Hajiya Amamata Area Ta Ɗauki Nauyin Koyawa Marayu 50 Sana'ar Hannu A Sakkwato

Hajiya Amamata Area Ta Ɗauki Nauyin Koyawa Marayu 50 Sana'ar Hannu A Sakkwato


Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto 


Shugaban Kungiyar tallafawa mabukata da marayu waton Garba Area Multi link Services Dake sokoto,
Hajiya Amamata Abubakar ta bayar da Tallafin kudi dalar Amerika 100 kimanin naira dubu 56,000, ga wata kungiyar taimakon Marayu Mai suna (Flag Global Foundation)da take Hannunta kudin ga shugabar kungiyar, Hajiya Amamata Abubakar, ta bayyana cewa a madadin kungiyarta ta bayar da kudin ne domin tallafawa Marayu 50 wadanda za'a koya musu sana'oin hannu, cikin Marayu 1153 da kungiyar Global Foundation ke daukar nauyin su.

Shugabar kungiyar ta yabama yadda Shugabannin kungiyar Flag Global ke gudanar da ayukkan su, tare da Basu tabbacin yin aiki tare duba da yadda kungiyoyin ke aikin Jin kan Al'umma.

Da yake jawabi a wajen taron Dukajin zazzau Alh Abubakar Garba Shehu, ya godewa Shugabar kungiyar Garba Area akan wannan Tallafi da ta bayar domin tallafawa Marayu.
An dai Hannun ta kudin ne a wani kwarya kwaryar taro da aka Gudanar a Garin zariya ta jihar kaduna.