HAƊIN ALLAH Labarin Soyayya Mai Rikitarwa: Fita Ta 43

HAƊIN ALLAH
Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
Page 43
Ya jima yana wankan, domin ya ji daɗin ruwan sosai yadda suke fitar da ƙamshi gasu da ɗan ɗumi hakan yasa ya kwashe dogon lokaci bai ankara ba.
Yana fitowa ya sake cin karo da wani ƙamshin a ɗakin, tana zaune tana latsa wayarta ko bai faɗa ba yasan hotunan da akai ne ɗazun take kallo.
Tana ganinsa ta tashi da sauri ta ɗauki towel dake gefenta ta fara tsane mai jiki sai ya yi tsaye tamkar wanda ya suma saboda tsabar farin ciki, irin wannan kulawar yake addu'ar samu ga shi tun farko an fara da wadda ma bai zata ba.
Man shafawa ta ɗauko ganin ya kasa motsawa daga inda yake yasa ta kama hannunsa ta kaishi kan stole ɗin gaban madubi ta zaunar da shi, a hankali cike da natsuwa tana kashe shi da murmushi ta fara shafa mai man.
Hure mai ido tai sai kuma ta duƙa a hankali ta fara sunsunar wuyansa, kamar a mafarki ta janye fuskarta tace "Prince ya naji haka?"
Ya dube ta da ƙyar ya ce, "Princess me kika ji ne?"
Ta zumɓura baki tace, "Ji nayi baka fita ba sam ba kai wankan kirki ba, gaskiya ba zan yadda ba mu je na sake yi ma da kaina."
Murmushi ya yi ya saba da zolayar Princess ɗinsa bata so su zauna ba tare da suna tattaunawa ba ko suna tsokanar juna ba, wanda hakan shi ke ƙara masu son juna da shaƙuwar gaske.
Tashi ya yi ya ce, "To amarya mu je ai duk yadda kika ce haka za ai ba mai musa maki zance ki koma ya yake wallahi, ko sau ɗari za ki ce nayi wanka zan yi don girmanki ne hakan ai."
Dariya tai lokacin ta gama shafa mai man, ta ɗauko turare ta fesa mai, sai kuma ta kalle shi ta fashe da dariya tace, "Prince wane kaya zaka saka na barci ne? Kasan ba kayanka ko guda a cikin gidan nan fa."
Ya saki baki yana kallonta, tai mai masifar kyau na ban mamaki, ganin bai tanka ba yasa ta buɗe kayanta ta fito da riga da wando ƙanana ta ba shi tana dariyarta tace, "Ga aro nan na baka zuwa safe idan kuma akai min datti da kaya za a wanke min abina." Ta nufi toilet ɗin ita ma don tai wankan.
Ya ɗaga kayan sun yi mai kyau ya yi mamakin yadda da yasa kayan suka amshi jikinsa sosai ya zauna yana ƙarewa ɗakin kallo yadda aka tsara shi ya yi kyau na ƙarshe abin sai ya sake ba shi nishaɗi.
Ta jima tana wanka, kafin ta fara tunanin idan ta fito kuma me zai faru oho? Tana gamawa tai alwala ta fito yana kwance yana kallon saman ɗakin tamkar mai tunani.
Cikin natsuwa ta shafa manta ta fesa turare ta ɗauki kayan barci masu ɗan mutunci ta saka ta ɗora zani sama ta taka a hankali har inda yake kwance tace, "Prince na shirya tashi mu yi sallar barci naje ji kasan gobe zan ƙulle kuɗin sadakina naje sarin kaya Lagos kamar yadda mu kai da kai."
Dariya ya saka yana kallon yadda take maganar tsakaninta da Allah ba wani alamar wasa a fuskarta.
Tashi ya yi domin jiranta yake shi daman har kafet ɗin sallar ya shimfiɗa jiranta kawai yake.
Bayan sun gama sallar ne ya dinga kwararo addu'ar neman zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba a tsakaninsu. Ita kuma ta dinga addu'ar Allah Ya taimake shi ya ba shi ikon sauke nauyin dake kanshi ya kuma riƙe alƙawarin dake tsakaninsu Ya ƙara mai buɗin alheri a rayuwarsa.
Suna gamawa ya janyo kaza da fura tare da kayan lambu ya ce, "Nasanki da shegen kwaɗai don haka kazar za ki fara yi ma sallama dai."
Dariya tai, tace, "Ai kuwa dai kamar ka sani don haka ma naga ka saka kejin kaji a gidan nan saboda idan zan ci ba sai kowa ya sani ba." Ta ida maganar tana mai hararar wasa.
Suna wasa suna dariya har suka gama cin kajin suka kora da kayan lambu sai Jiddah ta kama hannunsa suka fice ya bita yana kallon inda zata da shi kuma.
Gudan ɗakin ta kaishi ta rungume shi tai mai kiss ta juya tana cewa, "Mu kwana lafiya Prince kar da ka makara kasan gobe da asuba akwai gyaran gida da yi ma amarya Princess girki."
Ganin ta ja ƙofar da gaske ta fice yasa ya kasa ko buɗe baki balle ya yi mata magana sai kawai ya bi ƙofar da kallo kamar wani yaron goye .
Tana shiga ɗakinta ta fashe da dariya tana tunano yadda fuskar Prince ta koma data barshi tsaye tana kora mai jawabin da ya daskarar da shi gun.
Cikin sauri ta sake fesa turare ta kunna turaren ɗaki ta sauya kaya zuwa masu masifar kyau ta haye gadonta tana murmushi.
Ganin da gaske take sai ya samu ƙarfin halin takawa a hankali ya buɗe ɗakin jikinsa sanyi ƙalau ya nufi nata ɗakin ba tare da yasan me zai ce mata ba idan ya je.
Ƙamshi mai daɗi ya ziyarci hancinsa, ya shaƙa ya sake shaƙa ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta kwance ta lulluɓe jikinta duka tai lamo don yasan bata isa yin barci ba daga zuwanta ba.
"Princess." Ya ambaci sunanta cikin murya kamar zai kuka.
Juyowa tai daga kwancen ta watsa mai idanunta fuskarta fal fara'a tace, "Na'am Prince, baka kwanta ba ne? Ko akwai abin da kake buƙata ne?"
Kasa magana ya yi domin baisan me zai ce mata ba, don haka ya isa kan gadon ya zauna ya ce, "Kin taɓa cemin ba za ki iya barin mijinki ya kwana ɗakinsa ba, to me yasa Yau ni kike son na kwana nawa ɗakin na daban?"
Sai kawai ta tashi zaune tace, "Yanzu har ka manta alƙawarinmu dakai Prince?"
Cikin rashin fahimta ya ce, "Wane alƙawarinmu kuma Princess?"
Ta shagwaɓe fuska tace, "Kace min ba zaka kwana ɗakina ba sai bayan shekara biyu domin raino na za kai nayi yarinta da kwana da miji ɗaki guda."
Sakin baki ya yi galala yana kallonta, wai da ita a tunaninta da gaske yake mata wannan maganar? Cabɗijam! Sai kace dai wanda ya yi auren dole ba auren so da ƙauna ba?
Janye bargon jikinta ya yi ya ce, "Af, na manta fa, amma bari na duba nagani ko kin isa kwana da miji ko har yanzu sai na yi rainonki."
Tai saurin janyo bargon ta rufe jikinta, bayan ya riga yaga komai.
Cikin muryar shagwaɓa tace, "Kai Prince, kai ne fa kace zaka barni sai bayan shekara biyu sannan na zama ƴar duma-duma."
Dafe bakinsa ya yi ya ce, "Kai wannan baki baka kyauta ba da ka faɗa wa Princess abin da bai yiyuwa, amma dai bari mu gani." Ya sake ƙoƙarin cire bargon daga jikinta.
Ta kuwa riƙe bargon ta fara yin kukan shagwaɓa, bai san lokacin daya ida hayewa ba ya janyo ta jikinsa yana bubbuga bayanta tana cewa, "Sorry Princess ba zan sake ba, kin ji, ban san kina damuwa ji nake kamar zuciyata ta fashe don tsabar tashin hankali."
Lub tai jikinsa ƙamshin turarensu na ƙara masu nishaɗi a zukatansu.
Ɗago kanta tai ta kalle shi ta zumɓura bakinta ta sake fashewa da kukan shagwaɓar.
Baki ɗaya ta rikita shi ya rasa me zai mata sai kawai ya rungume ta ya fashe da kuka yana cewa, "Na gode! Na gode ! Na gode sosai Princess Allah Ya ban ikon riƙe ki kan amana da gaskiya, Ya azurtani da yi maki duk wata buƙata taki Yasa na zama abin alfahari a gareki ."
