HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Ban Al'ajabi, Fita Ta 30

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Ban Al'ajabi, Fita Ta 30

HAƊIN ALLAH: 

   

              Page 30


                 JIDDAH


Tun da ta dawo daga Kano gun rasuwar Uncle Salim sai ta sake komawa miskilar gaske, bata damu da kowa ba, bata magana, ranar da ta dawo ta sauka gun Mamarta sai dai da kanta taga dacewar ta matsa daga gun Mamar saboda yadda ita ma Mamar take zaune ba daɗi hakan yasa ta yanke shawarar barma Mama Haidar tun da bata da yaro ƙarami gabanta, ita kuma ta tattara kayanta ta nufi gidan mahaifinta, sai dai gidan a rufe yake ga alama kuma ya jima da rufewa don haka ta nufi asalin gidansu mahaifinta kanta tsaye duk da tana jin faɗuwar gaba amma sai ta dake ta nufi can, tana zuwa da sallamarta ba kowa tsakar gidan don haka ta nufi ɗakin Kakarta.

Tana zaune ga alama sallah ta gama, Jiddah ta gaidata ta amsa ba yabo ba fallasa bata damu ba tasan daman hakan zai faru don haka ta share ta kai kayanta ta ajiye ta dawo ta kalli Kakar tace, "Kaka naje gidan Babana naga ba kowa ko sun tashi daga gidan ne?"

Kamar ta kai mata duka haka ta watsa mata kallo sannan ta ce, "Ban sani ba, nace ban sani ba, kema shegiyar gulmar ce ta taso ki daga gidanki kika zo ki ka tasani gaba da tambaya? To ya saida abin shi ya ƙara gaba inda babu jin zafi sai wace uwar tsiyar kuma?"

"Kaka ina matarsa to?" Cewar Jiddah.
"Ban sani ba, wai ke Ni abiyar ki ce Ni da za ki zo ki tasani gaba da tambayoyi? To ya sake ta ai shi tun da Allah Yasa ya auri uwarki da farko shi ke nan komai ya taɓarɓare mai ya kasa samun macen kirki da arziƙi har yanzu. Shi yasa ake son ka auri mace ta gari da farko sai ka ga kana ta dace dana kirki daga baya." Cewar Kaka tana maka ma Jiddah harara.

Jiddah tai murmushi tace, "To dama Deeni ne ya sake Ni don haka na nufi can tun da bai nan zama nan ya kamani kenan."
Kakar ta zaburo tace, "Gidan Uban wa za ki zauna ɗin? To tun wuri ma ki san inda dare ya yi maki ba inda za ki zauna a nan atoh na gaya maki ma, haka kawai ki zo gaki ga yara to waye zai ɗauki nauyinku? To ban iyawa tun kafin ma dare ya yi ki sake mafaka wannan ba tai ba."

Jiddah ta dubi Kakarta fuska cike da hawaye tace, "Ban ce wani ya ɗauki nauyina ko nauyin yarana ba, kawai wajen kwana za a ban shike nan amma Ni zan ci da kaina da yarana insha Allah Kaka."

"To wannan fa, yanzu ki kai magana indan wajen kwana ne akwai ɗakuna sai ki fita ki zaɓi guda ki share ki zauna ban hana ba."

Duk da taji ciwon abin amma ta ji daɗin yadda Kakar ta bata damar zama a gidan, don haka tai godiya ta miƙe ta je ta duba ɗakunan ta zaɓi wanda ya yi mata ta share shi tsab ta ɗauko kayanta ta saka ta fice ta je ta fitar da kuɗi ta sai leda da katifa da labule ta dawo ta saka a ɗakin. Fahimtar su Afnah sun fara jin yunwa yasa ta sake fita ta siyo masu abinci ta dawo suka ci tare ta bar su a ɗakin ta sake fita ta siyo duk abin da tasan tana da buƙata ta haɗo da kayan tea da sauran kayan abinci ta siyo kwaɗo ta dawo.
Nan da nan ta kammala ɗakinta tsab ta ɗebi ruwa tai masu wanka ita ma tai wankan ta tura ɗakin su kai ta wasa da dariya da yaranta tana jin damuwarta na raguwa.

