HAƊIN ALLAH:Labarin Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Farko

Nafi awa biyu a yanayin sannan na samu bakina ya fara furta "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Hawaye masu mugun ciwo suka zubo min, me yasa ƙawata aminiyata wadda na fifita ta da kowa tai min haka? Me na ragi mijina da shi wanda yasa ya ci amanata mafi munin cin amana? Wace irin rayuwa ce nake a gidan mijina? Duka yaushe akai zaman da zai saka mun da wannan sakayyar?

HAƊIN ALLAH:Labarin Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Farko
*HAƊIN ALLAH* 
 
          Labari da rubutawa
  
    *Hauwa'u Salisu (Haupha)
 
 
 

 

Sauri nake ta yi na samu na isa gidana, saboda wata uwar rana da ake sheƙawa Yau, ko da na zo ƙofar gidan na ganshi a rufe, amma ta ciki aka rufe sai na ji daɗi, domin dama da biyu na zo idan na iske mijina bai nan na shige gidan maƙwabciyata Binta na zauna har sai ya dawo domin yau ban iya wucewa gidansu ko gidanmu kamar dai yadda na saba mafi yawan lokuta.

 
Tsaye nake, ga uban ciki sai buga ƙofar gidan nake amma ba alamar zai buɗe gidan, ga rana ana zabgawa mai shiga cikin kwanya, ga ciki ga gajiya, mutane nata wuce ni suna girgiza kai wasu na tausayi, wasu kuwa na ke kika ji za ki iya ne. Iyakar gajiya na gaji domin daga asibiti nake na je awon ciki kuma yau na sha wahala domin tun safe sai ƙarfe ɗaya na samu na dawo daga asibitin, ga yunwa ga ƙishirwa duk sun addabe ni, ga rana a nayi kamar me, amma Deeni ya ƙi buɗe min gidan na shiga, tunani nake a raina ko wane irin barci yake bai jin bubbuga ƙofar da nake yi? Duk na galabaita sai goge zufa nake, na yi tsaye na ma kasa ci-gaba da buga ƙofar gidan ma. Wani matashin saurayi ne ɗan cikin unguwar ya tsaya yace, "Amarya har yanzu bai buɗe gidan ba wai? Nan fa na wuce ki na je na dawo duk kina nan kuma, ko dai na hau ta katanga na buɗe maki gidan ne ko barcin ya yi nisa bai jin ki? Ajiyar zuciya na saki domin har ga Allah ta fara shirin yin kuka kan halin da nake ciki, don haka ban musa ba nace "Don Allah S.K ka shiga ka buɗe min wallahi na gaji sosai."   Ya cire takalma ya haye katangar gidan da yake gajera ce, ya buɗe min na kuwa shige cikin yanayin gajiya ina gode ma shi taimakon da ya yi min. 
 
Da sallamata na isa ƙofar ɗakin, sai dai ganin wasu takalma yasa gabana mugun faɗuwar gaske, haka nan na jini cikin firgita na dafe ƙirjina dake bugawa kamar zai fito. Hannuna   nasa na yaye labulan ɗakin, nan take  idanuna suka sauka kan tsakiyar falon, abin da na gani ne yasa idanuna neman daina gani, kaina ya fara juyawa na dafe kan na  zube rubda ciki a gun cikin tsananin tashin hankali da ɗimauta, can cikin bakina nake furta  "Safiya!!!  Shi ne sunan data ambata cikin maƙoshinta wanda ya kasa bayyana a fili.  Cikin tashin hankali da damuwa Safiya ta saka kayanta ta fice da gudun masifa tana waigen ƙawarta dake kwance cikin mawuyacin hali na kamata dumu-dumu da mijinta da ta yi a cikin gidanta cikin ɗakinta suna cin amanarta. Shi kam Deeni duk yadda ya so ya dake kasawa ya yi, sai da ya ruɗe, ya ɗebo ruwa ya yayyafa mata ya samu ta tashi zaune, ko da yaga ta dawo hayyacinta sai ya fice daga gidan ba tare da yace mata komai ba.
 
