Nasir ɗin ba ƙaramin jin daɗin maganar su kai ba.

 

Bilkisu kuwa kallonsu take tana tunanin yadda za ai mata auren dole da wanda bata so.

 

 

 

        Bayan sati guda aka fara shirin auren Bilkisu da Nasir wanda har lokacin Bilkisu bata sauraren Nasir ko magana bata iya yi ma shi iyakarta da shi idanuwa ne.

 

Hatta Shema'u Yahaiya da take yi mata maganar auren Nasir itama ta daina kulata.

 

 Ranar Juma'a kuwa aka ɗaura auren Bilkisu Ahmad da Nasir Abubakar akan sadaki Naira dubu hamsin cif.

 

Tabbas mutane sun yi mamakin yadda ɗaurin auren ya samu halartar mutane masu ɗinbin yawa na gasken-gaske.

 

Ga abinci kala da kala yanata wali wanda ba a san daga ina yake ba ma.

 

Mutane banza ta faɗi a sai kowa ya dage wasu hada guduri a leda.

 

Duk abin da ake Bilkisu na zaune ɗakinsu ko wanka batai ba, babu yadda ba ai da ita ba amma ta yi banza da mutane ba wanda take saurara.

 

Hakan yasa Huraira ta ce a kira mata Nasir ɗin.

 

Bayan ya zo ne take tambayar shi ina za a kai ma shi matar shi ?

 

Yace mata da ita zai tafi gun aikinsa ba anan zai barta ba.

 

Taji daɗin hakan don tasan idan taje inda babu idon sani dole zata natsu ta zauna lafiya da mijinta.

Don haka ta kira malam ta gaya ma shi ya kamata gobe Nasir ya wuce da matar shi tunda an ɗaura aure.

 

Haka kuwa akai washe gari dangi sun zo rakiyar amarya malam da Huraira suka hana suka ce daga amarya sai ango za su tafi idan tayi hankali a je a gano inda take.

 

Bilkisu na kuka na hargowa aka sata motar Nasir ya ɗauki hanyar Abuja kasancewar can aka maida shi aiki.

 

 

Sai misalin ƙarfe biyar na yamma suka isa Abuja duk tsawon tafiyar da sukai Bilkisu banda harara babu abin da take aikawa Nasir da shi, har ta gaji tayi barci .

 

Ko da ya isa gidan da aka ba shi barci take don haka ya ɗauke ta ya kaita ɗaki ya kwantar ya fara neman abincin da zai bata idan ta tashi.

 

Yana cikin aikin ne ya ji sallama amma bai ga kowa ba.

 

Sai yayi tunanin ko abokinsa ne Yuzarsef amma kuma ba irin muryar bace.

 

"Nasan baka san waye ni ba ko ? To ni ne Abduljalal bin Uwais, na zo gareka ne don baka amanar Bilkisu tare da yi maka gargaɗi akanta.

 

Nasir na yadda ka auri Bilkisu ne don nasan kana sonta to amma hakan ba zai hana in yi maka gargaɗi sosai akanta ba.

 

Ka sani ko da yaushe ina tare da ku don ganin yanayin zamanku na rantse da Allah idan ka ce zaka cutar da Bilkisu sai na azabtar da kai yadda ba zaka iya dawowa hayyacinka ba.

 

Ka yi haƙuri da duk abin da zata nuna maka a yanzu amma can gaba nasan zata amince da kai domin kai ne masoyinta na farko haka nasha fama da ita kai a kwai lokutan da nake amfani da siffar ka don kawai tayi farin ciki.

 

Don haka kai haƙuri ka zama miji na gari gareta domin itama mace ce ta gari.

 

Daga yau ba zan sake maka magana ko nuni ba sai dai idan kayi ba daidai ba hukunci ya hau kanka."

 

Sai ya ji ɗif ya ji komi ya ɗauke ya daina jin motsi komai.

 

 

Hankalinshi ya tashi sosai akan maganar da Abduljalal bin Uwais ɗin yayi.

 

Amma insha Allah zai kiyaye haka zai zauna da Bilkisu lafiya har ƙarshen rayuwarsu.

 

Cikin tunani ya gama komi ya aje ya watsa ruwa ya leƙa daƙin yaga gimbiyar tashi ko ta farka.

Tana zaune tana ta cika tana batsewa kamar wata saraki.

 

Cikin sanyin jiki ya isa gareta ya sunkuya yana leƙa fuskarta yace, "Gimbiya abinci na jiranki."

 

Kamar bata ji shi ba, sai da ya sake gaya mata sannan ta ja tsaki ta juya ma shi baya.

