WATA U NGUWA: Fita Ta 24

WATA U NGUWA: Fita Ta 24

BABI NA ASHIRIN DA HUƊU

 

"Shi kenan na shigangaɗi yau na san sai na fi gyaɗa markaɗuwa a gidan nan ka cuce ni Alhaji Saminu."

Ta faɗa tare da ɗora hannu a kai, tana ja da baya.

 

Baba ya ƙaraso hannunsa ɗauke da bulalar wayar wuta ya shiga tsula mata ita.

"Hanifah tun muna shaida juna ki faɗa mini uban da ya yi miki wannaan aika-aikar."

 

Ta kasa yin magana sai ihu take yi, ƙarajinta duk ya cika gidan har ya janyo hankalin makwafta na kusa suka fara zagayowa don ganin meke faruwa, sai dai ashe Baba Mudi ya riga ya rufe ƙofar gidan daga ciki don haka ba su samu damar ƙarasowa ciki ba.

 

Ruwan ƙanƙara ya jiƙa cike da ƙaramin bokitin roba su yake ɗiba yana watsa mata sannan sai ya dake ta da bulalar hannunsa.

 

Kamar yadda kowa ya sani bulala tafi azaba a lokacin sanyi, duk kuwa da cewa a lokacin sanyi ya ɗan ja baya amma haka ya ci gaba da azabtarshe ta da ruwan ƙanƙarar yana maimaita tambayarsa.

"Na ce uban waye ya miki wannan cikin?" Ya faɗa da ɗaga murya.

 

Duk da cewa Inna da sauran yaran gidan yan mata duk suna nan, amma an kasa samun mai cetonta kowa ya sha jinin jikinsa sai kallon tausayi da suke Binta da shi.

 

Da ƙyar ta buɗi baki ta ce "Alhaji Saminu ne."

 

"Wace unguwa mutumin banzar yake? Ko da yake kira shi a waya kice ina nemansa. Don kuwa dole ne sai ya aure ki." Ya sauke yana huci tare da kafe ta da ido.

 

Tana ɗagowa suka haɗa ido jiki na kakkarwa ta miƙe ta je ta dauko wayarta a ɗaki ta tsaya ta kira shi.

 

Yana ɗagawa ta fara magana cikin sanyi a ƙoƙarinta na ɓoye damuwarta "Alhajina don Allah ka zo gidanmu da gaggawa ina nemanka."

 

"Meke faruwa ne sweet Hanee? Ko jikin ne ya motsa."

Zancensa na ƙarshe ya haska mata irin ƙaryar da ta dace ta yi don haka ta ce "Eh, ina cikin matsala zan mutu...."

 

"Ke fa nake jira, ko Ni sa'arki ne da zaki shanya ni?" Muryar Baba ta kawowa kunnenta ziyara dalili kenan da ya saka ta yi saurin kashe wayar tare da fita jikinta na rawa kamar an kaɗa mazari.

 

"Bab.... Baba na kira shi yanzu zai zo." Ta faɗa a ranta kuma tana addu'ar Allah Ya Sa ya zo, domin bata da tabbacin hakan.

 

Bayan zuwansa ya yi sallama Baba ya fita yana cika da matsewa tamkar kwaɗon da ran shi ya ɓaci. Yana yin tozali da shi ya ce "Kai ne Alhaji Saminu?"

Ya gyaɗa kai alamar eh cikin mamakin wannan dattijon.

Eh Ni ne sannu da fitowa."

Ya mika masa hannu da nufin gaisuwa.

Tamkar wanda aka miƙowa ice mai ci da wuta haka baba ya yi saurin janye hannunsa yana faɗar

"Na saka ta kira ka ne don na shaida maka cewar ka turo a neman maka aurenta cikin kwanakin nan a rufawa juna asiri."

 

A razane ya ɗago idanunsa masu kama da curin ƙuli ya ce "Ban gane ba? Wai Ni ne zan auri Hanifah?"

 

"Ƙwarai kuwa, kai ka dace da aurenta."

 

"Allah Ya sawwaƙe ba da Ni ba gada a hurumi, auren kilaki cab."

Baba Mudi kuwa duk da yawan aibata ya'yan nasa da yake da yi musu ba ki, jin wannan kalmar ta baƙanta masa rai tare da fusata shi.

