MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Hudu

MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Hudu
          MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Hudu
        
                        
 
             
                        *Page*  9 & 10
 
Hajiya Hindu ta daga waya ta kira Alhaji Hisham yana dagawa ta ce ina jiranka 'a falo yace gani nan zuwa Hajiya cikin hanzari ya mike ya nufi falo, cikin hanzari ya iso falon ya zauna bisa carpet din dake shimfide a falon, ya sunkuyar da kansa kasa kafin yace Hajiya barka da zuwa,  Hajiya Hindu tace barka dai kafi ta kara cewa nazo daukan diyata Aisha ce zan kaita gidana tayi wankan gida Alhaji Hisham ya sunkuyar da kai a karo na biyu kafin yace ba wani damuwa Hajiya yanzune zaku tafi din ? Hajiya Hindu tayi murmushi kafin tace yanzu ma kuwa,  Alhaji Hisham yace da driver kukazo ?
 
Hajiya Hindu tace kwarai da gaske murmushi ya kuma yi kafin yace Hajiya takwarar ki ce a hannunki ? Hajiya Hindu tace eh! Kafin ta kara cewa yauwa wai naji kuna kiranta da wani irin suna waishi MEE'AD! Murmushi Alhaji Hisham yayi kafin yace dama nasan zaki tambaya shiyasa na shirya tsaf danna amsa miki tambayar taki suna MEE'AD dai yana nufin ALKAWARI! Wannan dalilin yasa na sanya ma takwarar ki wannan sunan sbd ta dace da hakan kuma bakina bazai taba furta sunanki ba gaskiya,  sbd koba komai ke kikayi silar zuwan mu duniya,  duk irin gatan da muka samu a fadin duniya sanadin kine kinga banida daman kiran sunanki ko Hajiyata ? Murmushi Hajiya Hindu tayi kafin tace naji dukkan abinda ka fada kuma naji dadi sosai Allah yayi muku albarka ya kareku da dukkan sharri, Alhaji Hishan yace Ameen Hajiyar mu.
 
Shekara kwana yau an wayi gari Mee'ad ta shekara 10 yayinda Amal take da 12years,  sun girma sun fara zama yan mata Amal da Mee'ad kansu daya bazaka taba cewa Amal ta girme wa Mee'ad koda 1day ne ba, sun taso cikin gata girmama juna da kuma kaunar juna, idan kai bakone ka shigo gidansu bazaka taba cewa ba mahaifiya 1 ce ta haifesu ba, "
 
Yaya Majeed ya girma sosai ya fara mallakan hankalin kansa dan kuma harya kammala secondary skull dinshi cike da hazaka gwanin son karatu da karance2 littatafai da dama,  Majeed ya tashi zuciyarsa cike da soyayyar kannesa guda biyu Amal da kuma Mee'ad,  sai dai kusan zan iya cewa zuciyar tasa tafi karkata ga Amal sbd sunfi shakuwa da ita fiyeda Mee'ad, domin ita Mee'ad yarinya ce miskila kuma mara son hayaniya, sau tari idan kayi mata magana sai kaga tayi maka murmushi sbd bata fiye surutu ba idan har kanason ganin surutun Mee'ad to kace Amal ta girme mata kaga surutu fiye da tinanin ka"
 
Mee'ad yarinyace mai hankali kamar Mommy da Daddynta, bata fiye shiga cikin abinda bai shafeta ba, yarinyace mai son karatu sosai, idan zaka hadu da Mee'ad sau 10 to zakaga littafi ko qur'ani a hannunta sau 5 ko fin haka ma sbd ma'abociya karance-karance.
 
Yayin da ita kuma Amal halinta dana Mee'ad ya sha bam2 sosai, Amal yarinyace mara son karatu koma wani irine ga bata wani damu da ibada sosai ba,  kusan kullum sai sunyi fada da Mee'ad akanyin sallah musamman sallar Asuba takan kai 10am kafin tayi sallan koma fin haka kusan kullum Mee'ad sai ta mata fada,  Amal ta kware sosai gurin tsalle2 da raye2 abindai sai wanda ya gani ya iya gane mi nake nufi.
 
Mee'ad ce zaune bisa kujera a falo tana danna wayan Mommyn ta kasancewa ta fita ba tare da wayar ba,  ta shagala cikin danna wayar taji fizge wayar,  a tsorace ta dago kai dan taga waye sai taga Yaya Majeed tsaye bisa kanta yana cewa waike mi kk yi hakane ? Inata yin magana bakima jiba, murmushi Mee'ad tayi kafin tace kayi hakuri Yaya wllh banjika bane,   gwale ido Majeed yayi kafin yace au duk maganar da nayi kenan bakima ji mi nace bako ? Ok tashi ki kira Amal ku sameni a garden na muku lesson ko ? To Mee'ad tace kafin ta tashi ta nufi bed din Amal cike da murna Majeed ya bita da kallo yana jijjiga kai yana mamakin son karatun Mee'ad din.
 
Mee'ad ta tarar da Amal sanye da wata blouse da wandon jeans tree quater ta kure volume din mp tana shan rawa abinta, Mee'ad ta dade tsaye tana kallon yar'uwar tata kafin ta karasa ta kashe Mp, a fusace Amal ta juyo tana fadin waye ya kashe mini abina ?" 
 
"Tana juyowa tayi arba da 6ter nata, tadan ja guntun tsaki mtsw! Kafin tace miye kuma kika wani kashemin abina ?
 
" Ta karasa maganar fiskarta bace 
 murmushi Mee'ad tayi kafin tace Allah ya baki hakuri my sis, dama Yayankine yace nazo na kiraki muje yayi mana lesson kinsan munyi kusan fara exams ko ?" 
 
"Amal ta tabe fiska kafin tace kice masa ina bacci kuma nace a daina tashina kinji ? 
 
Mee'ad tace nikam bazanyi karya ba gaskiya , " Amal ta galla mata harara kafin tace ko kije kice bazanzo dinba sbd banason damuwa da takura kina jina ko ? Mee'ad tace shikenan bari na hadaki da Umma,  Amal tace kije ki fada tinda kokin fada baza tayi mini komai ba, hasalima cewa zatayi bata son ana damina! Mee'ad tace ke kika sani ni kinga tafiyata, a harzike ta juya ta nufi kofar fita 'a hanzarce Amal ta janyo Mee'ad tana fadin yi hakuri kinji bloody tah jirani mu tafi Mee'ad tayi murmushi kafin ta tsaya sannan tace kiyi sauri ki shirya ina jiranki, 
 
"Amal tace naji dadi sosai bloody nasan kina kaunata sosai barina shirya da sauri, cikin sauri ta bude wardrop ta dauko doguwar riga ta saka kafin tace muje too  cikin jin dadi Mee'ad tace yauwa koke faah.......
 
 
 
 
Pls fans don't forget to read & share to other groups.
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Love u much my fans
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Pls 
 
Fans
 
Ku
 
Nemeni 
 
Akan
 
Wannan 
 
No din
 
Dan bada shawara ko makamancin haka haka zalika idan kina/kana son shiga MEE'AD FANS GROUP duka ku nemeni ta Nambata.
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Taku har kullum Hauwancyy Misau.