 

Kayan abincin ya kawo gabanta, ya zuba mata komi ya koma ya fito da brush ya bata yace, "Gimbiya a wanke baki a ci abinci don Allah."

 

Kawai abincin ta jawo ta fara ci ko kallon inda yake ba tai ba.

 

Da dare ya shigo ɗakin ta ce bata yadda su kwanta ɗaki guda da shi ba ita sam.

 

Dole ya koma falo ya kwanta yana mai fatan ranar da Bilkisu zata tuna baya su zauna lafiya.

 

Wasa-wasa haka suka share wata uku Bilkisu na tsula ma shi tsiya yadda ta ga dama shi dai komi tayi da ido yake binta.

 

Tunda suka zo shike komi, shike mata komi hatta wankin kayanta shi ke yi ya bada na shi a wanke.

 

Bata ma shi magana sai masifa ko da yaushe ta ƙware matuƙa wajen tujara da masifa (Ashe tayi gadon Inna Huraira)

 

Suna cikin haka aka tura shi yaƙi hankalinshi ya tashi sosai domin yana matuƙar ƙaunar rayuwa da Bilkisu, bai son abin da zai raba shi da ita ko alama.

 

Damuwa iyakar damuwa ya shigeta duk ya bi ya rame ya fita hayyacinshi .

 

Yana kwance falo yana kukan rabuwa da Bilkisu ya ga magenshi kusa da shi kwance tana kallon shi.

 

Zumbur ya miƙe, domin ya tuna labarin da aka ba shi na cewar Aljana ce ba mage ba.

 

Cikin mamaki ya dubeta yace, "Yau kuma me yake tafe da ke gareni."

 

Cikin mintuna ta koma siffar mace ta dube shi da murmushi ta ce, "Sunana Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash ni ce baiwar dake kulawa da kai da duk wani wanda ya shafeka.

 

A yau na zo ne in gayama maka cewar ka kwantar da hankalinka ka tafi aikinka insha Allah akan tafiyar ne zaka samu kan matarka Bilkisu.

 

Sai dai dole zaka wahala amma akwai nasara a gaba.

 

Ni zan kula da Bilkisu hatta dawo hayyacinta ta nemeka ruwa jallo."

 

Sosai yayi mata godiya sannan ta ɓace, ya tashi yayi ma Bilkisu doguwar wasiƙa ya shirya ya bar gidan yaje inda ake shirin tafiyar.

 

Washe gari Bilkisu ta tashi bata ji motsin Nasir ba haka bata ga abinci ba sai ta taɓe bakinta ta nufi kicin ɗin tana zumbura bakinta.

 

Tunda ta zo gidan sai yau ta shiga kicin ɗin, tsab yake ba komi na ƙazanta ta dafa indomie ta dawo ta zauna falon tana cin abinta hankali kwance.

 

Sai data gama komi ta wuce ta watsa ruwa ta ɗauki kayan da ya aje mata ta saka ta dawo falon anan ta hango farar takarda aje da biro sama.

 

Kamar ta share sai kuma ta ɗauka ta warware ta fara karantawa.

 

"Gimbiyata nasan lokacin da za ki ga wannan wasiƙar ni mun jima da nausawa cikin daji.

 

Bilkisu haƙiƙa ina sonki ina ƙaunarki kuma ba zan iya rayuwa babu ke ba, don haka komi za ki min zan dawwama dake a rayuwata.

 

Na tafi yaƙi wanda babu tabbacin dawowata a raye don Allah idan na mutu a can kinga gawata ko ita ce ki furtawa kalmar kin amshi aurena don Allah Bilkisu idan kin wani auren ki sakama yaron sunana, duk da nasan yanzu ba ki sona amma ni ina sonki so na gaskiya bana yaudara ba.

Duk tsawon zamana dake baki taɓa ɓata min rai ba, komi ki kai birgeni kike, sai kuma inga ya dace da ke ne.

 

Bilkisu don idan ban dawo ba ki dinga sakani a cikin addu'ar ki don Allah domin ina jin tamkar ba zan dawo ba na tafi kenan har abada.

 

Daga ƙarshe na aje maki yarana masu maki aikin gida za su zo da safe komi akwai ki duba idan kuɗi kike buƙata ki duba ɗakinki akwai waɗanda za su isheki nasan.

 

Daga mijinki masoyinki na har abada Nasir."

 

 

Taɓe bakinta tayi ta aje wasiƙar ta ci gaba da kallo abinta hankali kwance.

 

 

Duk abin da take Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash tana kallonta.

 

Karfe goma na safe ta ji ana sallama ko bata tambaya ba tasan masu aikin ne don haka ta amsa ta fito daga ɗakin don ganin har su nawa ne ya aje mata ?