 

"Idan baka aure ta ba wa zai kula maka da wancan shegen cikin naka?"

 

"Ciki kuma?" Ya faɗa a ɗan razane sannan ya ɗora "Ta dai faɗa maku inda ta samo abinta to ko da yake abu ga motar haya taya za'a iya ganewa."

 

Ya faɗa yana yar dariya, baba ya ɗaga murya ya kira Hanifah, tana fitowa ya nuna mata Alhaji Saminu da hannu "Ba wannan ba ne?"

 

Suna haɗa ido da shi ya maka mata wata uwar harara tare da kallon tsana ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa tana faɗin "Shi ne."

 

"To kin ji ya ce ba na shi ba ne? Gidan uban wa kika samo?."

 

"Wallahil azim shi ne Baba bana kula kowa sai shi."

 

"Karya kike munafuka, Ni dai kike son jajiɓawa don kici arziki ko da yake ance inda fata tafi taushi can ake mayar da jima. Ni kin ga tafiya ta daga yau kada ki ƙara nuna kin Sanni ko da a hanya muka gamu."

 

"Zaka ga abin da zan maka maci kawai." Baba ya faɗa.

 

Alhaji ya bushe da dariya ya ce "Akan wannan kucakar  yar taka kake faɗa mini haka? Kasan kuwa Ni waye? Kai baka da kuɗin da zaka yi Shari'a da ni, sannan ina son ka ƙara sani ba Ni da alaƙa da wannan shegen jikan naka, idan ka sake ka taro faɗa da Ni zan iya ɓatar daku baki ɗaya ma."

 

Yana gama faɗa ya karkade babbar rigarsa ya yi gaba.

 

Nan fa Hanee ta yi mutuwar tsaye rana ta mamakin yadda Alhajinta ya juya mata baya saboda wannan ƙaddarar da ta faɗa mata a silarsa, sai da Baba ya daka mata tsawa sannan ta shige ciki tana kuka.

 

Kalaman Alhaji Saminu sun yi tsauri a gare ta ta kasa gasgata cewa yau shi ne wai yake kiranta da kucaka, kalamansa na baya ta tariyo ta haɗa da waɗanda kunnenta suka jiye mata ɗazu ta ɗora a sikeli domin ta gano wanne ya fi rinjaye, sai dai duk yadda ta kai da aunawar ta kasa gasgata cewa kalaman da ya furta a gare ta yau sune ainahin matsayinta a zuciyarta waɗancan duk yaudara.

 

'kenan yana nufin ya ci moriyar ganga zai yada korenta? Ina ba zai yiwuwa sai na nuna masa cewa ni kilaki ce kamar yadda ya faɗa, duk rintsi sai na haife masa shegen cikinsa kuma na kai shi har wurin wanda baya son labarin ya jewa, sai na ruguza farincikinsa kamar yadda ya ruguza nawa.'

 

Haka ta ci gaba da saƙe-saƙe tare da zallar nadama mara kwatantuwa.

 

Ba yadda Inna bata yi ba akan ta zubar da cikin ta ƙi amincewa, a haka ta shafe watanni tara cikin zallar uƙuba da take sha a gidan bayan laulayin da take fama da shi, ga gulmar mutanen unguwa duka ta jure don cika muradin zuciyarta.

 

Bayan shafe tazarar wadannan watannin ta haifi yarta mace mai kama da ita sak, sai dai kana ganin jinjirar zaka san ba a raini cikinta cikin wadata da kulawa ba domin duk jikinta a jeme yake kamar yadda mahaifiyartata take a jeme.

 

Ranar da Hanee ta haihuwa Inna ta sha kuka ta yi istaqfari mara adadi musamman lokacin da ta ɗora idonta akan jinjirar kuma ta tuna ta hanyar da aka same ta.

'Ba shakka wannan duk sakacina ne, da ban biyewa don zuciyata na aikata alfasha a baya ba da girman wannan kuskuren dana aikata bai bibiyi zuri'ata ba, kaicona ni Luba.'

 

Haka Hanee ta ci gaba da renon yarta cikin tsana da tsangwama da kyarar mutanen unguwa har lokacin da yar ta cika watanni biyar a duniya.

