ANA BARIN HALAL..: Fita Ta 16
ANA BARIN HALAL..:
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*PAGE* 16
Ina fitowa nagan su dukkan su a waje, wasu sun shiga motocin su wasu suna tsatstsaye suna magana, hango M.G nayi tsaye a jikin motan su, wanda bansan wannene nashi ba wannene na A.G, wataran nakan gansu a Red, wataran a Black, so bansan nawaye a ciki ba, ƙarasawa nayi wurin shi bakina ɗauke da sallama, ɗago kansa yayi daga danna wayan da yakeyi ya sauƙe mun idon shi a kaina, abun mamaki yau babu wannan fara'an da yake fuskan shi, "meye schedules ɗinki na yau"? ya tambaye ni idon yana kaina, ɗan juya idona nayi sannan nabashi amsa da, "yanzu dai babu komai, sai zuwa anjima muna da liyafa da za'ayi acikin gidan nan," ina faɗa ido na yana kan masu decorating wurin, shima maida idon shi yayi wurin, muryan shi chan ƙasa yace, " barrister yace mun tare aka haife ku da amaryar, itace wannan twin sister ki da muka taɓa ganinku tare ko"? Murmishi nayi ina ɗaga mishi kai alaman hakan ne, ƙura mun ido yayi har sai da naji kunyan shi na sunkuyar da kaina ƙasa ina wasa da gyale na, kaman bazai sake magana ba sai kuma chan yace, "saura ke kenan, fatan dai bazai ɗauki wani lokaci ba zamuji kyakkkyawan labari"? Ɗan juyar da kaina nayi gefe ina murmushi, bance komai ba haka shima bai sake ce komai, amma idon shi yana kaina, chan na hango Yayah Ahmad da A.G suna tahowa wurin mu, a hankali na juyar da kaina ina kallon M.G nace, " yayah yace nazo kana ƙirana", wayan shi ya miƙo mun yace, "saka mun number ki zamuyi magana daga baya"
Hannu na saka na karɓi wayan nasaka mishi number na, ina miƙa mishi su Yayah Ahmad suna ƙarasowa wurin, wani kallo mai kama da harara naga A.G yayi mun sannan ya kawar da kanshi ya shige motan ta side ɗin mai zaman banza, sallama na musu bayan yayah Ahmad yace zuwa dare idan an watse na dafa mishi ruwan tea.
Ana sallan la'asar gidan mu ya cika maƙil da mutane, haka muka fito muka nemi sit muka zauna da su Aunty Bintu da dukkan wanda suke side ɗin ummin mu, dama kuma Aunty Rakiya ta sauƙe mun kyakkyawan warning akan zuwa inda ƙawaye suke, bata hana mu fita wurin ba tace saboda hakki na ƴan'uwan taka, amma tayi hani da shige musu, ko ita hafsy an ɗakatar da ita da zuwa wurin raliya, muna zaune aka fito da amaryah cikin shigan ta maroon, ƙawayenta na familyn su da ƴaƴan ƙawayen maminta ne suka rako ta, bayan ta zauna babu daɗewa dangin maminta suka rako mamin ta ita ma har wurin zamanta, wayaga uwar amaryah ansha leshi ɗan gaske kana ganinta kaga anaryar Alhaji Usman umar (U.U Ɓalewa) dama kafin fitowan ta mamah da ummi sun daɗe a fili kowa tana table ɗaya da ƙawayenta, ɗago da ido na ɗaɗɗaya ne zanyi ban tarar da idon habiba akaina ba, kuma duk haɗa idon da mukayi sai ta sakar mun murmushi, nima kuma sai na mayar mata, a haka naji tsakin hadiza, da wuri na juya sai naga harara ta ke ɓalla mun, sanin me take nufi ya sa ban kula ta ba na juyar da kaina ina kallon masu rawa.