 

Suna ganinta suka zube suka gaidata ga alama duk Kirista ne don ta ga yanayin shigarsu don haka ta ce banda dafa mata abinci ita zata dinga dafama kanta.

 

Su kai godiya suka fice.

 

Abin da bata sani ba hadiman Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash ne ba mutane ba.

 

Wannan duk cikin tsarin da Nasir yayi ne da Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash ɗin.

 

Hadiman Abduljalal bin Uwais suka gaya ma shi Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash ta tura hadimanta gidan Bilkisu, ya shaida masu su kula idan sunga da cutarwa gareta su yaƙe su kawai.

 

Tunda Nasir ya tafi kullum sai ya kira wayar gidan amma bata ɗagawa saboda tasan shi ne ke kiranta .

 

Rayuwa take ita kaɗai ba wata damuwa don Nasir bai nan ita ko da yaushe tunanin ta Abduljalal ɗin zai iya iya bayyana gareta ya ɗauke ta su koma rayuwarsu.

 

Amma shiru babu shi babu labarinshi haka nan take zaune ba amo ba labari.

 

 

Yau tana zaune ta kunna labarai ta ga yaƙin da su Nasir suka tafi, sosai ta ji faɗuwar gaba yadda taga ana yaƙi ba ji ba gani, duk an kashe sojojin Nigeriya sosai.

 

Zumbur ! Ta isa inda ta yada takardar da ya bar mata ta ɗauka ta sake karantawa.

 

Hawaye suka fara bin idanunta cike da tausayin Nasir ɗin take girgiza kanta.

 

"Ni fa aurenka ne kawai ban so amma ina sonka a raye Nasir insha Allah zaka dawo.

 

Tabbas ka faɗi gaskiya kana sona amma ni na rasa inda naka son ya maƙale a cikin zuciyata ko jikina Nasir."

 

Ranar haka ta yini kukan da bata san ko na miye ba.

 

Ga shi ta kasa daina kallon labaran wanda su kuma lokaci kaɗan za su hasko yaƙin.

 

Hankalinta ya tashi sosai da sosai, sai ga Bilkisu da sallar nafila kan Allah ya ba su Nasir nasarar yaƙin.

 

 

Cikin kwanakin tayi sukuku da ita sosai ta zama abar tausayi .

Hakan yasa masu aikin suka fara tunanin ta fara son Nasir ɗin sosai da sosai sai suka yanke shawarar su gwadata su gani.

 

Tana cikin ɗakinta ta jiyo ihunsu da gudu ta fito don ganin abin da ke faruwa, sai kuka suke ina ihu irin yadda arna ke yi idan bala'i ya same su , da ƙyar ta samu ta tambayesu abin da ke faruwa.

 

"Madam yanzu aka ce a labarai Oga ya mutu gun yaƙin nan!

 

Zubewa tayi agun ba numfashi, cikin sauri suka watsa mata ruwa ta farfaɗo tana kiran suna shi.

 

Da gudu ta shige ɗakinta tana kuka.

Turus tayi don ganin   Abduljalal bin Uwais da wata kyakkyawar mata rungume da jarirai har uku sunata dariya cikin nishaɗi.

 

"Bilkisu zuwa mu kai mu gwada maki yaranmu da muka haifa ni da masoyiyata Suwaibatul Zabbar." Cewar Abduljalal ɗin.

 

Wani baƙin takaici da baƙin ciki suka rufeta , kenan ita kawai ke haukanta Abduljalal aure yayi ya manta da ita ? Kenan daman shi ya fice da gaske daga rayuwarta kamar yadda ya ambata mata ?

Tabbas tayi asara tunda ta gaza amsar masoyinta na gaskiya akan shi , yau ga shi bai da rai balle ta samu damar gyara kura-kuranta.

 

Cikin kuka ta dinga yaɓa ma shi magana tana cewa su ɓace su bata waje har abada ta tsane shi.

 

Su ka kuwa ɓace ɗin ba musu tana jin tashin dariyarsu.

 

Kukanta ya dawo sabo, ta dinga tunano abubuwa da dama da Nasir Ke mata don farin cikinta amma ina ta aje babinshi gefe ta Abduljalal kawai take ita.

 

Yau ga abin da yayi mata, tabbas maza ba su da tabbas ta aminta da hakan.

 

Sallah kawai take tana azumi kan Allah ya yafe mata zunubin da ta ɗauka na mijinta da iyayenta, tasan fushi suke da ita shi ya sa basu neme ta ba ma sam.

 

Tayi nadama iyakar nadama.

 

Tana zaune tana jan carbi ta ji yaran gidan na ihun murna.

