Babban Buri:Fita Ta Shida

Cike da kallon mamaki ta ke kallonsu har suka fice daga cikin ɗakin, gyaɗa kai ta yi da hanzarin ta ta miƙe ta nufi ɗakin Haidar,  sallama ta yi da yake yana zaune Parlour , gyaran murya kaɗai ya yi ta faɗa cikin ɗakin a kiɗime. Zama ta yi a dai-dai gurin da yake zaune ta kai kallonta kansa sannan ta ce "Shalelena ka ji wani zance da iyayenka suka shigomin da shi?". Gyaɗa kansa ya yi sannan ya buɗe baki ya ce "na ji duk abin da suka ce, sai dai dama suna meeting ɗin nan ne a duk ƙarshen mako ko kuwa wannan makon ne za su fara?."

Babban Buri:Fita Ta Shida

BABBAN BURI.

MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.

SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU} MARUBUCIYAR MATAR ABDALLAH

FITOWA TA SHIDA.


Bayan an fito daga masallaci ne Alhaji Amadu  ya tare shi da batun  a kwai meeting ɗin da suke yi a duk ranar ƙarshen mako, dafatar zai samu halarta.

Kallon tsana ya watsawa ƙanen mahaifin nasa kafin ya yi gaba ba tare daya ce da shi komai ba.
Juyawa ya yi wunda 'yan uwansa suke tsaye ya ce "kun ga ja'irin yaro?."

Alhaji Mu'azu ne ya sauke a jiyar zuciya sannan ya ce "mu bi ta gun wacan tsohuwar ko Allah zai sa a dace".
Haka kuwa suka ajiye , kai tsaye daga masallaci sashen Hajiya Inna suka nufa wace ta kan yi wata biyu bata sanya ko ɗayansu cikin idanuwanta ba.

A Parlour suka sameta, gaidata suka yi sannan suka gaya mata batun meeting ɗin da za su yi yau.
Kallonsu ta yi ɗaya bayan ɗaya sannan ta ce "tau me kuke buƙata yanzu?".

Gyara zama Alhaji Sunusi ya yi sannan ya ce "Hajiya Inna muna buƙatar ganin ku ne dake da HAIDAR a wajen meeting ɗin nan domin kuwa ya dangance ku ne."

Gyaɗa kai ta yi ta ce"tau Allah ya kaimu lokacin ƙarfe nawa ne za'a yi?".
9 na safe  suka bata amsa suna masu miƙewa tsaye.

Cike da kallon mamaki ta ke kallonsu har suka fice daga cikin ɗakin, gyaɗa kai ta yi da hanzari ta  miƙe ta nufi ɗakin Haidar,  sallama ta yi da yake yana zaune Parlour, gyaran murya kaɗai ya yi ta faɗa cikin ɗakin a kiɗime.

Zama ta yi a dai-dai gurin da yake zaune ta kai kallonta kansa sannan ta ce "Shalelena ka ji wani zance da iyayenka suka shigomin da shi?".
Gyaɗa kansa ya yi sannan ya buɗe baki ya ce "na ji duk abin da suka ce, sai dai dama suna meeting ɗin nan ne a duk ƙarshen mako ko kuwa wannan makon ne za su fara?."

"Suna yi sai dai  a ɗaya rana ba su taɓa nema na a kan na je meeting ɗin ba, in taƙaicema na kan yi wata biyu zuwa uku banga ɗaya daga cikin su ba."

Juyowa ya yi gunda take ya ce "tabbas a kwai lauje cikin naɗi a cikin wannan taron sai dai tambaya Hajiya Wai mi muka tarewa wadannan bayin ne?, Ko wane ɗan adam da nasa BURI na alkheree ko akasin hakan, amman su da alamu ba BURIN aikata abu mai kyau a tare da su."

Kyaɗa kai Hajiya Inna ta yi  ta ce "tabbas *RAI DA BURI* aka san shi BURIN na alkheree ko akasin hakan amman ina mai gayama ka yi taka tsantsan da wadannan mutanen domin kuwa ina kuke da su burin da yake ransa ba mai kyau ba ne."

Cije lips ɗin bakinsa ya yi na ƙasa sannan ya ce "karki damu, ina nan ina kallon ko wanensu da idanuwa, zan ba su mamaki."
"Zan je taron da suka ce domin na ji miye da miye za su ce."

Miƙewa ta yi jikinta a saɓule ta fice daga ɗakin.

Ƙarfe takwas da rabi na isa gidan, wanda har lokacin masu gidan ba su tashi daga barci ba da alamu.

Ina shiga Yahanazu take sanar dani yau masu gidan suna da meeting ɗin safe a babban Parlour kamar yadda ta ji ana faɗa.
A gurguje muka haɗa masu break fast kana muka kai a babban Parlour muka ajiye ko wacen mu ta kama gabanta.

