Matsalolin Da Yawan Kwalliyar Zamani Ke Haddasawa Jikin Mata

  Kwalliyar zamani a yanzu ta zama ruwan dare game duniya, mata na aikatawa sosai ba tare da la’akari da illoli da masifun da ke cikin kayan ba.  Wannan abu ne da ya kamata uwaye mata su tashi tsaye wajen magancewa don su tsiratar da lafiya jiki da idon ‘ya’yansu. A yau ‘yan mata sun zama fitila mai haska duniya su kona kansu. Ya kamata a kula domin ina amfanin badi ba rai.

Matsalolin Da Yawan Kwalliyar Zamani Ke Haddasawa Jikin Mata
Hafsat Idris

                                                  

 

 

 

 

     Bayanai daga kwararrun masana lafiyar fatar jiki sun yi magana kan kwalliyar zamani, sun shawarci mata da rage yin kwalliyar kullum safiya, domin ta na iya bata musu ido da fatar fuskokinsu. Kayan kwalliyar suna hade da wasu sinadarai da fatar fuska da kwayar ido ba su bukatarsu a kowane lokaci.

   Kan wannan  Managarciya ta yi bincike kan illolin hodar nan mai maski da dangoginta da ake kira P.O.P. da sauran kayan kwalliyar zamani, in da ta gano illolin kamar haka:

 

1 – Rashin daukar Ciki ga mace – A nan masana sun ce yawan irin wadannan kayan shafe-shafe na iya sanya mace ta ka sa daukar ciki(juna biyu) saboda akwai wasu abubuwa a cikin man da ake shafawa ya ke shiga ta kofofin gashi zuwa cikin jikin mace da kan sa hakan ta faru.

2 – Yana kawo tsufa da wuri ga mace, za ka ga budurwa tana tsufa haka kawai jikinta ya tamure ya bambanta da yawan shekarrunta.

3 – Yana kawo cutar dajin fata, wato ‘Cancer’.

4 – Yawan ciwon kai.

5 – Tsigewar gashi a jikin mace.

 

Masanan sun fadi wasu hanyoyi da za a iya bi domin samun kariya daga wadannan matsaloli kamar haka:

1 – A rage yawan shafa jar hoda domin yawan shafa ta na kawo kurarraji a fuska. Kamata yayi a shafa farar hoda.

2 – A daina shafa tozalin zamani wanda wasu ke kira da ‘Gazar’ ko kuma da turanci ‘Eye Liner’ domin yana dauke da sinadarin da ke kashe ido. Kamata ya yi a shafa tozalin gargajiya ko kuma ‘Kajol’.

3 – A daina amfani da kayan kwalliyar da suka tsufa (domin sinadarin su ya tsotse ya tashi daga aiki, ba su dauke da komai sai illa a fatar jiki).

4 – Amfani da gashin idon kanti wato ‘Eye lashes’ na kawo rashin karfin ido domin ana amfani da gam kafin a manna shi kan gashin ido, wanda idan an je cirewa ya kan kawo wasu matsaloli kamar kumburin ido, rasa gashin ido, kurarraji da sauran su.

5 – A daina amfani da ‘Contact Lens’ domin yana kawo makanta. (Contact lens wani abun kwalliya ne da ya yi kama da leda, wanda mata kan saka shi a ido domin canja launin idon su).

 

   Kwalliyar zamani a yanzu ta zama ruwan dare game duniya, mata na aikatawa sosai ba tare da la’akari da illoli da masifun da ke cikin kayan ba.  Wannan abu ne da ya kamata uwaye mata su tashi tsaye wajen magancewa don su tsiratar da lafiya jiki da idon ‘ya’yansu.

A yau ‘yan mata sun zama fitila mai haska duniya su kona kansu. Ya kamata a kula domin ina amfanin badi ba rai.