Cikin mamaki ta fito don ganin me yasa su murna ?

 

Turus tayi don ganin an hasko Nasir a TV kwance duk raunuka a jikinshi ana cewa za a maida shi gida ayi jinyarsa.

 

Hannu ya ɗago da ƙyar alamar yana magana.

Kunne taga mutumin ya miƙa ma shi don jin abin da yake cewa.

 

Mutumin ya ɗago yace, 'Oga yace a kai shi gun matarshi yayi jinyar."

 

Ajiyar zuciya ta sauke tabbas taji daɗi ta kuma yadda cewar da gaske yana sonta.

 

Nan da nan ta fara shirin dawowar Nasir tana jin cewar insha Allah ba zai mutu ya barta ba sai suma sun haifi yara fiye da goma ma.

 

A ranar aka kawo Nasir kamar matacce ya ji raunuka sosai a jikinshi.

 

Likitan da yake kula da shi ya gaya mata  abubuwan da zata kiyaye don samun sauƙin jikin nashi da sauri.

 

Haka Bilkisu ta koma kulawa da Nasir  yadda ya kamata bata barci tana tare da shi ko da yaushe, sallah kawai ke tada ta daga gunshi sai kuwa dafa abinci shima don ya zama dole ne .

 

Cikin ikon Allah ya fara samun sauƙi har ya fara magana .

Sai dai ko da yaushe roƙonta yake idan ya mutu kada ta manta da shi.

 

Ita kam kuka take tana roƙonshi yafiya duk sanda yayi mata maganar mutuwa.

 

Sannu a hankali Nasir ya warke sumul kamar bai ciwo ba.

 

Wata mayyar soyayya suke mai cike da kulawa da inganci.

 

Bilkisu ta murmure ta goge tana matuƙar kulawa da Nasir.

 

Ko aiki ya fita suna manne a waya, ita dai ya kula mata da kanshi take fata.

 

Tana kwance ta ji amai kawai ya kamata kafin ta isa toilet har tayi shi a kan hanya.

 

Sai kuma taji jikinta duk ba daɗi don haka ta kwanta ta ɗan huta.

 

Tun daga ranar Bilkisu ta zama kamar kasa nan da nan barci zai kwasheta, kuma kullum sai tayi amai sau ɗaya a rana.

 

Nasir abin ya dame shi yadda Ibnah ta koma komi barci ga yanzu ya lura wani irin cin abinci take na ban mamaki.

 

Ya matsa mata su je asibiti ta ce ita ba sai sun je ba lafiyarta lau.

 

Saboda farin cikinta ya ƙyaleta ya ɗauki hutu yana kulawa da ita kawai.

 

Sanda ya fahimci kullum sai tayi amai  ba ƙaramin tashin hankali ya nuna ba.

Domin ɓoyewa take duk sanda zatai aman .

 

A ranar ya matsa dole ta shirya suka je asibitin su na sojoji.

 

Gwajin farko aka tabbatar da ciki gareta na watanni uku.

 

Murna sosai Nasir yake yayi ta kyautar kuɗi yana ƙarawa don farin ciki.

 

Abubuwan da suka kamata aka aka rubuta masu suka tafi gida suna farin ciki da murna.

 

Suna zuwa gida Nasir ya kira iyayen ya gaya masu Bilkisu na da ciki.

 

Sai murna suma suka tabbatar ma shi da idan cikin ya isa haihuwa ya maido ta gida ta haihu.

Shi kam da to kawai ya amsa ma su amma yasan hakan ba zai yiyu ba .

 

Cikin kwanciyar hankali sukai ta rainon cikinsu da kulawa.

 

Tana zaune da uban cikinta ya shigo ya bata wayarshi .

 

Muryar Shema'u Yahaiya taji ai da sauri ta gyara zama tana jin kamar tai tsuntsuwa.

 

"Madam Nasir kira nayi in gaya maki bikina saura wata huɗu ni da Malam Aminu."

 

Sosai Bilkisu ke fara'a domin haɗin yayi sosai sun dace .

 

Nasir ya amshe wayar yace "ai kuwa ba zata samu damar zuwa ba domin lokacin cikinta ya shiga wata tara."

 

Ihu Shema'u ta saka tana murna za su yi ɗa ko ɗiya suma ta mance da maganar zuwan Bilkisun ma.

 

Ita kuwa nan da nan sai kuka, tana jin Shema'u na tsokanarta ta kashe wayar tana zumɓura baki.

 

 

 

  Bayan wata huɗu kullum iyayen Nasir kiranshi suke ya maida Bilkisu gida ta haihu.