Har sai dab da magrib dangin ango suka iso, abun mamaki basufi mutum biyar ba, bayan table mai ɗaukan mutum goma aka bar musu guda biyu, saiga mutum biyar sun shigo, haka aka rakasu suka zauna aka kawo musu abinci, ana fara ƙiran magrib suka je fili bayan an ƙirasu da amaryah suka mata liƙi marar ma'ana, daga nan sukayi sallama suka kama hanya, ni acikin su ma bansan fuskan kowa ba, banda ƙanwar mummy guda ɗaya, haka dai aka cigaba da chashewa da DJ, mudai ana fara ƙiran sallan magarib duk mukayi side ɗinmu domin sauƙe farali, basu suka tashi a wurin ba sai wurin 9:00pm, shima sai da Abba ya dawo yace a sallame su tukun suka watse, ni lokacin ma ina kitchen ina dafe tea wa yayah Ahmad, da yake girkin ummie nane sai na haɗa hadda na Abba na, flask ɗin Abba na cika sai na yayah Ahmad, sai na cika wani wa don naji Aunty Rakiya ma tace zata sha, ganin akwai time sai na gasa bread wa yayah Ahmad don yana so sosai, hafsy na roƙa ta kai mishi lokacin da naji shigowan motan shi.
Wuraren 10:00pm muka fito tafiya gidan Aunty Bintu, da yake yau babu ummitah da maryam motan zata ɗauke mu ba sai an nemo driver ba, muna isa babu wani ɓata lokaci muka fara shirin kwanciya, da yake kowa ya gajji yau, a parlor muka tarar da yayah mohd yana kallo, muna shiga ya miƙa hannu ya karɓi Areefh da yake bacci a hannun hafsy, dukkan mu gaishe shi mukayi sannan muka wuce, babu wani dogon hira a tsakanin mu dukkan mu mukayi bacci, cikin bacci naji vibration ɗin wayana, a razane na jawo wayan na duba mai ƙiran, sai naga number ne, da sauri na yanke wayan, sannan na kashe ta gaba ɗaya na koma na kwanta.
Ana sallan asuba babu wacce ta koma bacci, gyaran gidan mukayi tsaff aka turare shi da turaren wuta masu ƙamshin gaske, saboda idan mun fita baxa mu shigo ba sai lokacin kawo amaryah, abun breakfast muka haɗa, muna karyawa aka dinga shiga wanka, wuraren 9:00am muka shiga gidan mu, ana ta shirye - shiryen tafiya ɗaurin aure, da yake ƙarfe goma za'a ɗaura a masallacin gwallaga, daga na yayah Ahmad har na Habiba achan za'a ɗaura, parlon Abba dukkan mu muka shiga, achan muka haɗu da mamie da Aunty Rakiya tare da Abban mu suna magana, gaishe su mukayi muka fito.
Wuraren 11:30am gidan mu ya cika da ƴan'uwa da yayun mu, wanda sukaje ɗaurin aure daga dangin Ummie har na Abba duk sun hallaro gaisuwa da taya murna, gefe ɗaya kuma ga ƴan'uwan mamie da suke ta baza guɗa, nidai duk guɗan su yankar mun zuciyata takeyi, wato ya tabbata habiba ta auri Aliyu? Aliyun da ya soni, Aliyun daya gama cewa babu mace da yasani wanda ta kaini kyau, kuma yaji a duniya yana sonta sama dani, Aliyun da aka daɗe ana son aga macen da zaice yana so, wai yau ƴar'uwata da nakeyiwa so da ƙauna itace ta zama mallakin shi, itace zasuyi rayuwar aure ba ni ba? Tou Allah ya sanya alkhairi, Allah ya bani haƙuri da juriya.