Jikinta yai sanyi ganin yana kuka yana magana wadda tasan da gaske daga can ƙasan zuciyarsa take fitowa sai itama ta kama hawaye ta shige cikin jikinsa sosai tana cewa, "Don Allah ka daina kuka kana tada hankalinka a wannan rana mai daraja, a wannan rana mai alfarma, a wannan dare mai cike da farin ciki da nishaɗi tare da cikar dukkan burikanmu Prince. Insha Allah za mu rayu cike da farin ciki tare da walwala mai ɗorewa har ƙarshen rayuwarmu. Ina maka kyakkyawan zato wanda ya inga dukkan tunanina yasa na amince da kai ya tunzura zuciyata da jikina ƙara ƙarfin sonka da ƙaunarka da son aurenka. Shin Prince ka taɓa tunanin zuwan wannan ranar a shekaru biyar zuwa goma da suka wuce ne?"
Kanshi ya girgiza mata don kuka bai barinsa faɗin ko da kalma guda.
Ta cigaba da shafa sumar kansa tana magana cikin zubar hawaye, "Ka sani Prince ba kai ya kamata kai kuka ba, ba kai kuka ya kama ba, sannan ba kai fargaba ya kamata ta kama ba Prince nice, saboda kafin auren nan an faɗa min maganganu da dama akan ka da halayenka wanda na runtse ido na toshe idanuna nayi kunnen uwar shegu da su na kafe sai kai duk da tarin masoya da Allah Ya azurtani da su kaine kawai ka zauna min a raina ka mamaye min duk wata jijiya da tsokar dake jikina. Prince ka zama jajirtacce mai kauda kai daga dukkan abin ƙi mai aikata abin da za a yaba mai, wanda kowa zai dinga Allah san barka da halayensa."
Ƙara shigar da ita ya yi jikinsa sosai yana cewa, "Nayi maki alƙawarin hakan Princess don Allah kema ki dinga saka Ni a hanya idan kinga na kauce daɗin zaman kenan Princess kin ji?" Ya ɗago mata kai yana kallon idanunta.
Itama cikin kukan take share mai hawaye yana cewa, "Nai maka wannan alƙawarin Prince nima idan kaga ina ba daidai ba ka zaunar dani cikin natsuwa da lumana ka gayamin abin da nayi ban daidai ba zan baka haƙuri kuma na gyara kuskuren ba zan sake aikatawa ba."
Sun jima suna yi ma juna alƙawarin zama da lafiya da taimakon juna da kulawa da juna har ƙarshen rayuwarsu. Sannan labarin ya sha bambam domin Prince ya rikice mata shi ala dole bai san wane lokaci ya ce mata zai raine ta saboda shi idan tana gabansa manta wane hali ma yake ciki yake sam.
Sanin cewar daman ranar suke jira, kuma shi ne matafin farko na samun nishaɗi a rayuwar aurensu da nuna godiya ga Allah Yasa ta saki jiki ta taimaka mai ta ba shi kulawa iyakar kulawa sai ga Prince na faɗin "Princess nayi maki kyautar kaina, na baki komai nawa ke ce ma mai Ni ke Princess Allah ke ce kika aureni."
Ita dai ba baka sai kunne domin abin ya girmi kunnenta don haka sai ta yi tsit kawai tana amsar saƙon da kowace jijiya ke amsa daga gun Prince ɗinta.
Sai da taga yana neman yi mata rauni sannan ta dinga ture shi amma ina shi bai ma san me yake faruwa ba don zuwa yanzu ko magana ya kasa sai tashin nishinsa kawai da kalmar Princess kawai yake iya ambata.
Sai da tai da gaske sannan ta ture shi ta mirgina gefen gadon ita kaɗai tasan me take ji a jikinta.
Shima sai ya yi lamo kawai yana hangen taurari na yawo a sararin samaniya yana ganin furanni na kai da kawowa ga network ta ko'ina na yawo duk a idanunsa.
Sun jima kowa jiki ba ƙarfi sannan a hankali ta tashi ta nufi toilet ta haɗa ruwan zafi ta shiga kenan sai ga shi ya shigo, kunnenta ya kama ya ɗan ja, tai ƙara ya ce, "Me yasa kika taho baki jira na ɗauki ki ba? Kin manta da aikina ne ɗaukarki nayi maki wanka na shafe ki ko'ina na kwantar da ke jikina ki yi barci ina baki labarai masu daɗi da saka barci cikin nishaɗi ba?"
"Afuwan Prince, na tuba ba zan sake ba, sai dai kar ka manta nima wannan shi ne burina naga nayi maka komai na tsare maka komai na saka barci cikin nishaɗi."
Rungume ta ya yi bai damu da kayan jikinsa ba yana cewa kenan wayau kike so ki yi min kenan komai kice ke ce za ki yi Ni kuma ba zan komai ba kenan? Gaskiya ba zan yadda ba Princess nima ina son naga ina taimaka maki gun ayyukan gidan nan dama kin gane komai tare zamu dinga yi."
Zuwa yanzu su duka sun afka babin wankan tana yi mai yana yi mata, suna tsokanar juna ta hanyar watsawa juna ruwa. Sun ɗauki lokaci suna wankan sannan suka fito ko wajen fitowar ma sai da suka saida halin don Jiddah cewa tai sai dai ya goya ta, shi kuma ya ce idan ya goya ta to zai sake mata garambawul don ya lura a zabure take sosai.
Kan gado ya ɗora ta ya ɗauki towel yana tsane mata jiki itama tana tsane mai nashi jikin, turare kawai ta fesa masu suka sake kwanciya ta shige cikin jikinshi sukai shiru kowa na tunanin yadda rayuwarsa ta juya Yau shi ne kwance cikin yanayin da yake gani a mafarki.
Jiddah ta ɗan bugi ƙirjinsa tace, "Prince ka kwanta kai barci saboda gobe nasan jama'a za su zo da wuri kada barci ya hanaka amsa taya murnar aure gobe."
Shafa ƙananan kitson kanta ya yi ya ce, "Ke dai Princess ki faɗi gaskiya kada gobe na fita ace lallai na auri jaruma kwana guda har ta gama mai aiki ya ƙara tsawo."
Sunne kanta tai cikin ƙirjinsa tace, "Kai Prince ban da sharri dai, Ni ban ma san komai ba, don haka ba ruwana."
Murmushi ya yi ya ce, "Ni kam kinga na sani domin Yau naga network kala-kala naga kuma sararin samaniya haka naga furanni na yawo a saman ɗakin nan."
Dariya tai, don tasan me yake nufi, don haka sai tace, "Ni sai ba ruwana don Malama ce kowa yasani."
Shima ya yi dariya ya ce, "Kai ai Ni zan bada wannan labarin don tunda nake ban taɓa amsar irin wannan darasin ba sai Yau gaskiya Malama kullum zan dinga amsar darasi daga gareki ba dare ba rana balle safiya."
Dariya tai mai ɗan sauti tace, "Duk ban san wannan ba, amma dai nasan an ban manyan kyauta kala-kala kuma gobe zan ɗauki kyautuka na saboda na baka ta rabani da abuna."
Ya ɗago inda ta nufa don haka sai ya yi murmushi kawai yana sake jin wani sabon nishaɗi na zagaye ilahirin jikinsa ya ce, "Ai Ni da sauƙi tunda har nayi kyauta ke fa? Ai tsabar amsar saƙon da nake baki ko kalma guda kasa furta wa ki kai sai santin kurma kawai ki ke wanda kowa yasan yafi kowane santi."
Sun kai wajen ƙarfe biyun dare ba su yi barci ba, haka ba firar kowa suke ba, firar kansu suke da kansu, sai tsabar tsokanar juna kawai.
Washegari tunda asuba suka tashi ya yi alwala ya fito ta ɗauka masallaci zai je sai kuma ta ga ya zauna ga alama ita yake jira.
Ta dube shi da alamar neman ƙarin bayani sai kuma tai murmushi ta isa inda yake ta kama hannunsa tace, "Mu je na raka ka ƙofa Prince yanzu an tada salla kar da ka makara."
Wata ƴar harara-harara ya jefa mata ya ce, "Tab ina ango ina zuwa Masallaci ranar farko na angonci?"
Dariya ta saka ta dube shi sosai tace, "Ai na manta ai Malam ango ashe fa bakai ba fita sai bayan kwanaki huɗu ko?"
"Ai daɗina dake saurin fahimta don haka maza ki yo alwala mu yi sallah domin so nake na ƙara ɗaukar darasi ya Malamata mai ɗunbin ilimi da tarin hadisai."
Sanin idan ta biye mai har gari ya ida waye wa basu yi sallar ba haka basu daina tsokanar juna ba yasa ta faɗa toilet ɗin tana murmushi.
Suna gama sallar ta jashi suka koma barci duk da idan zata biye mai to darasin zai sake ɗauka amma sai tai mirsisi tace barci ya kamata su yi tunda akwai gajiyar biki jikinsu. Ba don yana so ba, sai don bai san takura mata, kuma yasan tai namijin ƙoƙari a jiya da ta ɗauke duk buƙatarsa ba tare da raki ba duk da abin ya koma mata sabo, don shi da ace bai san yaranta ba zai iya rantsuwa a rufe ya same ta.
