WATA UNGUWA: Fita Ta Farko
Tamke fuska ta yi tare da ɗora hannu kan mabuɗin ƙofar motar za ta fita. Cikin zafin nama Alhaji Saminu ya riƙo hannunta yana Faɗar "Haba habah! Hanee Baby ki yi haƙuri na daina kawo jakarki na saka miki kuɗin hajarki." Banza ta masa kamar ba ta ji ba ya ɗauki jakar da ke kan cinyarta yana murmushi irin na gogaggun 'yan bariki, ya ciro kuɗi daga gaban motarsa bandir na yan ɗari biyar-biyar rafa ɗaya ya saka mata a jaka, ya miƙa mata jakar.
WATA UNGUWA
*(Labari game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan mamaki da al'ajabi)*
Alƙalamin: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)
Marubuciyar: SOYAYYAR MEERAH.
*YAR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA(GAJEREN LABARI)*
*HALITTAR ALLAH CE*
AND NOW
*WATA UNGUWA*
GODIYA: Dukkan godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki buwayi gagara misali Sarkin da ya aramun rayuwa da lafiya ya kuma bani basira da damar rubuta wannan littafi domin ya zama faɗakarwa da jan hankali a rayuwa al'umma baki ɗaya.
Tsira da aminci su ƙara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam
Tare da iyalan gidansa da sahabbansa baki ɗaya.
*Gargadi:* Ban yarda wata ko wani ya canza mun labari ta kowacce siga ba ba tare da izinina ba.
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Free page
P 1
BABI NA ƊAYA
GARIN MAMBIYA
UNGUWAR GARWA
Da misalin ƙarfe shida na safiyar ranar Lahadi unguwar ta yi tsit ba ka jin motsin komai sai na iskar da ke kaɗawa, titin ya yi tsit kamar ba wani mahaluƙi da yake rayuwa kusa da wurin.
Bayan shuɗewar mintuna biyu sai ga wata dalleliyar baƙar mota ta hawo titin da alama matuƙin motar ya na cikin hanzari ne. Can kuma motar ta ci burki dai-dai kan wani ƙaramin layi.
Daga cikin motar wata matashiyar budurwa ce da ba za ta haura shekaru ashirin ba zaune a mazaunin mai zaman banza. Juyawa ta yi ta kalli wani babban mutum da ke zaune a mazaunin direba ta ce "Ya Alhaj ni zan ƙarasa gida ka san halin mutanen unguwar nan, da na sake wani ya ganni shi ke nan na shiga uku."
Yar dariya ya yi sannan ya kuma dubanta ya ce "Haba Hanee baby daɗina da ke masifar tsoro, don kin sha daɗinki a waje miye?"
Tamke fuska ta yi tare da ɗora hannu kan mabuɗin ƙofar motar za ta fita. Cikin zafin nama Alhaji Saminu ya riƙo hannunta yana Faɗar "Haba habah! Hanee Baby ki yi haƙuri na daina kawo jakarki na saka miki kuɗin hajarki."
Banza ta masa kamar ba ta ji ba ya ɗauki jakar da ke kan cinyarta yana murmushi irin na gogaggun 'yan bariki, ya ciro kuɗi daga gaban motarsa bandir na yan ɗari biyar-biyar rafa ɗaya ya saka mata a jaka, ya miƙa mata jakar.
Karɓa ta yi ta fita daga motar ba tare da ta kuma ce masa komai ba.
A zahirin gaskiya gangar jikinta ce kawai take a wurin amma ruhinta yana gun tunanin me zai je ya dawo idan wani ya gan ta. Duk da ba ta fatan kasancewar hakan amma tana tsoron afkuwar ɓacin rana. Da ma masu azanci kan ce rana dubu ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya.
Sanye take da baƙar abaya ta yanke kanta da ƙaramin mayafin abayar wannan ita ce zahirin shigar da ake iya gani a tare da ita, amma a cikin jikinta riga da wando ne ɗamammu wadanda sai ka a je hankalinka sosai za ka lura da hakan.