Yau ma anko mukayi da hafsy, wata super da yayah Mohd yasaya mana, nawa ash nata yellow, gaba ɗaya munyu kyau babu ƙarya, ina lure da hafsy da ummitah jiki na rawa suke ta haɗa duk wani nau'in abinci da akayi a gidan wa yayah umar da yayah ishaq, yayah umar ne ke shigowa ya karɓa su tafi, nidai mamakin su yayah umar ɗin ma nakeyi, yabawa hafsy fah wurin 10yrs amma jibi yadda yake ta wani rawan jiki da kai wa ummitah, koda yake ni kaina bana gajjiya da kallon ummitah, domin duk gidan su tafi su kyau, ga wani diri da Allah yayi mata, ummitah ba fara bace, sai dai wani colour ta keshi mai hasken gaske, idan ka ganta sai kasake kallonta saboda wasu ido da takeda masu kyaun gaske, ga shagwaɓa kamar babu wata ɗiya a gidan sai ita, kullum kaga ganta cikin shagwaɓa take bansan yayah za'ayi da yayah umar ɗan zafi ba, hala fah sai ya biye mata a hakan, dariya nayi ni kaɗai na.
Ana sallan magrib babu daɗewa wannan number ta sake ƙirana, yanzu banƙi ba na ɗauka, murmushi nayi lokacin danayi karo da muryam M.G yana cemun, "mai kyau ina kika ɓuya ne yau? Gaba ɗaya ban ganki ba"?
Murmushi nayi na fara gaishe shi batare da na amsa mishi tambayan shi ba, amsawa yayi ina jin sautin murmushin shi, "jiya kinyi bacci ae na ƙiraki, naso da safe na ƙira mu gaisa Allah bai nufa ba, yanzu ma ina so na sanar dake idan an tashi tafiya dinner ki jira zanzo na kaiko idan babu damuwa".
Murmushi nayi na bashi amsan da "Allah ya kaimu yayah,"
Sallama mukayi yace sai yazo, yana zolaya na wai nayi ɗaurin da za'a san ƙanwar su 1 in town ne, dariya ne ya suɓuce mun na kashe wayan, ina murmushi a zuciyata nace, "nidai M.G yana burgeni, gaba ɗaya baida wani matsala kaman ɗan'uwan shi, shi baida wani sara sai hararan mutane da shegen son girma, ni mai yawan ɗaure fuska baya burgeni a duniya nan, ima son mutum mai faran-faran, gashi fari dogo ga fara'a", murmushi na sakeyi na miƙe nayi parlor wurin su hadiza.
Wuraren 9:00 M.G ya ƙira waya na yana tambayan mun shiryah,? Ido na yana kan zainab da take wani juyi a jiki mirrow tana kallon kyaun da tayi da aka mata make-up da aka mata, koni kallon kaina nake tayi ina ganin yadda na chanja kama, amma dai gaskiya yayiwa kowan mu kyau, domin ba'a wani tsauwala mana shi da yawa ba, muryan shi naji yana "tou ku fito na shigo gidan", amsa mishi nayi da "tou" sannan na kashe wayan, kallon su nayi nace su fito muje, dama Aunty Bintu tunda na gaya mata ɗazu tace yama fi mata sauƙi, don ita da yayah moha zasu tafi, hafsy da ummitah ma tare zasu tafi da su yayah umar, dama na gayawa ummie nah M.G yace zai kaimu, nasiha ta mun da mu tsare mutuncin mu kuma banda rawan kai, a haka muka fito, kowan mu tasha lace mai musulmin kyau, orange ne colour nawa, na hafsy black da golden, an mana wani fitted gown, ga gyalen mu shantily, munyi kyau dukkan mu kaman ka ɗauke mu ka ɓoye, *"MASHA ALLAH*"
Naji muryan M.G yana faɗi lokacin da muka iso jikin motan, shima lokacin ya fito ya buɗe mun gaban motan yana wani sara mun, hakan da yayi sai duk ya saka mun dariya, naji kunyan abunda yamun har sai dana ɓoye fuskana a tafin hannu na, Ya Rabbi M.G yana da kyau da burgewa, nidai halayen shi da ɗabi'un shi sun fara burgeni, ina son yabawa, ina son kulawa sosai, haka na shiga gaban na zauna, maryam, fatima, hadiza, zainab suka shige baya, ina jin shi yana tambayan su basu matsu ba? Basu matsu ba suka bashi amsa dayake motan mai girma ce, amare tun yammah aka kaisu, habiba ma da yamma aka kaita gidan ta, amma dukkan mu babu wanda Aunty ma'u ta bari yaje rakiyanta, Aunty Bintu ma nan ta tsaya suka amshi amaryah, kuma ana magrib tana ciki. Wanda suka jagoranci amaryah zuwa gidanta, domin ummie tace a wuce da ita gidanta tayi shirin abun da yake gaban su, shiyasa gidan namu yayi shiru, domin duk an tafi kai amare.