Cikin jikinshi ta shige tai lub da ita yana shafa kanta har barci ya ɗauke shi, daman haka take so ya yi barci ta tashi tai ma shi breakfast don haka tabi a hankali ta zare jikinta ta kanga mai filo kamar ƙaramin yaron goye ta sunkuya tai mai kiss ta fice tana murmushi.
Jinta take wasai kamar ba ita ba, duk da ta ji jiji hannun Prince ɗin nata amma sai take ganin ba komai bane, gwara ta haɗa mai breakfast kafin ya tashi, don ta lura bai damu da cin abinci ba shi yasa yake ta ƙara tsawo ba ƙiba.
Kicin ta nufa kai tsaye, sai kuma ta zubawa kayan kicin ɗin ido tana son tuna abin da ya kamata ta shirya mai na breakfast ɗin.
Ganin ba a kai ga kawo doya da kayan miya ba gidan yasa kai tsaye ta zuba ruwan zafi ta ɗebi fulawa ta dama kunu ta zuba madarar gari wadatacciya a ciki ta zuba flover don ya yi ƙamshi, ta sake ɗibar fulawar ta kwaɓa fanke, Sannan tai tsaye tana tunanin me kuma zata sake yi mai tunda babu kayan miya da dankali da doya a gidan. Sai kawai ta haɗa kayan ƙamshi ta zuba Lipton ta haɗa mai ruwan tea ta ɗauko sauran kajin jiya ta ƙara masu kayan ƙamshi da haɗi ta zuba a kula masu kyan gaske ta haɗa komai ta jera.
Tana gamawa a gurguje ta koma ɗaki ta share duk da bai komai ba , ta goge ko'ina ta kunna turaren wuta ta fesa turaren ɗaki ta faɗa wanka, tana fitowa ta zaɓi leshinta mai kyau doguwar riga ta saka ta zauna gaban madubi ta zuba kwalliyar gaske ta murza ɗaurin kallabi, daidai lokacin agogo ya buga ƙarfe tara na safe, don haka sai sake gyara ɗakin ta fesa turare ta nufi inda yake kwance a hankali ta sunkuya ta zuba mai ido kawai tana kallon kyakkyawar fuskarsa, wani irin kyau ya sake yi mata, kallon wani kyakkyawa ajin farko take mai wanda bata taɓa ganin mai kyansa ba.
Tunda ta sunkuyo kan fuskarsa ya shaƙi ƙamshin turaren ta sai ya farko ya buɗe idonsa yadda ba za ta san ya farka ba, godiya ga Allah kawai yake yana ƙarawa ganin yadda Allah Ya azurta shi da mata kamar Jiddah.
Ganin sai kallonsa take yasa ya ja mata hanci a hankali.
Dariya tai itama ta ja siririn hancinsa tace, "Good morning Prince."
Tashi ya yi zaune ya jata jikinshi ya ce, "Ba zan amsa ba tunda ki kai wanka kika barni." Ya gama maganar yana haɗe fuska shi ala dole ya ji haushi.
Kunnuwanta ta kama ta ɗan ƙara rusunawa tace, "Afuwan Prince nayi babban laifi amma yanzu zan gyara sai na cire kawai mu sake yi tare, daman ji nake tamkar ban fita ba saboda ba dai nayi ba, haka zalika ina ƙwadayin yin sunnar Manzo na yin wanka tare da mijina, tamkar yadda yake da iyalinsa."
Ganin tana niyyar cire kallabin ya dakatar da ita ya ce, "Kin yi kyau sosai Princess wanda ban san da shi ba sai Yau, kin yi wa kayan kyau sosai ban wayata na ɗauke ki hotuna."
Wayar ta miƙa mai ya shiga ɗaukar ta hotuna kala-kala sannan ya yi mata bidiyo.
Ganin ya kasa dainawa yasa tace, "Prince haka nan sun isa kada a cika wayar bayan akwai na musamman da za ai idan mun shirya."
Cire kayan tai suka sake shigewa toilet ɗin suna maƙale da juna. Suna shiga tai saurin ɗaukar sabulun tace, "Prince Ni zan fara yi maka don na lura ba ƙaramin datti kai ba daga jiya zuwa Yau ba."
Murmushi ya yi baice komai ba, tana can tana niyyar ɗaukar soson yai saurin ɗibar ruwan sanyi ya watsa mata ya fashe da dariya.
Tai ɗan ihu ta faɗa jikinsa tana cewa ba zata yadda ba ita sai ta rama ko saka mai kuka.
Sai kuma ya fara bubbuga mata baya yana cewa cikin siririyar murya, "Afuwan Princess ban san lokacin da marar jin hannun nan ba ya watsa maki ruwa ba amma ki hutunta bakinsa daya kasa gaya maki abin da zai faru." Ya miƙa mata bakinsa nufinsa tai ma shi kiss.
Manna mai kiss ɗin tai da nufin tai mai ƙwalele amma ta makara sai ji tai yai caraf da halshenta yana tsotsa tamkar ya samu sweet.
Sun jima a yanayin har ya fara sauka layi tai azamar janye jikinta, tana cewa time na ƙurewa fa Prince yanzu ka fara jin sallamar mutane kasan Yau ƴan Jalingo za su koma fa."
Shi dai ko magana bai iyawa, don haka tai mai wanka ta tsaya jiran yai mata taga alamar wutar jikinsa ta ɗauke baki ɗaya sai ta nufi yin wankan da kanta, sai kuma ya amsa ya cigaba da yi mata.
Suna fitowa tai mai shafa, shima ya shafa mata mai da powder ta zizara kwalli zata ɗora jan baki ta tuna da wani abu don haka ta aje shi zuwa anjima.
Kallonshi tai ta kalli kayan daya cire jiya ta fara sinne dariya irin alamar zai maimaita kayan daya cire yana matsayin ango guda.
Fahimtar abin da take nufi yasa ya nuna mata wata leda dake can gefen gadon. Tana ɗaukowa taga wata rantsattsiyar shadda mai kyan gaske wadda tana da irinta cikin kayan daya ɗinka mata na cin bikin, hakan yasa ta fahimci iri ɗaya za su saka kenan Yau ma kamar kwanakin baya kala guda suke sakawa.
Da kanta ta saka mai kayan ta ɗauki turare ta fesa mai tana cewa, "Idan aka ƙarar min da turare ba wani daɗin bakin da za ai min sai an biyani abina har da riba."
Girgiza kansa ya yi ya ce, "Ni fa taimaka maki nake ina saka wannan ƙaramin turaren saboda turarena yafi naki nauyi da hidimar ma baki ɗaya."
Zumɓura baki tai ta fara dire-diren ita ba zata yadda ba sai dai a fitar da turare guda kowa ya dinga amfani da shi.
Dariya ya dinga yi yana cewa bai yadda ba shi ba zai dinga shafa turaren mata ba, ta kuwa ƙara ƙaimin abin da take tana cewa ita fa ba ruwanta ƙamshi guda take so shi da ita su dinga yi kawai.
A haka dai ya taimaka mata ta saka tata shaddar, kawai ɗaukar ta ya yi ya kama juyi da ita wai tayi kyau fiye da ɗazun.
Hotuna suka cigaba da yi sannan suka koma yin videos abin gwanin birgewa.
Sun ɓata lokaci gun hotunan da videon sannan ya janyo ta jikinshi suka nufi falo suna ta murmushin nishaɗi. Tabbas sun cika amare masu son junansu.
Kan kujera suka zube ya dubeta da dukkan kulawa ya ce, "Princess me kike son ci na fita na nemo maki naga rana tayi amarya bata karya ba, duk ƙwazon da tai jiya gun bada darasi."
Sunne kanta tai, tana dariya ƙasa -ƙasa sai kuma tace, "Har ka tuna min da babbar kyautar da akai min kuwa a wajen ɗaukar darasin."
Miƙewa tsaye yake son yi don fita nema mata abin da zatai breakfast da shi, sai ta kama hannunsa ta nufi inda aka tsara don cin abinci ta zaunar da shi yana bin ta da kallo don bai fahimci komai ba.
Sai da ta buɗe naman ta zuba a filet ta zuba mai kunun a kofi ta zuba fanken ta tura gabanshi ta zagaya ta zauna kusa da shi tace, "Bisimillah Prince komai ya kammala kai kaɗai ake jira daman."
Kasa cewa komai yai sai ƙoƙarin tunanin lokacin datai girkin kawai yake, bai ankara ba ya ji saukar kofi a bakinsa ya buɗe ta zuba mai kunun. Lumshe idonsa ya yi jin wani garɗi da daɗi na musamman daya sauka akan halshensa, a hankali ta cigaba da ba shi a baki yana sha, ganin kamar bata sauri ga shi kunun ya yi mai daɗi sai ya amsa ya cigaba da sha da kansa yana haɗawa da fanken. Sai da ya shanye wanda ta saka mai duka sannan ya aje kofin ya fara ƙoƙarin zuba mata naman a baki don itama ta gama shan nata kunun.