Tana fitowa ta ji wani irin sanyi na ratsa gaɓoɓin jikinta ta yanda har yake shiga ƙasusuwan jikinta. Hannuwanta ta rungume a ƙirjinta tana kanƙame jiki wuri ɗaya.
Waige-waige ta hau yi daga hagu zuwa dama, ganin ba kowa ya saka cikin hanzari ta shige layinsu tana tafiya gudu-gudu sauri-sauri.
Abin da ba ta sani ba shi ne ashe tun lokacin da Alhajin ya faka motarsa Mamuda s/m yana zaune ketaren titin ya na kallon su.
Tun lokacin da aka fito daga sallar asuba kowa ya koma gidansa ya rufe saboda tsananin sanyin da aka tashi da shi, amma ban da Mamuda wanda a maimakon hakan ma sai ya shimfiɗa ƙyalle ya zaunaa gefen titi duk ya takure jikinsa saboda sanyi, amma ba ya son ya shiga gida don kada wani ya zo ya wuce ko ya yi wani abun bai gani ba tsabar munafunci.
Ya na ganin shigewar Hanifa layin ya miƙe tsaye ya na Faɗar "Kai! Ashe kura ce muke gani da fatar Akuya dama wannan yarinyar 'yar bariki ce? Ba mamaki...
Dariyar jin daɗi ya yi sannan ya koma ya zauna yana faɗar "Na samu rahoto na ɗaya bari na zauna ko a samu na tarawa."
Lokacin da Hanifa ta isa gida ta tarar da ƙofar gidansu a rufe kamar dai yanda ta yi tsammani hakan ya saka ta yi sauri ta kewaya ta hanyar da ta tanadarwa kanta saboda hakan, ranta fal tsoro ta taka dutsen ta haura kan katanga sai ga ta cikin gidan tsulum tamkar ɓarauniya.
Ajiyar zuciya ta sauke da ƙarfi "Hmmm!" sannan ta wuce saɗaf-saɗaf ta nufi hanyar ɗakinsu.
Har ta wuce ɗakin Inna kamar yanda ta yi tsammani suna nan suna baccin asarar da su ka saba, da ma baba sallar asuba ba ta dame shi ba sai ƙarfe takwas na safe ma watarana yake yi balle kuma ya tsawatar masu.
Bai fi saura taku biyar ba ta shiga ɗakinsu kamar daga sama ta jiyo a bayanta "Kambu.... Ashe ba a gida kika kwana ba?" Ta tsinto muryar yayanta Mankas yana faɗa cikin muryar 'yan daba.
Tsuru-tsuru ta yi kamar ɓarawon da aka rutsa tana kallonsa shi kuma ya matso kusa da ita yana faɗar "Daga ina ki ke? Bari baba ya tashi yau akwai kallo a gidan nan kenan."
Sanin halin yayan nata ya saka ta ɗan haɗe fuska tare da zuba idonta cikin nashi ta ce "Matsalata da kai kenan ba ka da sirri, yanzu dai zan ba ka cin hanci sai ka rufa mini asiri."
"Yawwa yarinya da kin wa kanki adalci." Ya faɗa yana rangaji kamar zai kifa da ƙasa.
Jakar hannunta ta buɗe tana ƙoƙarin lalibo masa kuɗi shi kuwa ya zuro kai yana leƙen kuɗin. Ko da ya ƙyalla ido ya ga kuɗi da yawa sai ya sake baki kamar wani gaula, har ya buɗi baki zai yi magana kenan ta dungura masa dubu ɗaya a hannu tana harararsa ta wutsiyar ido "Ga shi sai ka sake mun kurwa ko?."
