DUHU DA HASKE: Fita Ta 31
DUHU DA HASKE
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 32*
~Dare duk suna zaune a falo banda Ameesha wacce take zaune tana danna laptop akan gadon ammi take, ta gaji sosai so take tayi bacci, ammi ce ta shigo tana rike da kwalba zama tayi a gefen ameesha tace "bacci fa kikeji ya kamata ki kwanta"
hamma tayi sannan ta aje laptop ɗin tace "to ammi bari na tafi dama har kaina ya fara ciwo"
tashi tayi zata tafi ammi tace "ameesha?"
a hankali tace "na'am ammi"
nuna mata wajen data tashi tayi tace "zauna mana akwai maganan da nakeso muyi"
zama tayi ammi tayi shiru, tace "ammi menene? akwai wani matsala ne?"
ammi tace "kwarai ameesha akwai matsala sosai ma"
tace "na menene ammi?"
tayi maganan tana kallonta da alaman tsoro, ammi tace "zanso muyi wannan maganan dani dake da man amma yana cikin ƴan uwanshi yanzu zasu iya ganin kamar mun keɓe zaki iya janshi da wayo zuwa garden na gidannan sai muyi maganan acan?"
ameesha tace "to ammi"
murmushi tayi mata sannan tace "to tashi kije ni kuma zan fita ta kofan baya sai ku sameni acan"
tace "to"
tashi tayi zata tafi ammi tace "kada ki bari kowa ya gane zaku fito"
gyaɗa kai tayi gabanta yana faɗuwa, fita tayi ta gansu duka a falo suna hira shida yazeed, su kuma su Imran suna sana'a cewar ameesha wato game, Imran bai san ma tazo ba duk hankalinshi akan game ɗin fizge remote tayi tace "an gama game"
yace "saura kiris fa na gama unty meesha dan Allah ki bani"
ɓoyewa tayi ta hanashi ta zauna akan sofa kusada man tace "bazan bayar ba"
yace "dan Allah unty meesha idan na gama zan baki da kaina"
wurga mishi tayi ganin kamar zai mata kuka, yazeed ta kalla tace "ya yazeed kamar fa bacci kake ji naga sai lumshe idanu kake"
tsaki kaɗan yaja yace "meesha na gaji wallahi bari ma naje na kwanta dama banson barin man shi kaɗai naga babu alaman bacci a idonshi, tunda kinzo bari naje na kwanta"
tace "to ya yazeed good night"
tafiya yayi, man ya juyo duka yana kallonta, murmushi tayi mishi zatayi magana momy ta fito tana rike da flower a hannu tace "meesha wannan na cake ɗin da zan yiwa Amal ne kince kin iya cake muje mu tayani"
ameesha tace "to momy amma ki bari anjima zanyi miki da kaina"
tace "a'a ameesha dare fa yayi"
tace "karki damu momy zauna zanyi nace miki"
zama momy tayi tace "to bari na kalli game nasu Imran, ameesha ta saci kallon man ido huɗu sukayi tayi mishi murmushi kasa tayi da murya tace "soyayya nake so muyi"
dariya yayi kaɗan sannan yace "to muyi"
tace "ba anan ba"
da mamaki yace "to aina my meesha?"
tace "a garden"
waro ido yayi ya kalli lokaci sannan yace "garden war haka meesha?"
tace "yes acan nakeso muyi soyayya yau"
shiru yayi yana kallonta sai kuma yace "to muje"
fita sukayi momy tace "ina zakuje?"
man ne yace "wai garden"
murmushi tayi ganin ameesha tana turo baki kada ya faɗi abinda ta faɗa, tafiya sukayi zuwa garden tun a bakin kofa yace "to munzo me rigima"
tace "shiiii ammi ce take nemanmu tace muzo mu biyu kada kowa ya sani"
da sauri yace "ina take?"
ammi dake nesa dasu kaɗan tace "gani"
ganinta sukayi tana tsaye ta goya hanu a baya, tare suka karaso ta fara magana tana zagayasu tace "wani abu ya bani mamaki game daku man"
shiru sukayi, tace "kun san menene abin?"