Yana cin naman sau ɗaya ya kalle ta da alamar tambaya sai kuma ya ce, "Princess yaushe kika fita har ki kayo cefane ban sani ba?"
Dariya tai ta cire kallabinta ta saka a gefensa wai ita ala dole santi yake yi.
Sai da ya sake tambayar sannan ta gaya mai sauran na jiya ne ta gyara saboda ba kayan da take buƙata na girki a gidan.
Ya kalli jug ɗin kunun ya ce, "Shi kuma wancan fa ina kika samo shi ban taɓa shan irinsa ba ke ban ma san shi ba Ni sai Yau, don Allah dame ake yin shi?"
Ta fashe da dariya tace, "Da zallar so da ƙaunar Prince ɗina ake yinshi , ina fatan ya yi maka daɗi?"
Kiss ya manta mata a fuska ya ce, "Bayan daɗi ma har garɗi da birgeni ya yi don haka na gode sosai da wannan breakfast mai inganci dana samu bayan kyakkyawan darasin dana ɗauka."
Shiru tai ta ƙyale shi, domin bata san lokacin da Prince ya koma haka ba, shi da take hangen magana bata dame shi ba, a hangenta ma sai ta koya mai wasu abubuwan da dama ashe kar yake.
Sai da ya ji cikinsa na neman fashewa sannan ya haƙura ba don ya gaji da ci ba a bakinsa ba.
Falo suka dawo yana kwance cikin doguwar kujera ita kuma tana kwance jikinsa suna kallon hotunan da sukai ɗazun tana cewa yafi ta kyau yana cewa ta fishi kyau.
Suna cikin haka suka ji ana buga gidan, tashi tai ya miƙe tsaye ta nuna mai kumatunta alamar yai mata kiss kafin ya fita buɗe ƙofar, ya kuwa manna mata ita ma tai ma shi ya fice yana kallonta tana ɗaga mai hannu alamar bye-bye kamar wanda zai fice daga gidan baki ɗaya ba ƙofa kawai zai buɗe ba ya dawo.
Yana ficewa ta ruga ɗaki ta sake gyara fuskarta ta shafa jan bakin ta gyara ɗaurin kallabinta ta zauna tana jiran taji su waye suka zo.
Tana jin yana magana da yara sai ta fito, kayan alaci ne aka aiko daga gidan Yayarsa ta amshi kayan tana tambayar yaran ya Auntyn take, ta juye komai ta zuba masu cin cin da dubulan suka zauna suna ci ita kuma ta ja Prince suka shiga kicin ɗin don zubama Auntyn kayan bikin nata yaran su tafi da su.
Sai ya dinga ganin abin kamar a mafarkin daya saba yi na rayuwar da yake so suyi da Princess ɗinsa idan sun aure, nishaɗi suke su duka kowa cike yake da annashuwa har ta gama zuba komai yana cewa sun yawa tana cewa Auntynsa za a kai mawa ko tata? Dole ya ja bakinsa yai shiru don abin yafi ƙarfinsa.
Suna fitowa yaran sun gama ta basu kayan tace su gaida mata da Auntyn sosai.
Suna tafiya suka koma inda suke da ta jawo wayarta ta kira lambar Alawiyya kamar jira take daman ta kama kiran tana cewa, "Kaga amarya a gidan Mustapha bada kanki a sare ki je gida kice ya faɗi, tun ɗazun nake ɗaukar waya da zummar kiranki sai Abbansu Anam ya hanani ya ce yasan baku tashi ba, haka kawai zan matsa ma sabbin amare da kira."
Dariya ta saka tace, "Ya kyauta min kuwa, domin yanzu haka juyin farko ne mukai abinmu."
Alawiyya tace,"Ai fa abu ya zo ga ma'iya daman breakfast ɗin ku ne nace ya za ai kuna iya buɗe gidan yanzu a kawo maku koko sai anjima?"
Tai murmushi tace, "Aunty ta jima da kawo mana breakfast Madam ke dai kice kin kira ki ji gulma kawai to Prince da Princess na lafiya."
Wayarsa ce tai ƙara don haka ya ɗauka bai ma duba suna ba, sai ji ya yi ance, "Sai ka zo kaba yara kuɗin makaranta da kuɗin cefane?"
Murmushi ya yi don Maryam ce hatta Jiddah dake jikinshi tana waya tana jin yadda take magana cike da gatsali da fusata.
"Yanzu za a kawo, bari na kira waya, amma har cefanen jiya duk ya ƙare?"
"Ban sani ba, sai ka zo ka duba da kanka , kai dai ka ji haushin kanka kuma wallahi ka ji tsoron Allah tun yanzu ka fara mugun halin naka, to indai kai ne ai gata ga ka nan muna nan zamu ga yadda zata kaya."
Murmushi ya yi yana cigaba da wasa da kitson Jiddah ya ce, "Shike nan za a kawo maku komai."
"E daman kace haka man, ai Allah Ni ba zan juri wulaƙanci ba don taƙamar kayi wani auren banza can."
Kashe wayarsa ya yi kawai don yasan idan ba katinta ya ƙare ba, ba zata tsiyaya mai masifa ba, shi kam ko zaginsa za tai ba zai ji komai ba yanda yake tare da Princess ɗinsa matsayin matar aure .
Duk abin da tace mai tsab Jiddah ta ji sai tai kamar bata ji ba, suka cigaba da waya da Alawiyya.
Sallamar ƴan Jalingo ce tasa ta tashi daga jikinsa su kai sallama da Alawiyya ta fita waje ta tarbe su, shi kuma ya koma ɗaki.
Sun gaggaisa suna ta zare ido sunga gidan Jiddah kamar ba Nigeria ba, gida mai kyan gaske ya ji kayan alatun rayuwa komai akwai a gidan wani abun ma basu san ko miye ba.
Jiddah ta tarbesu da martaba ta kawo masu kayan abincin da Aunty ta aiko masu da shi, suna ci suna sunne kai domin baki ɗayansu ba wadda ta taɓa taka ƙafarta gidan auren Jiddah da Deeni.
Suna gamawa ta kwashe kayan ta kai kicin ta leƙa ɗakin tace mai ya fito ya gaisa da mutan Jalingo suyi bankwana za su koma gida Yau.
Tare suka jera suka fito yana riƙe da hannunta suka gaisa suna ta yi mai Allah sa alheri da fatan zaman lafiya, ya kawo kuɗi yaba Jiddah ya ce ta basu idan za su tafi zai ɗan fita ya je ya dawo.
Ta basu kuɗin sunata godiya tabi bayan shi yana tsaye yana kallon ƙofar ɗakin da tsammanin fitowarta .
Tana zuwa ya buɗe hannu ta faɗa ciki ya maida ya rufe suka dinga saukar da ajiyar zuciya.
A cikin kunnenta ya raɗa mata, "Zan fita Princess ba jimawa zan ba zan dawo, zan je nima nayi bankwana da waɗanda suka zo daga wasu garuruwan ƴan'uwan Mamana."
Cike da kulawa tace mai, "Allah Ya tsare min kai, Ya kiyaye min kai, Ya Kai ka lafiya Ya dawo min da kai lafiya Prince. Ina fatan zaka runtse Idonka daga kallon kowace mace, idan ma tsautsai yasa ka kalla kaga abin da ya birgeka a jikinta don Allah ka kira Ni a waya ko ka turomin message ka faɗa min ko miye kafin ka dawo na tanadar maka ko miye ma." Suka haɗe bakinsu waje guda suna kissing ɗin juna na tsawon lokaci, sannan ta zare jikinta tana sake maimaita mai addu'a yana amsawa da "Amin Princess, sai na dawo ki kulamin da kanki sosai don Allah ban da aiki ki kwanta ki huta har in dawo."
Murmushi tai tana sake ɗaga mai hannu har ya fice daga gidan.
Mutane da dama suka dinga shigowa ganin amarya da ɗakin amarya, amma ita hankalinta na kan wayarta da suke chat suna waya da Prince ɗinta yana gaya mata yadda yai kewarta itama tana gaya mai yadda tai tata kewar har tana cewa ta rame ita dai ya dawo gida haka nan ko ta saka mai kuka.
Jin hakan yasa ya ruɗe ya ce mata ga shi nan zuwa yanzu insha Allah yana hanya.
Ko da jin haka sai ta tashi da sauri ta shiga kicin kasancewar ta bada an siyo mata kayan miya da kifi ta ɗora taliya ta gama ta yi mai gurasa ta haɗa lemu mai daɗi ta saka a fridge sannan ta shiga wanka tana fitowa matan dake gidan suka ce za su tafi ta zuba masu kayan biki ta raka su ta rufe gidan da niyyar ba zata sake buɗe wa kowa ba sai Prince ɗinta.
Ƙananan kaya ta ɗauko masu kyau ta saka tai bala'in kyau a cikin kayan domin komai ya amsa sunansa a jikinta ya kuma bayyana ta fesa turare ta sake gyara ko'ina ta dawo kan kujera ta zauna ta kira shi a waya amma har wayar ta katse bai ɗauka ba, sai ta samu kanta da turawa mai saƙo.