"In kin isa Allah ya tsinen, in ga kuɗi da yawa ki bani dubu ɗaya rak, ko an gaya maki wannan kuɗin ne zai ishe ni yin chaji? Ga ma yau muna da wani ofireshin da za mu fita tun safe." Ya faɗa yana ƙara matsowa kusa kamar zai warce jakar. Ta ƙara cacume jakar ta da kyau tana cuno ƙaton leɓenta tana faɗar "Haba Mankas, ni ka san wahalar da na sha kafin na samu kuɗin?."
"Ok ajiye kayanki a jaka bari in ta so Baba." Ya faɗa tare da juyawa ya fara ɗaga murya
"Baba!, Baba!!."
Cikin hanzari da rawar baki Hanifa ta riƙo rigarsa ta baya jiki na ɓari ta ce "Don Allah Mankas yi shiru zan ƙara maka wallahi."
"Kin kyautawa kanki." Ya mayar mata yana basarwa.
Cikin ƙunƙuni ta dauko dubu biyu ta ƙara masa, tana 'yan maganganu can ƙasa-kasa yanda ba zai ji ba. "Me kika ce?" Ta tsinkayo tambayar daga bakinsa. Harara ta aika masa a cikin duhun don tana da tabbacin ba zai gani ba sannan ta ce "Ni ban ce komai ba."
Da ba ta da niyyar ƙara masa amma sanin jaraba irin ta Mankas ya saka ta ba shi tun suna sheda juna kafin ya janyo mata kara da kiyashi. Ganin shigewarsa ɗaki ya sa ta yi hanzarin ƙarasawa nasu ɗakin tana faɗar "Jarababbe kawai, ni Ya Abba ya fi mun kai don ba ya yunƙurin tona ni, mu kashe mu binne ba wanda ya sani. Amma kai a karon banza kana son janyo mun tsinannen duka."
Daga haka ta ƙarasa ɗakin nasu da kallo ɗaya za ka masa ka san yana cikin gidan talakawa ne, domin kuwa ginin bulo ne kawai ko filasta babu har wani ɓangare na ginin ya fara ƙwaƙwarewa.
Abayar ta cire tare da riga da wandon da ke jikinta ta kuɗundune su ta tura su can ƙasan bakkon kayanta, sannan ta janyo wani tsumman zanin atamfa da kallo ɗaya za ka masa kasan ya yi kewar ruwa da sabulu, ta yi ɗaurin ƙirji sannan ta haye yagalgalallar katifarsu da ko albarkacin shimfiɗa ba ta samu ba, ta takure daga can gefe gudun kada ta tashi ƙannenta 'yan mata biyu da suke kwance kan katifar. Zama ta yi tana ƙirga kuɗin da ta karɓo gun farkanta, kawai sai ta ji motsin ɗaya daga cikin ƙananun yaran dake kwance a ƙasa kan tabarma.
Da sauri ta mayar da kuɗin jaka ta kwanta luf kamar mai bacci tana ta faman ƙissima abubuwan da za ta yi da kuɗin.
Bayan gari ya yi haske Inna ce ta fito daga ɗaki tana ƙoƙarin gyara ɗaurin ƙirjinta da yake daman suɓalewa, buta ta ɗauka ta nufi banɗaki bayan ta fito ta zauna a tsakar gidan ta yi arwala sannan ta shiga ciki, a lokacin ta yi sallar Asuba. Har zuwa Lokacin Baba Mudi bai tashi daga bacci ba balle a yi zancen Sallah ko fita nema, sai kusan ƙarfe goma na safe ya fito ya yi Sallah. Koda Inna ta tambaye shi kuɗin karin kummalo sai ce mata ya yi "Ni yau ko asi ba ni da, je gun wacce kika saba karɓa gun ta ta ba ki."
Ba ta bi ta kansa ba ta fice sai ɗakinsu Hanifa lokacin duka yaran sun tashi daga bacci ban da Hanifa dake ramakon baccin da bai ishe ta ba daren yau.