tare suka girgiza kai, tace "tun ranan dana haɗa ido da mahaifiyar manal naji gabana yana faɗuwa ku kuma banga alaman komai a tare daku ba, hankalina kwata kwata ya kasa kwanciya da wannan matar wallahi duk yadda take shiru shiru manal kawai nake gani a tare da ita, ban fara jin tsoronta ba saida tace kanwarta zata zo nan gidan, anya kuma ganin babu matsala? anya zuwan kanwarta ba zai kara jefa rayuwarmu a hatsari kamar yadda manal ta jefa namu ba? ban hango alkhairi game dasu ba wallahi ina tsoro"
man ya kalli ameesha itama ta kalleshi, kallon ammi fa tsorata tayi da manal shiyasa take tsoron momy amma momy batada matsala hasalima ta tsani manal, kuma babu yadda za'ayi ace kanwarta da momy halinsu ya zama irin na manal"
hanunta ameesha ta rike tace "zauna ammi"
akan kujeran dake wajen ta zaunar da ita sannan ta durkusa ta zuba hannayenta a cinyar Ammi wacce kana ganinta kasan tana cikin damuwa, man ma ya durkusa a gabanta sukace "ammi a tsorace kike shiyasa kike wannan maganan, momy batada wani hali kawai dai kin gama tsorata da ƴarta manal ne, amma kin manta irin tsanan data yiwa manal? kin manta a gabanta a rataye manal kuka kawai tayi na uwa da ƴa? tunda Allah ya bayyana mata ƴar uwarta guda ɗaya tilo a ganinmu bai kamata mu juya mata baya mu nuna mata muna zarginsu da wani hali ba ko ammi?"
cikin yanayin damuwa tace "ba zaku gane bane yarana ray...."
rufe mata baki ameesha tayi da ɗan yatsa tace "amminmu ta gama tsorata ne kuma munsan bakiso rayuwarmu ta kara shiga irin yadda muka shiga a baya amma babu komai insha Allah"
ammi tace "to shikenan amma rayuwarku nake tunawa ameesha da man kada fa...."
man ne ya rufe mata baki wannan karon ya ɗagata yace "muje ki kwanta dare yayi ammi baba ma ya jima da dawowa"
zatayi magana sam suka hanata akan gado ta kwanta ameesha ta zauna a gefen hagu man a gefen dama, duk suna son kwantar mata da hankali sukace "karki damu kiyi baccinki babu komai ki cire tsoro a ranki"
a hankali tace "to shikenan Allah ya barku tare har karshen rayuwarku Allah yasa ayi aurenku a sa'a ku haifo yara irinku masu taimako da jajircewa marasa tsoro masu neman na kansu"
a hankali suka amsa da "ameen ammi"
baba ne ya shigo da sallama man yace "yawwa baba zo kasa matarka tayi bacci zamu tafi"
baba yace "wai nikam man mantawa kake ni mijin uwarku ne baku jin kunyata?"
dariya man yayi suka tashi shida Ameesha suka yiwa ammi saida safe, a falo suka tarda babu kowa ameesha tace "saida safe"
zata wuce ɗakinsu da hanan ya tare hanya, da sauri tace "me?"
lumshe mata ido yayi ya buɗe yana kallonta, tace "me?"
yace "soyayyan mana ba kince zamuyi ba?"
tureshi tayi ta wuce, da sauri yace "to saida safe"
tace "Allah kaimu lafiya"
ta rufe kofan bayan ta ɗau cake na momy ta tashi hanan dake bacci tace "tashi muyi cake"
hanan tace "cake kuma na me?"
cikin muryan bacci tayi maganan, ameesha tana fara shirye shiryen kwaɓa cake tace "na zuwan amal mana ya kamata muyi kada ran momy ya ɓaci taga kamar bama murnan zuwan ƴar uwarta"
mika hanan tayi cikin bacci take kallon ameesha tace "nifa kinga dama ba wani murna nake ba, hasalima banga yarinyar ba amma wallahi naji na tsaneta yaƙe kawai nake a wajen momy sabida naga tanada hakuri da bawa mutum girma shiyasa badan haka ba wallahi na tsaneta"
murmushi ameesha tayi haka Imran ya faɗa mata sabida momy ne kawai yake nuna yanason zuwan yarinyar badan haka ba shima yace bama yason ganinta, tace "to shine ba zaki tayani ba?"
tace "wallahi ba zanyi ba"
komawa baccinta tayi duk yadda ameesha taso ta tayata taki, ita kaɗai tayi cake ɗin a sama ta rubuta you are welcome Amal"
cake ɗin yayi kyau sosai a ranta tace "ban taɓa yin cake me kyawun wannan bama"
kaiwa fridge tayi tasa sannan tazo tayi wanka tasa kayan bacci ta haye gadon kusada hanan sai bacci.