 

Ranshi ya ɓaci sosai ƙarshe ya nemi transfer ya koma Katsina da aikinshi ya tarkata suka koma baki ɗaya, kai tsaye gidanshi ya sauka yace ta zauna nan ai nan dai kusa da gida ne.

 

Babansu Bilkisun yace a bar ma shi matarshi dole suka haƙura aka barta gidanta.

 

Ansha bikin Shema'u Yahaiya da Malam Aminu sai dai Bilkisu bata samu damar zuwa ba kasancewar cikinta ya tsufa ga shi yayi girma sosai kamar ba cikin farko ba.

 

Ranar juma'a da dare suna zaune ta fara cije leɓe tana yamutsa fuska, ya dubeta yace "Ibnah lafiya kuwa ? Sai da ta sake cije leɓe ta ce, "Bayana ke ciwo amma ba sosai ba."

 

Wayarshi ya janyo ya kira wata likita dake dubata, nan da nan kuwa sai gata ɗauke da kayan aikinta.

 

Ɗaki ta shigar da Bilkisun ta dubata, anan taga haihuwa ce don haka ta ce su isa asibitinsu kawai.

 

Cikin hanzari suka isa, sannan ya kira gidansu da gidansu Bilkisun ya gaya masu suna asibiti Bilkisu zata haihu.

 

Nan da nan sai ga Mamarsu Nasir wai Huraira ta ce bata iya zuwa.

 

Suna nan zaune aka ce su miƙa kayan haihuwa, suka miƙa ba a jima ba aka ce su miƙa wasu kayan yara biyu ta haifa duk maza.

 

Bakin asibitin ya fita yayi siyayya ya koma ya miƙa murna kamar me .

 

Sai ga yara an miƙo masu kyawawa sai barci suke cikin ƙoshin lafiya.

 

Aka wuce da Bilkisun ɗakin hutu.

 

Nan da nan ya dinga kiran wayar Abokai da ƴan'uwa yana gaya masu Bilkisu ta haihu yara biyu maza.

 

Bayan awa huɗu aka sallame su kasancewar lafiyarta lau ita da jariranta , kai tsaye Mamarsu ta ce ya wuce gidanta da Bilkisun, a hargitse ya kalleta alamar bai gane ba.

 

Ta sake maimaita ma shi kuwa, ya nemi musawa ta daka ma shi tsawa dole ya nufi gidansu ranshi na ƙuna.

 

Ɗaki guda aka ware mata, sai shima ya kwaso kayanshi ya dawo gidan da zama.

 

Ranar suna yara suka ci Abduljalal da Yuzarsef .

 

Mutane sukai ta mamakin sunan.

 

Bilkisu taita masifa akan me zai sama yaranta sunan Aljanu .

 

 

Ƙarshe dai ta haƙura.

 

Taro yayi taro, kamar yadda bikinsu yayi mutane haka sunan yayi mutane sosai .

 

Ƙarshe dai aka fara surutun hada Aljanu a cikin taron.

 

Kaya kuwa kamar wani makeken kanti haka aka tara su .

 

Raguna manyan gaske aka yanke guda shida, bayan kaji da sauran kalan  naman dabbobin dake shawagi .

 

 

Washe gari bayan an gama komi gida ya gyaru Nasir yace a ba shi matarshi da yaransu su koma gida .

Faɗa sosai Mamarsu tayi ta ce ya koma shi su kam suna nan sai ta gama wanka sannan.

 

Dole ya haƙura ya bar maganar komawa gidan.

 

Sosai suke samun kulawa gina mahaifiyar Nasir yadda ya kamata.

 

Duk abin nan Inna Huraira bata zo taga jikokin nata ba.

 

Babansu Bilkisun kawai ke zuwa ya kuma ce kada akai yaran idan ta gama kunyar ta zo ta gansu.

 

Amma duk bayan kwana biyu tana aiki da abubuwa .

 

 

Cikin ikon Allah haka suka gama wanka su ka je yawon dangi sannan suka fara haramar komawa gidansu.

 

Ranar da Bilkisu ta je gidansu Inna Huraira baki ya ƙi rufuwa don murna da farin ciki.

 

Kwanansu biyar gidan daga nan suka koma gidansu.

 

Sabuwar rayuwa suka shimfiɗa mai cike da farin ciki, ba su da wata damuwa suna ta rainon yaransu.

 

Lokuta da dama Bilkisu najin Nasir na magana da Abduljalal ko Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash amma bata taɓa jin zata iya zuwa ayi maganar da ita ba.

 

Da gaske ta mance Abduljalal ta rungumi mijinta da yaranta suna zaune lafiya.

 

 

Ƙarshe