 

Watarana ta saci hanya da sunan zuwa gidan aminiyarta ba ta zame ko'ina ba sai gidan Honourable Tasi'u mai akwai, tana zuwa ta nemi maigadi ya mata iso gun mai gidansa. Lokacin kuwa kamar ta kintata Alhaji Saminu na gidan aka mata izinin shiga.

 

Da sallamarta ta shiga har tsakiyar harabar gidan sai gasu sun fito bayan ta gaida honourable Tasi'u ta fara magana ba tare da kallon Alhaji Saminu dake gefe cikinsa ya duri ruwa ba.

 

"Ina wuni Alhaji." Ta gaida shi cikin ladabi.

"Lafiya qlau amma ban waye ki na baiwar Allah."

 

"Haka ne Alhaji, na hannun damanka bai taɓa haɗa mu ba ne shi ya sa, yau ga ni na zo gare ka...."

 

Kafin ta kammala rufe baki Alhaji Saminu ya kalli ogansa ya ce "Ya haj Ni zan tafi tun da mun gama magana..."

 

"Kana tsoron na fallasa asirinka ne a gurinsa? Idan wannan ne gara ka tsaya don ko tafiya ka yi abinda zai faru kenan." Ta masa murmushin mugunta.

 

Honourable ya ci gaba da binsu da ido, ta yi murmushi tare da kunto yar dake bayanta ta ce "ranka ya daɗe na zo kawo maku jinjirarku ne, na ga tun lokacin da aka haife ta baka ziyarce ta ba da alama Abbanta bai sanar da kai wanzuwar ta a duniya da silar hakan ba."

 

"Bangane ba baiwar Allah me kike son cewa ke matar Saminu ce?"

 

"Ko ɗaya, sai dai ni uwar ɓoyayyiyar yarsa ce?"

 

"Kin saka Ni a duhu fito mini a mutum yarinya."

 

Nan take ta fashe da kuka sannan ta fara labarta mi shi tun lokacin haduwarsu ta farko da Alhaji Saminu har zuwa yau.

 

Alhaji Saminu ya soke kai ƙasa lokacin da uban gidansa ke tambayarsa "Shin abinda wannan yarinyar ta faɗa gaskiya ne?"

 

Ganin ya yi shiru ba amsa ya kalle shi cike da ɓacin rai ya ce "Amma ka ba ni kunya Saminu, Albasa bata yi halin ruwa ba da ba zata yi yaji ba. Ka sani cewa a duniya inda wani mutum da natsana yana bayan mazinaci, amma ka yaudare ni, a ƙarƙashin inuwar dukiyata kake fakewa kana aikata alfasha mafi girma. To ka sani daga yau zaka janye akan duk wani matsayi da kake nema a ƙarƙashin ikona, kuma dole ka auri wannan yarinyar idan ba haka ba zaka yi biyu babu."

 

Yana gama faɗa ya juya zuwa ciki yana faɗar "Ka ba ni kunya Saminu."

 

Hanee ta ɗaga murya tana faɗar "Alhaji Ni fa ba inda zan koma da yar nan, ance mini kai ne tamkar mahaifinsa shi ya sa na kawo maka ita."

 

Tana gama faɗa ta kunce goyon ta kalli Alhaji Saminu ta sheƙe da dariya murya ƙasa-ƙasa ta ce "Wannan kaɗan kenan daga cikin tuggun ƙaramar kilaki, ka haddace wannan a daƙiƙiyar ƙwaƙwalwarka sauran na biye." Ta kalle shi  a wulaƙance ta juya ta fice daga gidan.

 

Ya kalli yar da ta ajiye a kan tsakiyar gidan tana ta faman tsala ihu bisa ga tilas yasa hannu ya ɗauke ta. Da yake rabonsa da Hanee tun ranar da ya je gidansu ya masu cin kashi, sai yau ya koma ɗora idonsa a kanta.

 

Murya ƙasa-ƙasa ya ce "Zaki ga sharrin alhazan bariki Hanifa, da ni kike zancen sai na ga bayanki matuƙar ina numfashi a doron ƙasa...."

 

 

 

 

 

Ummu Inteesar ce