Man yana kwance akan gado sai juye juye yake, shifa tunda yaga momy shima kamar ammin ne hankalinshi yaki kwanciya, daya kalli idon momy sai taga kamar manal yake kallo, yana daurewa ne kawai sabida yaga wannan tanada hakuri sosai batada matsala gata da son mutum, gashi Abba yana sonta sosai kamar ya cinyeta tsaban biyayyan da take mishi, amma shima tuna yaji wannan kanwar tata zatazo sai yaji bayason ma tazo gidan, share zancen yayi ya fara tunanin ameesha yaso ya kirata a waya yaga dare yayi kawai ya bar kiran ya fara bacci.
washe gari ameesha ce ta yiwa momy surprise ta hanyar yin decorating na gidan gaba ɗaya, musamman main parlour ta gyara da kayan ado masu kyau kamar za'ayi event a wajen, girki taje kitchen ta fara yin masu lafiya, ta samo manya manyan warmer's ta zuba aciki ta kai dining, sannan tayi lafiyayyen juice me bala'in daɗi shima ta kai dinning, kafin kowa ya tashi ta gama komai da komai, part na ammi taje domin kiransu tunda momy tace ƴar uwarta jirgin safe zatabi ya kamata a shirya mata zuwa ɗaukota, waya ta kira tasa motoci su shirya, momy tunda ta tashi tayi wanka ta shirya cikin lafiyayyen maroon na leshi wanda yasha ɗinkin half bubu, tayi bala'in kyau tasa sarƙan gold da Abba ya siyo mata, tasa bakin mayafi yau ta fito asalin balarabiya, fitowa tayi cike da farin ciki tana amsa waya cikin harshen larabci take magana, duk suka kalleta yadda take larabci sosai abin birgewa, murmushi tayi musu tana kan yin wayan saida ta gama ta katse kiran kafin ta fara bin ko ina da kallo, kallon ameesha wacce tayi matukar kyau cikin riga da wando na pakistan me kyau sosai, tayi kitso ɗata da gashinta ta sauke har bayanta, ta shafa gel a gaban gashinta dake kwance a goshinta, tasa takalmi flat da karamin mayafin pakistan dress ɗin, tace "kece kika yi wannan"
ameesha tayi murmushi tace "bani kaɗai bace nida kowa ne sabida murnan zuwan ƴar uwarki Amal"
cikin jin daɗi ta kalli dukkansu sunyi kyau sosai da alama zuwan ƴar uwarta kawai suke jira, tace "na gode muku Allah ya saka da Alkhairi bansan ta yadda zan gode muku bama"
sukace ba komai, saide fa da ganinsu duk kasan yaƙe suke ameesha ce ta sasu dole musamman ammi da Imran dan ko daga maganansu zaka gane bale hanan dake Allah Allah ta koma ɗaki, momy tace "bari naje na ɗaukota nafi son ta sameni a airport ba wai ta jirani ba"
ameesha tace "zamu rakaki"
tace "ba komai ku zauna zanje na taho da ita"
ameesha tace "a,a momy ki bari..."
hanan ce ta danne hanunta alaman tayi shiru, shiru tayi momy tace "na gode muku bari naje"
taga yadda hanan ta danne hanun Ameesha bataji daɗi ba, tare sukace "Allah ya kiyaye hanya momy"
tace "ameen"
fita tayi, ameesha tace "amma wallahi sai kun canja hali kun san fa momy tanason ganin farin cikin kowa a gidannan ya kamata itama mu rinƙa faranta mata"
duk suka amsa da "to"
sannan kowa ya wuce dinning, tsayawa tayi tace "babu wanda zaici har sai momy ta ɗauko Amal sunzo tare za'aci sabida momy tasan mun damu da ƴar uwarta da ita"
duk suka fara cewa "wallahi a'a mu ba zamu jirata ba kisa mana abinci kawai"
Abba ya sauko daga stair yace "ameesha ta fiku gaskiya sabida haka dole ne kubi magananta"
shiru sukayi kowa yana kwaɓa fuska babu wanda ya kara tanka mata kamar su tashi su rufeta da duka, man hararanta yake taki yadda su haɗa ido, gara yazeed ma danna waya kawai yake.
ammi kuma tayi shiru kamar akwai abinda yake damunta, baba daya lura yayi mata alama ta saki jiki, da kyar ta ɗan saki jikinta.
*Jiddah Ce...*
managarciya