"Idanuwana sun rufe, kunnuwana sun toshe, jikina ya yi yaushi miyan bakina ya ɗauke duk don rashin dawowar Prince gida da wuri, don Allah ka dawo gida ina son jinka kusa da Ni Prince cike nake da kewarka tunda ka fita."
Yana ta sauri yabar gun abokansa sun riƙe shi, ga shi hankalinsa na kan Princess ɗinsa, yana ganin kiran ya kasa amsawa ne saboda bai taho ba, sai dai ganin saƙon yasa ya miƙe tsaye duk da tsiyar da su Ɗangote ke mai ya nufi gidan.
Sai da ya shiga unguwar sannan ya tsaya ya kira ta, tana ɗauka ta fashe da kukan shagwaɓa. Baki ɗaya ya rikice ya kama lallashinta.
"Afuwan Princess ga Ni nan yanzu haka cikin unguwa ina hango ƙofar gidanma yanzu haka."
Cike da shagwaɓa tace, "Na kusa mutuwa saboda kewarka Prince don Allah ka dawo ina jiran ka ko abinci ban ci ba sai ka zo mu ci kuma fa yunwa nake ji sosai Ni ."
"Yanzu -yanzu za ki ganni Princess gaskiya ban kyauta ba ai min afuwa."
Mintina kaɗan ta ji shi yana buga gidan, sai da sake fesa turare sannan ta nufi ƙofar tana buɗe mai suka rungume juna tana sauke ajiyar zuciya ta tamkar wadda tai kuka da gasken-gaske.
Shi kuma ya dinga shafa bayanta yana sunsunar wuyanta a hankali yana raɗa mata kalaman ƙauna da yaba kwalliyar da tai.
Sannan ta ɗago tana murmushi ta sumbace shi ta sake shigewa jikinsa tana cewa "Oyoyo Prince, sannu da dawowa, Allah nayi kewarka sosai, shin ka manta da Ni ne yasa baka waigo gida ba tunda ka fita?"
Cike da farin cikin ganinta ya ce, "Haba Princess taya zan manta da ke bayan ke ce rayuwata baki ɗaya."
Cikin ɗaki suka nufa, kan kujera ya zauna ta ɗebo mai ruwa mai ɗan sanyi ta ba shi a baki ya sha, sannan ta fara jera mai sannu kamar wanda ya yi wani uban aiki.
Shi kam ji yake baki ɗaya duk wani burinsa ya gama cika tunda har ya mamaki Jiddah matsayin matarsa kuma ta kasance irin macen da yake so ciki da waje. Allah Sarki Salim ina ma ace kana raye da kaga yadda ƙanwarka ke sakani nishaɗi ta sakani cikin aminci da walwala yadda nake fata nake buri.
Sai da ta tabbatar da ya ɗan huta sannan ta ja hannunsa suka nufi inda ta haɗa kayan abincin.
Tunda suka doshi gun yake jin ƙamshin abincin har miyansa ya fara tsinkewa. Cikin natsuwa ta zaunar da shi ta fara zuba abincin tana jerawa gabansa shi kuma sai aikin kallonta kawai yake yana jiran ta gama ya fara tada saiti.
Kamar yadda ya zata dai, ita ta dinga ba shi abincin har zuwa lokacin da ya ji cikinsa ya fara nauyi sannan shima ya fara bata a baki.
Sai da ya ci mai ɗan dama daga gurasar har taliyar sannan ya ɗora da lemu mai sanyi suka koma kan kujera ta shige jikinsa ta fara karanta mai wani littafi da take karantawa yana sauraren ta.
Suna cikin karatun suka ji sallamar Bilkisu, ta amsa mata sallamar ta ɗan zame daga jikinsa ba tare da ta tashi baki ɗaya ba.
Bilkisu na shigowa tana cewa, "Mun zo mu ga gidan amarya wankakka da sabulu da mai... Tai shiru ganin Mustapha kwance cikin kujera Jiddah na kishingiɗe a rabin jikinsa. Tai baya da sauri wai irin abin nan maigida ya shige ɗaki ko ya fice anyi baƙi.
Jiddah tai murmushi tace, "Ban gane komawa ba, kina nufin baƙonki ne Prince ɗin ko me?" Daga can tsakar gidan Bilkisu ta saka dariya tana cewa, "Ke Ni ban san iskanci ce maki nai baƙona ne Mustaphan?" Sai ta sake dawowa cikin falon.
Shi dai ko kallo bata ishe shi ba, balle ya daina wasa da kitson Jiddah da yake, har sai da Bilkisun ta gaida shi sannan ya amsa yai mata kallo guda darajar yaron dake bayanta yana ma yaron wasa.
Ganin ta tukara a zaman wajen yasa Jiddah jan Prince cikin ɗakinta suka bar Bilkisun a nan. Suna shiga ya fara sunsunar wuyanta yana jan ta, so yake ya biye mai su bar Bilkisu a falo don haka ta samu da ƙyar ta lallaɓa shi ta fice gun Bilkisun.
Tana zaune sai kalle-kalle take tana jinjina kanta, Jiddar ta fita, suka kalli juna Jiddah tai murmushi ya yin da Bilkisun tace murya ƙasa -ƙasa "Amarya kin iya kama angoki tun jiya ake nemansa gidansa ba a ganshi ba har yanzu ashe yana nan ana shan madarar ƙauna ta shekaru da aka kwashe ana zabgawa."
Jiddah tai murmushi domin tuni Bilkisu ta fice mata a rai ta san dai gulma ce kawai ta kawo ta, don haka zata yi iyakar yinta ta bar gidan shike nan.
Abinci ta zubo mata da kayan biki ta zauna sai dai sam ta kasa sakin jiki da Bilkisun domin ta san cewar Bilkisu ƙawar Maryam ce don haka dole ta kiyaye abubuwa da dama idan tana son kare kanta daga sabgar tsegumi da gulmace-gulmace irin na Bilkisun.
"Shegiya ƙawata sai da kika dai aure Prince ɗin nan hankalinki ya kwanta, kin zo daga sama kin ƙwace ma mata miji sai yadda ki kai da shi, naji ana cewa bayan lefen da ya yi maki har wasu kuɗi ya baki wai kiyi siyayyar abin da baki da shi ko?" Ta idasa maganar tana kallon kayan dake tsaune a falon masu matuƙar tsada.
Jiddah ta dubeta sai kuma tai dariya tace, "Ai ke dai bari kawai ko da yaushe cikin yi wa Allah godiya nake daya azurtani da miji irin Prince ban san wane irin farin ciki yake ban ba domin abin yafi kwatance balle misali, ai shi komai nashi nawa ne daman don haka kar ki yi mamakin komai aka ce ya yi min zai iya don yana ƙaunata kamar yadda nake ƙaunarsa."
Muƙut, Bilkisu ta haɗe miyau ta miƙe tsaye"To Jiddah ni zan tafi sai anjima Allah Ya bada zaman lafiya Yasa a jima tare."
Jiddah ta gyara zamanta sosai alamar ba zata iya ko rakata ba tace, "Amin Ya Allah zama kam ai mun fara kenan ba maganar tafiya ko rashin ƙarko."
Bayan tafiyar Bilkisu ba jimawa Prince ya fito zai tafi Jiddah ta raka shi tana shagwaɓar kar da ya jima ya dawo da wuri ita dai.
Gidansa kai tsaye ya nufa fuskarsa fal fara'a da farin ciki ba alamar damuwa ko kaɗan a tare da shi.
Matan gidan na ɗaki kowace tana jin yana sallama amma ba wadda ta samu ikon amsa mai sallamar balle a leƙo ai mai tarba ta musamman.
Ya bi yaran duka yai masu magana kana ya buɗe ɗakinsa ya shige yana jin kewar Jiddah fal a ransa, da ace gidanta ne ya je da yanzu tana jikinsa tana masa sannu da zuwa ta ba shi lemu ko ruwa mai sanyi tana shagwaɓa tana ba shi har sai ya ƙoshi ta ja shi zuwa toilet tai mai wanka ta tsane mai jiki tai mai shafa ta fesa mai turare.
Kan gadonsa ya faɗa yana hasko jiya zuwa Yau kawai irin nau'in ni'imar da ya kwasa gun Jiddar...
"To marar adalci, wanda bai san Annabi Ya faku ba, ashe kai ka sai mata kayan ɗakin da nake jin ana cewa sun yi kyau? To wallahi Allah Ya Isa kuma sai ka ban nawa haƙƙin dole tunda ba tsoron wani nake ba."
Hafsat ce tsaye kansa take ta masifa ta ji ana maganar shi ya saima Jiddah komai na ɗakinta.