Hannu ta saka tana bubbuga kafaɗarta "Hanifa! Hanifa!! tashi ki ba mu wani abu mu karya."
Cikin bacci da jiyo dukan ta farka tana turo leɓe "Oh shit! Habah Inna! Wai miye haka ba kya ganin bacci na ke?" Ta faɗa tana tashi zaune sai daman turbuna fuska take.
"Kuɗin kari za ki ba mu tun da kinsan uban naki ba bayarwa yake ba sai ya ga dama." Innar ta mayar mata tana tsaye ƙere-re a kanta.
Jakarta ta janyo tare da ciro ɗari biyar guda biyu ta miƙawa innar "Ga shi a siyo abin da za a siya a kawo mun canji su kaɗai nake da, su ma kuɗin da na yi wa wasu mata kitso ne jiya suka biya ni."
"To an gode." Innar ta faɗa har ta juya ta fita ta sake hankaɗo yagalgallen labulen ɗakin tana faɗar "Ɗazu Faridar gidan Bargaja ta zo nemanki zancen kitson da kuka yi alƙawarin za ki yi mata yau da safe, na ce ki na bacci. Yanzu sai ki aika yaro ya kira miki ita." Daga haka ta juya ta tafi abin ta don neman abin da za a sarrafa.
Ƙanzon shinkafar da suka ci jiya ta gyara aka siyo kayan haɗi innan ta kwaɗanta musu. Shi aka kakkasawa yaran gidan kowa ya ɗauki na shi cikin halamniya suna hannu baka hannu ƙwarya suka cinye ba don sun ƙoshi ba.
Ba abin da ya fi ɓatawa Hanifa rai irin yanda Baba ya matso kusa yayin da ake rabon kwaɗon ba ko kunya wai a saka mi shi na shi. 'rashin kunya ƙauri da kare.' da faɗa a ranta.
Da yamma bayan Hanifa ta sallami yan kitsonta ta je maƙwafta neman ruwan da za ta yi wanka. Da ƙyar Ladidi ta samma ta ɗai da karamin bokitin ƙarfe.
Ta na shigowa gidan ba ta nufi ko'ina ba sai ƙofar ƙaramin banɗakin dake tsakar gidan, har za ta shiga ta tuna da sabulu da sosonta da ta manto a ɗaki, ajiye bokitin ruwan ta yi ta nufi ɗakinsu.
Can bayan minti biyu sai ga ta ta dawo hannunta riƙe da kwandon soso, sai dai me? Ko da ta ƙaraso ta duba sama da ƙasa, bokitin ya ce neme ni inda kika ajiye haka kuma ƙofar ƙazamin banɗakin nasu a rufe take ruf, saɓanin mintuna biyu baya.
"Waye ne a ciki?" Ta faɗa cikin ɗaga murya, sai dai ba alamar wanda ke cikin zai ba ta amsa.
Tana nan tsaye a gun tana jijjiga ƙafa tare da mamakin waye wannan mai ƙarfin hali a gidan nan da ya raina ta haka?
Maryam ce ta zo wuce wa za ta fita, ta ga yayar tasu tsaye.
"Yaya Hanee me ya faru ne?" Ta tambaya.
"Ke wai ruwan wanka na samo maƙota shi ne daga na shiga ɗaukar sabulu wani wanda ya fi ni jikin wankewa ya ɗauke mini." Ta faɗa tana kada kai cikin alamun jin masifa.
"Tab! Ni dai ba ruwana Allah yaya Sofi ce , na ga lokacin da ta shige."
Maryam na gama faɗa ta kaɗa kanta ta fice daga gidan, yayin da zuciyarta ke azalzala mata ta yi azama ta je ta dawo don ganin bidirin da za a sha a gidan yau, ba don ma tana shakkar Mankas ya zo ya tarar ba ta je aiken shi ba masifa ta faɗa mata da ba abin da zai hana mata kallon wannan series da za a fara kafcensa a yau.