Tunda muka isa M.G bai barmu mun shiga wurin programm ɗin ba, wanda aka shirya yi a *ZARANDA HOTEL* muna zazzaune a cikin motan yana ta jan mu da hira, inda hadiza da maryam suka fi mu zaƙewa wurin hiran, kuma daga dukkan alamu ko wacce a cikin mu taji daɗin yadda yake tafiyar da mu, ango da amaryah basu iso ba sai wuraren ƙarfe 10:00, wata irin jeep ce mai girma da kyaun gaske baƙa wuluk tana shaining ango da amaryah suka iso a ciki, gaba ɗaya kallo ya koma kan motan, inda wasu daga cikin angwaye da ƙawaye suka matso wurin motan suna jiran fitowan su, Ƙafan driver tana buɗewa naga A.G ya fito a ciki, fuskan nan kaman an mishi albishir da ranan mutuwan shi ko alaman ya taɓa dariya babu a fuskan, haka kawai naji yabani haushi, daga nan ango da amaryah aka buɗe musu suka fito.
Kaiii yau wace rana Yayah Ahmad fuskan shi cike da fara'a? Sai wani dariya yakeyi kaman bashi ba, yana fitowa ya matso gefen amaryan shi ya riƙo hannun ta, bamu san me aka gaya mishi ba gaba ɗaya wurin suka ɗauki dariya, angwaye da amaren duka, shi kuma ya ɗan rungumo amaryan shi kusa da shi, dai-dai lokacin M.G yace muje wurin mu gaisa dasu sai mu shiga.
Muna isa wurin yayah Ahmad ya miƙo mun hannu na ƙarasa wurin shi ya rungumoni jikin shi yana sunkuyawa kunnen amaryan yana mata magana, inaji ta saka hannun ta tajawoni kusa da ita, dayake fuskanta rufe yake da mayafinta, gaisheta nayi zuciyana cike da ƙaunar ta, bayan mun gaisa abokan shi suka fara maganan a jera yadda za'a shiga DJ yana announcing shigowan su, jin haka mukayi niyyan shigewa cikin hall ɗin.
Juyawan da zanyi naji an riƙo hannu na an jawoni, tunani na Yayah Ahmad ne, amma juyawan da zanyi sai naga hannun A.G ne riƙe da nawa, ina ji ya jawo ne baya kusa da ƙofan da ya fito na motan, gaba ɗaya idon M.G yana kanmu, Yayah kuma kallo ɗaya yayi mana ya sake maida kanshi kan abokin shi da yake maganan su gyara yadda za'a shige.
"ki maida hankalin ki nutsu a wurin nan, idan kikayi wani abu da bai mun ba zaki koma gida a ƙafa", A.G ya faɗa mun murya ƙasa-ƙasa wanda nima da ƙyar nake jin shi, ga wani yankewar zuciya da na samu kaina inayi akai - akai, bai ishe shi ba ya sake cemun, "wani irin kwalliya ne aka miki gaba ɗaya ya maida ki kaman dodo? Ga wani gyale kaman wani gidan sauro?"
Zuciyata naji ya ɓaci na yanda ya wani kushe ni, turo baki nayi gaba kaman zanyi kuka, "zan buge mummunan bakin nan idan baki gyara shi ba", "kana bugewa zan buge naka, kabarta ƴan'uwan ta suna jiranta zasu shige ciki" M.G ya faɗa yana ƙarasowa inda muke, harara A.G ya mishi sannan ya sake hannuna, yana sake ni da sauri na ware nabi bayan su maryam jiki na yana rawa.
*AUNTY NICE*
managarciya