Ko kallo bata ishe shi ba, saboda ba ta ita yake ba, shi baki ɗaya hankalinsa yana kan Jiddah jin ƙamshin turaren ta yake a hancinsa, hasko yadda take lafewa jikinsa kawai yake a idonsa tana wasa da gemunsa ko maɓallan gaban rigarsa, ko kuma ta dinga jan hancinsa tana cewa yafi nata bata yadda sai sun yi musaya. (Irin abin da matanmu su kai sake kenan yanzu, baki iya shigewa jikin mijinki ki yi duk wani kalar karuwancin da zai birgeshi ki koma ƙaramar yarinya a gunsa ki dinga wasa da abubuwa da dama na jikinsa kina yaba kyansa kina ƙarawa hakan ba ƙaramin so da shaƙuwa yake ƙarawa ba sannan ko baki nan zai dinga tunawa dake komai yake kina cikin ransa zai dinga sauri duk inda ya je don kawai ya dawo gunki ki dinga saka shi nishaɗi.)
Ganin ya ƙi kula ta yasa ta fara zage-zage, sai alokacin hankalinsa ya dawo kanta, ya nuna mata ƙofa ta bar mai ɗaki, amma kamar ya sake tunzura ta ma sai ta cigaba da zagin tana kiran shi mugu azzalumi wanda bai san adalci ba, hakan yasa ya miƙe da nufin yabar mata ɗakin sai ta sha gabansa ta ci gaba da aibata shi son ranta, ganin zata fusata shi yasa ya ture ta ya bar ɗakin ranshi a ɓace.
Yana fita itama ta fice kai tsaye kayanta ta haɗa ta bar gidan, yana zaune cikin abokansa sai ga kira daga surukarsa akan ya sakar mata yarinya ko ya ji kira daga kotu.
Shi daman yasan duk abin da Hafsat ke yi mai da taimakon mahaifiyarta sam ba tai na'am da shi matsayin suruki ba duk irin ƙaunar da yake ma Hafsat a banza bata gani sam, ita burinta ko da yaushe ya sakar mata yarinya shi kuma yana son matarsa don haka ma yake kauda kai daga duk wani iskanci da rainin hankali da Hafsat ke yi mai a zamansu.
Duk lokacin da tai yaji bai natsuwa sai ya maidota ba don komai ba sai don shi da gaske yake son ta yana son zama da ita musamman da suka fara tara yara da ita, da farko bata biyewa mahaifiyarta amma daga baya sai ta ɗauki duk wasu shawarwari da uwar ke bata.
Hankalinsa baki ɗaya ya tashi don shi mutum ne da bai san damuwa ko tashin hankali don haka ya dawo gidan ya shige ɗakinsa ya rasa abin da ke masa daɗi sam.
.
Sai ga Maryam ita ma ta shigo ranta ɓace tai tsaye tana ƙare mai kallo cike da takaici tace, "Wallahi ka ji kunya, kuma insha Allah sai ka ga abin da kai ya dawo kanka. Shi ne tsabar rashin adalci ka koma ka tare jikin mace kana mata hidima ka bar mu nan ba komai sai kace ba aurenmu kake ba."
Baki ɗaya so suke su saka shi ciwon kai, ko da yake har yaushe ma tun kiran wayar Maman Hafsat kan shi ke ciwo ita ma gata ta zo da nata rashin mutuncin.
Jiddah sai kiransa take ya ƙi ɗagawa ta turo saƙo fiye da biyar shima sai dai ya buɗe ya aje wayar kawai bai san me zai ce mata ba.
Ita ma Maryam haka ta ƙare nata rashin mutuncin bai tanka mata ba, saboda bai san itama ta nufi nasu gidan ace kuma ya kora su daga yin aurensa.
Da ƙyar ya je sallar magrib yana fitowa sai ga Yayan Hafsat gabansa ya tabbatar mai da cewa ya ba ƙanwarsa takarda don ba zata koma gidansa ba aurensu ya ƙare.
Duk lokacin da aka ce aurensu ya ƙare sai ya ji kamar an caka mai mashi a ƙahon zuciya yake ji.
Shi fa yana son matarsa yana son zama da ita don haka ba zai sake ta ba duk yadda za ai ba zai basu takarda ba.
Har dare bai san ya zai ba, ga Jiddah ta dame shi da kida da turo saƙo shi kuma ko guda ya kasa maida mata amsar saƙonta balle ya ɗaga kiran da take mai.
A daddafe ya je gun abokinsa Ali Ɗangote ya ce ya raka shi gidansu Hafsat ɗin ya basu haƙuri ta dawo gidansa don ba zai iya sakinta ba yana son zama da ita.
Suna zuwa aka bar su zaune falon gidan ko yaro ba wanda ya leƙa suka gaisa har wajen awa guda don har Alin ya gaji ya ce ya tashi su tafi amma ya ce shi sam ba inda zai je sai sun fito ya basu haƙuri ya kuma gaya masu gaskiya kan abin da taji ƙarya ne ba gaskiya ba.
Bayan uban zaman da su kai ne sai ga Mamarta ta fito a fusace ta zauna ko gaisuwar da suke mata bata samu damar amsawa ba sai tambayar ina takardar yarinyata da ta jefa mai.
Kanshi a ƙasa cike da ladabi ya ce, "Mama don Allah ku yi haƙuri wallahi ba haka bane ba, taya za a ce Ni nayi wa Jiddah kayan ɗaki? Ba Ni nayi mata ba Allah kuwa Mama duk sharrin mutane ne da son ganin an yi tashin hankali kawai a tsakaninmu."
Baki ta taɓe ta kira Hafsat ɗin da ƙarfi, sai ga ta, ko kallon inda yake ba tai ba, ta samu waje ta zauna kawai tana kallon Mamar.
"Wai kin ji ya ce ba shi ya yi mata kayan ba." Cewar Mamar Hafsat kenan tana watsawa Hafsat ɗin harara.
Kwance take kan gado ta rufe idonta tana jin saukar hawaye a idanunta amma sam bata damu ba, babban burinta shi ne meke faruwa da Prince ne haka? Tunda ya fice take kiransa bai ɗauka ba, ta tura mai saƙo ba amsa anya kuwa lafiya yake? Gabanta ya sake faɗuwa ta sake ɗaukar wayar ta kira lambarsa sai kawai ta ji ya kashe wayar.
Zaune ta tashi ta dafe ƙirjinta dake bugawa, tabbas ta fahimta kawai bai san kiran da take mai ne, tunda ya kashe kiran yanzu alama ce ta duk saƙo da kiran da take turawa duk yana gani bai da lokacinta ne kawai.
A hankali ta fara zagayen ɗakin domin tunanin ko abin da tai mai kafin ya fita ko kuma daga zuwanta gidan zuwa yanzu? Tas ta tuna komai, ita dai bata ga abin da tai mai ba, tana ƙoƙarin inganta zamansu ta hanyar kulawa da ba shi duk wani haƙƙinsa to a ina ta rago shi ne ? Me yasa ya zaɓi ranakun cin amarcinta ne ranar da zai fara yi mata sauyin yanayi? Ko dai bai same ta a yadda yake son mace ba? Ma'ana ko dai ita ɗin bata gamsar da shi bane ba? Tabbas ba zata ce ya daina son ta ba amma dole akwai abin da ke faruwa ko ya faru a tsakaninsu, sai dai bai kamata ba koma miye ba ace ya ɗauke shi da zafi haka ba, ya manta duk irin alƙawarin da sukai ma juna ne? Ya manta shi ne cikar farin cikinta ne? Ya manta nan shi ne aljannarta ta duniya sai ya buɗa mata zata ji daɗinta? Kuka take sosai tana zagaye ɗakin tana kiran wayar yana katse kiran.
Ganin har dare ya yi bai dawo ba kuma bai amsa kiranta ba haka zalika bai turo mata saƙo ba ko da na hujjar katse mata kira da yake sai ta samu a hankali tai wanka tai sallah ta jawo Alkur'ani ta ci-gaba da karantawa idanunta na zubar hawaye.
Ta jima tana karatun sannan ta aje ta koma falo ta lafe cikin kujera abar tausayi ta fara tunanin. Dama haka Allah Ya ƙaddara mata rayuwar aure cikin matsala da damuwa ita kenan a rayuwarta? Kenan ba za ta dai ji daɗin rayuwar aure yadda take so ba kenan? Me yasa Prince zai mata haka tun yanzu? Me yasa ya kasa riƙe ko da alƙawarin sati ne kafin ya bayyana mata waye shi? Cikin muryar kuka take cewa, "Ya Allah kaga halin da nake ciki, ina neman ɗauki daga gareka, ina neman rangwame daga gunka, Ya Allah ka azurta zuciyar mijina da adalci ka wadata shi da halayen kirki kai mai sadakar karamci ka ba shi ikon zama da mu cikin aminci ka ƙara mai buɗin alheri kasa ya gama lafiya." Kuka take tana nanata addu'ar a bakinta har zuwa ƙarfe goma na dare ba Prince ba labarinsa don haka sai kawai ta takure a cikin kujerar tai lamo.