Sashen Hajiya Inna na nufa, cikin shirinta na tarar da'ita tana karin safe, kunun tsamiya ne da ƙosai take sha , miƙomin cup ɗin ta yi bayan mun gaisa, sanin cewa bata son gardama ya sanya ni sa hannu biyu na amsa na yi zaune a ƙasa ina ƙurɓar kunun muna ɗan taɓa fira da ita.

Can ta ce dani "Za mu je meeting a babban Parlour Hadeejatu ki sharemin ɗakinnan dan Allah ki haɗa dana shalele ki gyara mana su kin ji, idan kika ƙare ba mu dawo ba ki shiga kitchin ƙullun wake yana nan a cikin freezer ki haɗa mana alale."

Cike da gamsuwa na amsa mata da "tau" kana na ci gaba da shan kunu na.

Ba mu jima a zaune ba kuwa wani sanyayyen ƙamshi turare ya ziyarci hancina , lumshe idanuwana na yi haɗi da buɗe su a kan ma mallakin wannan ƙamshin.

Sanye yake cikin ƙananan kaya , wadanda suka fito da ainihin kyaunsa yayin da kansa  ya sha gyara domin kuwa kwance yake luf luf luf da gashi.

Gaida shi na yi ba tare daya kalli in da nake ba ya amsa da "lafiya" hakan bai dame ni ba domin kuwa ban ma sa ran ya amsa ba, sai kuma na dinga mamakin kaina miyasa idan na ganshi gabana ya dinga faɗuwa  sai lokacin dana daina ganinsa ya bari?."

Taɓe ɗan ƙaramin bakina nayi kana na ce "Allahu a alamu".

Tsinkayo muryar Hajiya Inna tana yimin sallama ne ya sanya ni mayar da hankalina kansu , wanda zuwa lokacin ya yi ficewarsa daga ɗakin ashe.
Ƙara taɓe bakina na yi na ce "kai dai ka sani"

Sannan na miƙe na je na fara gyara ɗakin Hajiya Inna, ban ɗauki tsawon lokaci ba na kammala da yake ɗakin ba wani datti ne dashi ba.

Ɗakin Shalelen Hajiya Inna na shige a Parlour na shiririce gurin kalla ce kallace, sannan na faɗa uwar ɗakin, ko a can na ɗauki tsawon lokaci kamin na hanzarta ajiye komai a muhallin sa na share a ɗakin wanda ba wata ƙazanta a cikinsa sai ɗan abinda ba'a rasa ba, anan na ƙara tabbatar da tsaftar Shalelen Hajiya Inna."

Parlourn part ɗin na fito sannan shi ma na sharesa haɗi da yin morping kana na feshe ko ina da turaren air fresh....

Kitchin na nufa na haɗa komai da ake buƙata na alale kana na ƙulleta a leda na sanya a cikin tunkunya na kunna gas na fito daga kitchin ɗin  na ƙarewa ɗakin kallo gwanin sha'awa fes da shi.

A can kuwa bayan buɗe taro da addu'a  Alh Bello, shi ne babba a cikinsu, ya kalli HAIDAR ya ce "Wannan taron kusan a kanka ne za'ayi sa,  ba dan komai ba kuwa sai dan mu ƙara ƙarfafa zumunci mu, ta hanyar Aura ma ɗaya daga cikin 'yan matan dake cikin gidannan, idan kuwa har akwai wace kake ra'ayi daga cikinsu za ka iya sanar mana".

Ba tare daya ɗago kansa ba kai tsaye ya ce "Ba 'yar wanda zan aura daga cikin ku!, Idan ita kaɗai ce maganar ku inada abin yi, idan kuwa ba ita kaɗai ba ce ina jin ku!."

Kallon kallo suka rika  a tsakaninsu kan Alhaji  Murtala da tun fara maganar bece komai ba ya ɗago a zafafe ya ce"Wannan wacce irin maganar banza ce kuma, ta yaya muna a matsayin iyayenka kake neman ka gaya mana maganar banza?."
"Kenan idan shi Aminun ya dawo  yanzu ya baka umurnin yin wani abu za ka iya cewa da shi kai tsaye ba zaka yi ba?."

Ɗago da dara daran idanuwansa ya yi ya zube su a kan Alhaji  Murtala ya ce "idan shi ne ko wuta ya ce na faɗa ba makawa zan faɗa domin ganin na faranta ransa, ku ne dai bazan iya faranta ranku ba akan son cika wani BURI naku na can daban, don haka ku kiyaye halshenku idan kuna maganarku ku daina sanya bawan Allahn da bai san abin da ake yi ba!"

A matuƙar kiɗime suke biyansa da idanuwa kan Alhaji Usman ya kai kallonsa gunda Hajiya Inna take zaune tana biyansu da idanuwa ya ce "Hajiya Inna kina jin cin mutuncin da wannan taƙadirin yake yi mana amman kin yi shuru kuma....

Za mu cigaba a gobe......


ƳAR MUTAN BUBARE CE.