Tamkar ba nice na dawo a jigace ba, tamkar ba nice ke jin yunwa da ƙishirwa ba, tamkar ba nice mai ɗauke da ciki wata tara ba, sai naji na manta komai, komai ya tsaya min, ba abin da nake iya ko tunawa ko a cikin idanuna na zama tamkar wadda komai nata ya goge (loosing memory) haka na koma, ban iya ko ɗaya halshena haka zuciyata ta rufe jikina ya yi sanyi, baki ɗaya na kasa gane a wane yanayi nake kawai dai gani a duniyar kamar ba ni haka nake ji komai ya tsaya cak a rayuwata.
Nafi awa biyu a yanayin sannan na samu bakina ya fara furta "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Hawaye masu mugun ciwo suka zubo min, me yasa ƙawata aminiyata wadda na fifita ta da kowa tai min haka? Me na ragi mijina da shi wanda yasa ya ci amanata mafi munin cin amana? Wace irin rayuwa ce nake a gidan mijina? Duka yaushe akai zaman da zai saka mun da wannan sakayyar? Shekara guda kenan da aurenmu, shi ne ya ganni yana sona haka zalika shi ne ya kai kan shi gidanmu har ga iyayena, ba shi ne zaɓina ba a lokacin amma saboda darajar Kakannina yasa aka ba shi ni ba tare da an duba cewar wanda nake so daban ba... Sallamar Gaje naji matar Yayansa amma na kasa goge hawayen idanuna,haka na saka daina ganin lamarin a fuskata. Safiya da mijina suna aikata zina a cikin gidana cikin ɗakin aurena! Tabbas dole inyi kuka, idan akwai abin da ya fi kuka ma dole inyi ... Gaje ta dafa kafaɗata "Jiddah lafiya kike kuka ke kaɗai a cikin gida? Ko jikin ne? Ina Deeni yake? Duk a lokaci guda ta jero min tambayoyin nan wanda ko guda ban jin zan iya amsawa, to ta ya zan kirari a kasuwa kuma na daɓa ma cikina wuƙa? Deeni mijin aurena ne uban abin da ke cikin cikina, ita kuma Safiyar ƙawata ce ta gasken-gaske, da zuciya guda nake sonta, ban da ƙawar da ta wuce ta, duk da cewar dama can ta girme ni nesa ba kusa ba, amma na ɗauke ta tamkar ƙawata, komi nayi sai nayi mata, tun da na santa da aurenta na santa kitso ne silar haɗuwar mu daga nan na dinga tausan yadda take rayuwar aurenta, wannan yasa na amince ta zama babbar ƙawata duk da cewar ta girman... "Jiddah don Allah ki gaya... Sallamar maƙwabciyar Jiddah tasa Gaje yin shiru ta amsa sallamar ta maida hankali kan Binta data shigo gidan. "Gaje tare kuka zo kuka iske lamarin kenan? Wallahi kullum nayi niyyar gaya mata gaskiya sai naji tsoro saboda yadda mutane suke kada ace ka kashe ma mutum aure." Kallo na bi Bintar da shi ina mamakin yadda akai take wannan maganar, wace gaskiya ce zata gaya min? Me mutane za su ce? Wane aure ne zata kashe?  Gaje tace, "Binta ai ita gaskiya ɗaci ne da ita daman, amma matsayinki na maƙwabciyar ta bai kamata ki ɓoye mata gaskiya ba, nasan da ita ce wallahi ba zata ɓoye maki komai ba." Binta tai ajiyar zuciya tace, "Yau tare mu ka je da ita asibiti gun awon ciki, amma sai ta tafi gidan Auntynsu Usaina tace tai kalaci bata iya zama da yunwa, hakan yasa layinta ya koma baya sosai bayan ta dawo, to ni kuma da akai min naga da saura ita sosai sai nace mata na tafi sai ta dawo, tace min ai har na rana sai ta je ta ci gidan Aunty Usaina kafin ta dawo gida tasan ita da gida sai yamma Yau. Hakan yasa na wuto abuna ni kaɗai, to ban jima da dawowa ba mijinta ya yi min sallama ya tambaye ni yaushe zata dawo ita? Nace ma shi sai yamma ka ji yadda mu kai da ita, ya juya ya tafi, ban jima ba na fito zan je gidan markaɗe naga Safiya ƙawarta nata waige-waige ya buɗe mata gidan ta shige ya rufe, to ban san ya akai ba sai ta dawo da wuri kuma duk kan idona ta buga da sanda tasa aka buɗe mata, haka naga sadda ƙawarta Safiya ta fice da gudu a ruɗe, nasan kuma dubu ce ta cika domin ba yau suka fara ba daman kowa yasan tana zuwa duk sanda Jiddah ta bar gidan nan."    Gaje ta dafe ƙirji tana Salati, Ni kam ban da ta sauran cewa asiri ya tonu mutuncin mijina ya jima da zubewa a she ban sani ba? Waye wai mijin da nake aure? Ashe shi yasa kullum yake cewa na je gidansu na yini ko naje gidanmu? Ashe dama abin da yake yi kenan? Ko shi yasa nake yawan ganin gyalen ƙawata Safiya ko hijabinta ko takalma a gidan yace min biyowa tai zata je unguwa ta aje nata ta ɗauki nawa? Tun yaushe suka fara cin amanata? Me yasa bai ban haƙuri ba ya fice? 
 
 
 
 
Ku biyo Haupha don jin ya lamarin yake wai? 
Wacece asalin Jiddah?
Wacece asalin Safiya?
Wanene Deeni mijin Jiddah? 
Wace irin rayuwar aure ake?
Wane mataki Jiddah zata ɗauka kan Deeni da Safiya?