Ba yadda bai ba kan tai haƙuri amma Hafsat tai biris tace ita fa ko zata koma to sai ya bata wani abu tai gyare-gyaren ɗakinta, duk da cewar ya basu nasu kason don su yi gyaran amma haka ya sake bata wasu masu dama har ma da Mamarta sannan suka tafi yana ƙara neman alfarmar ta koma gidan washegari tunda tace ba zata bi shi ba yanzu, sai kuma ta taɓe baki tace "Idan ka zo gobe ƙarfe shida na safe mu tafi idan baka zo ba zan yi tafiya ta garinsu Mama na huta." Ta kwashe kuɗaɗen ta shige ɗaki ita da Mamar suka bar su nan zaune.
Zuwa lokacin karfe sha ɗaya na dare don haka Ali Ɗangote ya gama fusata ko magana bai iya yi mai ba, kawai gidansa ya kai shi ya wuce na shi gidan.
Yana turawa gidan ya buɗe ya yi mamaki, domin ya ɗauka ta rufe gidan, amma sai ya ganshi a buɗe duk da daren da ya yi.
Tana kwance falo ya wuce ta ko kallonta bai ba, kai tsaye ɗakinsa ya nufa don bai san magana ko da yake bai san me zai ce mata bama idan tai mai maganar don haka ya zaɓi shigewa ɗakinsa ya rufe kawai ya kwanta.
Kiran Hafsat ne ya shigo wayarsa da sauri ya ɗauka don jin me ya faru kuma.
"Har ka isa gidan?" Tace cikin muryar ko in kula.
"E na isa harma na kwanta yanzu haka." Ya amsa mata da muryar ban tausayi.
"Ni dai na gayama goben idan baka zo da wuri ba Allah sai dai ka iske yaranka na ƙara gaba Ni." Tace cike da gatsali
"Zan zo fa, Allah zan zo tun kafin lokacin ma ba wasa nake ba, kin san dai ina sonki ban iya rabuwa dake koma me zai faru."
Ji tai jikinta bai iya ɗaukarta, saboda tun da ya shigo ƙamshin turarensa yasa ta buɗe idonta sai dai ganin fuskarsa ba alamar fara'a yasa ta kasa tashi ta tarbeshi ta bari ya shiga ɗakin sai ta bishi don jin damuwarsa, ganin ya nufi ɗakinsa kai tsaye bai shiga nata ɗakin ba ta sake jin ba daɗi sosai amma sai ta tashi ta nufi ɗakin don ta ji me tai mai Yau ya sauya baki ɗaya? Sai dai jin yana waya da mace kuma taji me yake cewa yasa ta fahimci cewar ba ta ita yake ba don haka ta ja ƙofar don ta shiga ta ji ko da akwai abin da yake buƙata.
Sai dai kuma ɗakin a rufe yake alamar bai son ta shigar mai ɗaki bai buƙatar ta kusa da shi kenan, don haka ta ja jikinta cike da damuwa ta koma kan kujerar tana hawaye.
Ganin har sha biyun dare bai fito ba sai kawai ta koma tai alwala ta cigaba da jera sallah har sai da taji bata iya buɗe idonta sai kawai ta takure cikin hijabin tai barci a ƙasa tana saukar da ajiyar zuciya lokaci zuwa lokaci.
Sai wajen ƙarfe biyun dare suka gama wayar duk da tsogumi da kashedi yafi yawa a wayar tare da jan kunne duk dai tai mai wanda duk ya ji ya amsa ya amince zai gyara mata duk wasu kura-kuran da take cewa ya yi mata a gidan na shi.
Sai da suka gama wayar sannan hankalinsa ya dawo jikinsa ya dinga jin bai jin daɗin kwanciyar , sai yake jin kamar ya rasa wani abu a tare da shi, sai juyi yake ya kasa barci ya kuma rasa me ke damunsa don haka sai ya miƙe tsaye ya fice zuwa falo ko ruwa ya sha ya ji sauƙin zuciyarsa.
Buɗe ya ga ɗakinta ko haske bata kashe ba, kai tsaye sai ya nufi ɗakin don ganin me ya hanata barci har zuwa yanzu ita kuma.
Bata kan gadon har ya ɗauka tana toilet sai ya hango ta can ƙasa a takure bisa abin sallah sai ajiyar zuciya take alamar taci kuka ba ɗan ƙarami ba.
Wutar kawai ya kashe mata ya fice ya ja mata ɗakin yana jin bai kyauta mata ba, amma hakan shi ne daidai ya kamata ya yi mata idan ya kula ta tabbas gobe ba zata bar shi ya fice kan lokaci ba zuwa gidansu Hafsat ba.
Ita kam Hafsat dama don ta ba Jiddah haushi yasa tace mai ya zo da sassafe saboda an ce mata jiya sai wajen azahar ya fito daga gidan nasa shi da tsiya ga ango to zata ga ta yadda za ai angonci indai ita ce Hafsat sai ta ga abin da ya turewa Buzu naɗi, za tai ta buga shi har sai ya gama buguwa sannan zata koma idan taga dama idan kuwa bata ga dama ba zata tsaya tsayin daka sai ya sake ta.
Tunda asuba Jiddah ta tashi tai sallah ta nufi kicin ta fara haɗa breakfast don taji ya ce zai fita da wuri don haka zata haɗa komai da wuri bata son ya fita bai ci komai ba.
Cikin sauri ta haɗa simple breakfast ta jera ta shiga ɗakin cikin sanyin jiki ta gaida shi ya amsa ba tare da ya bari sun haɗa ido ba, ta maida hawayen dake son zubo mata tace, "Don Allah ka daure kai breakfast kafin ka fita na gama haɗa maka komai."
Bai ce komai ba yana ta ƙoƙarin fesa turare sai da zai fice ya ce, "Ki aje min idan na dawo zan yi." Ya zo ta gabanta ya raɓa ta zai wuce, kamar ta ƙyale shi sai kuma ta ga rashin dacewar hakan don haka ta jawo shi ta baya ta shige jikinsa tana cewa cikin raunanniyar murya, "Idan laifi nayi maka ina baka haƙuri kuma ina neman alfarmar ka gayamin domin na gyara kuskurena, idan kuma ba laifina bane na wani ne ya shafe Ni ina maka addu'ar Allah Ya sassauta mata zuciyarka Ya tsare min kai Ya kiyaye min kai daga dukkan sharri da abin sharri Prince, sai ka dawo ka kula da kanka, idan ka jima ka samu wani abun ko a can ne inda zaka ka ci domin ban san kana zama da yunwa don Allah." Ta janye jikinta daga nashi ta shige cikin toilet ɗin ɗakin saboda bata son ya ji sautin kukanta.
Sanyi ƙalau ya ja jikinsa ya fice ya kasa aiyana ko da kalma guda a zuciyarsa.
Yana zuwa ƙofar gidan ya kira ta cikin barci ta amsa wayar tace ya jira ta zo ta buɗe mai gidan.
Wayarsa tai ƙara alamar saƙo ne ya shigo ya buɗe don ganin waye.
"Dare da rana, safe da yamma ban tunanin akwai lokaci ko rana da zata zo wadda zan gaza fahimtar Prince ɗina balle na kasa yi mai uzuri kan dukkan abin da ya shafe shi, ina maka fatan alheri tare da addu'ar dacewa da abin da kake nema koma miye. Ka kula da kanka sosai don Allah ka ci abinci kan lokaci ina matuƙar kewarka Prince ɗina, zuciyata sai ƙara ƙaunarka take duk bayan sa'a guda.
Sai ka dawo farin cikina abin alfaharina, daga taka Princess ɗin ka."
Ba don jingine yake jikin bango ba da sai ya faɗi yadda ya ji jikinsa ya yi wani sakau kamar ba nashi ba.
Princess kenan tana danne duk wani damuwa da takaicinta ta saka shi cikin nishaɗi ba ruwanta da yadda ya sauya daga jiya zuwa ya kasa bata kulawa ya kasa yi mata ko da rabin abin da take mai, to ya zai yi? Yana sonta kuma yana son matarsa Hafsat kowace da wajenta dole ne hankalinsa ya koma kan Hafsat don ba zai gangancin rabuwa da ita ba saboda yana sonta a duk yadda take.
Maida wayar ya yi a aljihu ba tare da ko kalma guda ya maida mata ba. Ya kusa awa guda a tsaye sannan ƙanin Hafsat ɗin ya zo ya buɗe mai ƙofar gidan ya ce, "An ce ya shiga ciki."
Ko da ya shiga ya ɗauka zai iske ta zaune ta shirya tana jiransa kamar yadda su kai jiya sai dai wayam ba kowa falon don haka sai ya samu waje ya zauna yana tunanin tana shiryawa ne.
Sai dai ko ɗaya Hafsat na kwance abinta barci ma ta koma bayan ta tabbatar da zuwan nasa, sai ta koma barci don dama ta faɗa ne kawai don ta saka ƙunci da takaici a tsakaninsa da amaryar tasa ba komawa za tai ba gidansa Yau ba.
Bawan Allah yana zaune har takwas tayi sannan Mamar ta fito suka gaisa take shaida mai ai Hafsat ɗin barci take saboda kanta nayi mata ciwo tun da asubar fari.
