Gwamnan Kano ya bada Umarnin kama tsohon sarkin Kano Aminu Ado Bayero
Daga Ibrahim Hamisu, Kano.
Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif ya baiwa Kwamishinan 'yan sandan Kano umarnin kama Sarkin Kano na 15 wato Alhaji Aminu Ado Bayero.
Gwamnan ya sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da kakakin sa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a safiyar nan, inda yace matakin yazo ne saboda zargin ƙoƙarin tada hankalin al'ummar Kano,
Hakan dai baya rasa nasaba da wasu rahotanni dake cewar sarkin Kano na 15 wato Alhaji Aminu Ado Bayero da gwamnati ta sauke yake kan hanyar sa ta komawa fadar masarautar Kano daga Abuja.
Wata sanarwa da Sakataren yada Labaran sa, Abubakar Balarabe Kofar Na'isa ya fitar, ta bukaci magoya bayan Aminu Ado Bayero su fito su tare shi da safiyar yau Asabar a filin jirgin saman Malam Aminu Kano domin raka shi gidan Dabo.
managarciya