Bayan kamar mintuna biyar sai ga Sofi ta fito daga bandakin tana yarfe ruwan jikinta ranta wasai.
Cikin azama Hanifa ta yi kanta tana huci tamkar zakanyar da ta yi arangama da nama. Ƙwace bokitin ƙarfen da ke hannun Sofi ta yi cikin shammata ta kwaɗa mata shi a gaban goshi, sai ga jini yana fesowa daga kan nata.
Wani razanannen ihu Sofi ta kwarara tare da dafe gaban goshin nata da tafin hannunta ɗaya cikin muryar kuka ta ce "Ni za ki fasawa goshi?"
"An fasa miki ɗin, uban wa ya ce ki ɗauke mun ruwa? Kin san wahalar da na sha kafin na same su, ko kin san inda nake shiri za ni?" Ta faɗa tana huci, da ganin yanayin ta ka san ranta ya mugun ɓaci.
"Tab! Ai ko yau za ki ga haukar da yafi naki don sai dai mu yi kare jini biri jini da ke a gidan nan." Tana gama faɗa ta wuce da sauri ta nufi madafa tana waige-waigen neman wuƙa, yayin da Hanifa ta ɗauko wata jibgegiyar ƙotar gatari ta riƙe tare da gyara tsayuwarta tana jiran Sofi.
Duk wannan bidirin da ake ba kowa a gidan Inna ta ficewar ta zuwa ƙauye kamar yanda ta saba duk ranar Lahadi, sai ƙananun yara kawai suma sun fice gun wasar su Sadik da Basma kawai suka rage a gidan, sai ihu suke suna faɗar "Faɗa na da daɗin kallo, faɗan da ba naka ba zura ido, ku kashe kanku a gidan ba mai raba ku." Sai tsalle-tsallen jindadi yaran suke, da alama sosai faɗan ke yi musu daɗin kallo.
Can Sofi ta rarumo wata sabuwar wuƙa mai kaifin gaske sai walƙiya take ta nufo inda Hanifa take da ita tsirararta tana faɗar "Yau sai na fitar miki da jar kala ajikinki kamar dai yanda kika mun."
Hanifa gyara tsayuwar ta ta yi tare da ɗaga ƙotar gatarin tana faɗar "Allah ya ba ki sa'a jiki bai fi jiki ba, haka kuma ba ki fini iya daba ba..."
Kafin ta gama rufe bakinta Sofi ta dako tsalle cikin zafin nama da sa'a ta kai wa Hanifa suka a gefen ciki.
Dai dai lokacin Maryam ta kunno kai cikin gidan, a tare suka saka ihu da Hanifa. Ita tana ihun firgicin da ta yi tozali da shiHanifa kuwa tana ihun azaba da zogin da take ji.
Kafin Maryam ta yi wani yunƙuri jiri ya ɗebe su duka suka zube a gurin sumammu.
Hmm! Wannan labarin salon shi daban ne kamar yanda yake na dabam....
Kai dai ka biya kuɗinka N200 kacal domin ci gaba da karantawa
A dadin comment naku da kuma soyayyar da zaku nunawa littafin gurin siyenshi shi zai tabbatar mun da yanda kuka karɓe shi.....
Kada ku manta ɗari biyu ne kacal
Domin biyan kuɗin littafin ku Tuntubi wannan number : _08109634202_
Bank name: Rukayya Ibrahim lawal
Account number: 0431343346
Gt bank
Ku biya kuɗinku ta wannan account ɗin.
₦200 ne kacal cikin sauƙi don faranta wa masoya rai.
Washegari ranar ma kamar wacce ta gabata an tashi da tsananin sanyi wanda ya so yafi na jiya
*WATA UNGUWA*
*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*
*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*YAR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*RASHIN GATA (GAJEREN LABARI*
*HALITTAR ALLAH CE*
*AND NOW*
*WATA UNGUWA*
managarciya