Cike da damuwa yake tambayar ta sha magani ? Ta dube shi tace, "Wane magani zata sha bayan bata ci komai ba?"
Ya karkace ya fito da kuɗi ya kira yaron daya buɗe mai ƙofar gidan ya ce, ya je ya haɗo kayan breakfast ɗin.
Ta tashi ta shige ɗaki ta bar shi nan zaune yana son shiga ɗakin da Hafsat ɗin ke kwance yana jin kunyar Mamar duk da ba ɗaki guda suke da Hafsat ɗin ba, sai ya fito da wayarsa ya kira layinta sai da ya yi kira biyar sannan ta ɗaga tana tambayarsa lafiya?
Cike da kulawa yake tambayarta ya kan ya daina ciwo?
Cikin halin ko in kula tace, "Ba wani serious ciwo yake ba, kawai wayar da mu kai ne jiya yasa kaina ciwon kuma ya daina ina hutawa ne yanzu."
"To ki ɗan fito mu gaisa man naga yadda kika kwana." Ya ce cikin muryar ban tausayi.
Ta ɗan ja tsaki tace, "Ka jira na gama abin da nake ai fitowa zan dama ba sai ka ce ba, tun da ba cikin ɗakin zan dawwama ba."
"To shike nan sai kin fito ina nan dai ina jiranki idan kin gama ɗin."
Ƙala bata ce mai ta kashe wayarta ta gyara kwanciyarta tana murmushin mugunta.
Duk da ta haɗa komai ta gyara komai tai wanka amma ta kasa kai ko da ruwa bakinta, ita kaɗai tasan yadda take ji, ita kaɗai tasan yadda zuciyarta ke kuka idanunta hawaye kawai suke amma ciwon danƙare yake a cikin zuciya da ruhina.
Wace irin rashin sa'ar rayuwa gareta ta fannin zaman aure ne? Haka fa tai rayuwa gidan Deeni cike da yaƙinin zata yi duk yadda zatai don kawai su rayu cikin farin ciki amma hakan ya faskara samuwa, anya kuwa ba a jininta abin yake ba? Me yasa a waje kawai take farin ciki banda gidan aurenta ? Kuka take sosai tana girgiza kanta cike da karayar zuciya.
Wace irin jarabta ce wannan ke bibiyarta? Daga aure da kwana guda har miji ya juya mata baya ya manta duk irin soyayyar da suke ma juna, ya manta duk alƙawarin da su kai ma juna? Cikin kwana guda har ya manta shi? Ina duk mafarkan nashi suke? Ina soyayyar da yake iƙirarin zasu yi ma junansu? A haka ne yake cewa yana son rayuwar soyayya da farin ciki a rayuwarsa ta aure? Me yasa kai min haka Prince? Me yasa? Me yasa Prince?" Kuka take gwanin tausayi ita kaɗai ba mai lallashinta balle ya bata haƙuri ko amsar tambayoyinta.
Hotunansu dake zagaye da falon take kallo idanunta na zubar hawaye tana ƙara kallon fuskar Prince ɗinta tana raya abubuwan da suka wuce a tsakaninsu masu daɗi na cikin kwana guda kacal.
Wayarta ce tai ƙara don haka ta amsa cike da son ɓoye damuwarta, "Amarya Allah Yasa ba mu yi maku kutse ba, don ga Ni a ƙofar gidanku na zo yi maki bankwana zan je Katsina kan wani case." Cewar Alawiyya kenan tana dariya.
Bata so zuwan Alawiyya a yadda take ba, amma ya zatai, dole ta ce gata nan , ta shiga ta gyara fuskarta don kar da taga alamar tai kuka ta fice don zuwa buɗe mata gidan.
Cike da fara'a Alawiyya ta kai mata runguma sai kuma ta sake ta, ta ɗan ja da baya ta ƙura mata ido, hakan yasa Jiddah tai saurin kauda kanta tana dariya ta ja hannunta suka koma cikin gidan.
Jikin Alawiyya ya yi sanyi ƙalau tasan akwai matsala kallo guda tai ma Jiddah ta fahimci ta ci kuka ba mamaki ma ko kukan ta kwana yi, nan da nan ranta ya ɓaci ta haɗe ranta tamau ta ja tunga ƙofar ɗakin tana cewa, "Ke ba shiga zan ba maigidan na ciki zan afka mai ɗaki da asubar fari?"
Abin da ta guda dai ya faru, Alawiyya ko tace Barista Alawiyya Bello Gareji ta ɗora alamar tambaya kan ta da mijinta wanda hakan babban ƙalubale ne a tare da ita, ace kwana biyu kacal da aure har ta fuskanci matsalar da ƙawar tata zata ji nadama ko takaicin auren nata bayan tayi mata abubuwa da dama , har yaushe ne zata zama jaruma kamar ƙawarta itama ta jama jaruma a gidan aurenta ta dinga magance damuwarta ba tare da ta sani ba balle taji ɓacin rai ? Me zai sa tai saken da ƙawarta zata yi tofin alatsine ga auren da kwana biyu ne kawai da kafuwar sa?
Don haka ta dube ta cike da yaƙe tace, "Shi ai bai kwana gidan ba asibiti ya kwana ciwon ciki ya taso mai cikin dare kamar zai mutu." Hawaye suka zubo mata.
Alawiyya tai saurin dafa ta, "Ayyah! Ko da naji nasan dama da akwai abin da ke damunki da ganinki kin sha kuka , amma Jiddah ba sai ki kira Ni ki gayamin ba, don Allah sai ki zauna ke kaɗai cikin gida kita kuka? Mu je ki yi wanka sai mu je asibitin mu ga ya kwana to."
Cike da ruɗanin cikin zuciya tace, "Ai yanzu na dawo ƙaninsa ke gunsa mata basu zama suka ce wai a ba shi lokaci ba su san ana takura mai shi ma ƙaninsa ba ɗakin yake ba sunce ya zauna ne kawai don kar a ce ba kowa gunsa."
"Shike nan to, amma don Allah ki cire damuwa ki aje gefe ki dinga yi mai addu'a insha Allah zai samu sauƙi." Cewar Alawiyya.
Ta ɗan ji sanyi ganin Alawiyyar ta yadda da ƙaryar data shirga mata.
Alawiyyar ta matsa mata ta sha tea haka nan, da har ta ce ta fasa zuwa Katsinar sai da Jiddah tace ta tafi kawai ba komai ita ma gidansu Prince Mamarsa tace ta je ta zauna kar ta zauna ita kaɗai kewa ta dame ta ba kowa.
Sannan Alawiyyar ta amince ta wuce tana ƙara bata haƙuri tana lallashinta don tasan yadda Jiddah ke ƙaunar Prince shima Prince ɗin haka yake ƙaunar Jiddar ba ƙaramin abu bane guda ya kwanta ciwo ba gudan ya samu natsuwa ba.
Haka dai ta tafi tana ƙara bata haƙuri.
Jiddah na samu Alawiyyar ta tafi ta rufe gidan ta koma ɗaki da gudu ta fashe da kukan takaici wai ita ce ke ƙarya.
Agogo ta kalla ƙarfe sha biyu na rana kamar ta tashi ta haɗa mai abincin rana sai kuma ta ga kar ai ta asarar abincin don bai ci na daren jiya ba ga na safen Yau duk bai ci ba sai kawai ta sake gyara gidan ta lafe cikin kujera ta kunna waƙar soyayya tana ji hawaye na kwaranyowa daga idanunta na tausayin kanta da kanta.
Can kuma ta ɗauki waya ta kira layin Prince ɗin.
A daidai lokacin yana zaune gaban Hafsat ɗin yana ta faman bata baki kan ta tashi su tafi gida don Allah kuma duk abin da take so zai mata shi tun a kan hanya ma, wayarsa tai ƙara ko bai duba ba yasan Jiddah ce don kiɗanta daban haka hotonsu ne a jikin lambarta don haka ya katse kiran kawai , wani kiran ya sake shigowa ya sake katsewa yana tsaki alamar kiran na takura mai, a kira na uku ne ya ɗaga a fusace ya ce, "Wai ke baki san idan kin kira mutum a waya ba ya katse kiran ki haƙura ba?" Sai kawai ya kashe wayar.
Hafsat tai murmushi a ƙasan ranta tana cewa kaɗan kika gani ma yarinya.
Jiddah kuwa jin abin da ya ce yasa kanta ya sara nan da nan ta fara ganin juwa falon na juyawa da ita sai kawai ta runtse idonta tana jiyo amon muryar Prince ɗinta cikin fusata yana gaya mata magana.
Tun yanzu an fara kenan? To mu je dai mu gani shin ya zata kaya kenan? Hafsat ta murza nata kambun kwana guda da zuwan Jiddah gidan Mustapha ko ya kenan idan itama Maryam ta murza nata kambun?
Ta ya Jiddah zata samo bakin zaren kenan ?
To duk ku biyo Haupha don jin yadda zata kaya a tsakanin wannan kishi na mata uku.
Taku a kullum Haupha ✍️