Mama ta kira ta gaya mata duk abin da ya faru, tace Allah Ya kyauta kawai don bata da abin cewa kan lamarin.

Cikin sati guda Jiddah ta saba da zama gidan Kakarta duk da cewa zaman ɗaki yafi mata daɗi kan zama kusa da mutanen gidan don yanzu sun fara gaya mata magana wadda za tai mata ciwo.
Ƙarin jin daɗin ta yadda su Afnah basu bata ciwon kai sam, har ta kai su makarantar boko dake haɗe da islamiyya suna zuwa kullum hankalinta kwance, kawai ko da yaushe takan tanadar masu abinci ne da sun dawo su ci su yi ta wasa cikin ɗaki.

Kwatsam! Hutun semester ya ƙare don haka ta tarkata su ka maida ma Mama su da kayan abincinsu ta harhaɗa ta koma makaranta cike da burin yin karatu. Da ta dawo sai ta sauka ta can ta ɗauki yaranta su wuto gida.


Maza da dama na damunta da maganar aure amma ita ko a Film taga aure bai burgeta balle a gaske, ita ba abin da ke burgeta irin karatunta sai kuwa kasuwancin da ta fara na saida kayan ɗaki da sauran tarkacen mata na sawa, kuma masha Allah tana samun ciniki sosai a makarantar yadda ya kamata.

Hutun aji biyu ta samu don haka ta shirya ta nufi Kano don ko da yaushe Hajjo cikin ƙorafin rashin zuwanta take duk da tana gaya mata karatu take.

Ta so ƙwarai ta tafi da yaranta amma sai makaranta ta hana don haka ta barsu gun Mama ta shirya ta nufi Kano. Tun da ta shiga motar wani ke kallonta ita ma taga kamar ta san shi amma ta rasa ina ne ta san shi don haka ta share ta fito da wayarta ta fara karanta littafi kawai don hankalinta ya ɗauke daga kallon da mutumin ke mata.

"Amma sai naga kamar na sanki ko?" Cewar mutumin dake kallonta.

Tai banza da shi tamkar bata ji me yake cewa ba, amma saboda kunya tai mai kaɗan sai ya janye wayarta daga fuskarta ya sake maimaita tambayarsa.
Yamutsa fuska tai kafin tace, "Ban iya ganewa nima."  Murmushi ya yi tabbas ya gane yarinyar wadda yake gani ce a school ɗin su, don haka ya ce, "Wace makaranta ki ke ne pls?" Cike da gatse tace "Wadda kake."
"Tabbas nasan ke ce daman, ko a school ina ƙoƙarin yi maki magana amma sai ki share ki yi kamar baki san da mutum ba, don Allah ki daina girman kai babu kyau."

Kamar ta ja tsaki sai kuma taga rashin dacewar hakan don haka ta kauda kanta kawai, don har zuwa yanzu wayarta na hannunsa ya ƙi bata.

Tana ganinsa ya saka lambarsa ya kira a wayarta bata dai tanka mai ba, haka bata nuna ta gane me yake ba, duk tana kula da yadda ya yi saving number da sunansa ta taɓe baki ta kauda kanta.

Har suka isa Kano yana ta zuba kamar Kanyar da babu daɗi, tai banza ta ƙyale shi kowa na jin shi yana ta magana ita kuma tai banza da shi kamar bata gun.

Suna isa ya bada kuɗin motar shi da nata ya tsaida mata mai keke napep ya biya shi kuɗin ya ce ya kaita inda zata je.

Yana zaune abin duniya ya dame shi, tabbas yana cikin matsala mai girman gaske bai kamata ba ace cikin mace uku ba bai samu wadda zatai mai abin da yake so ba, ko dai shi ne ke da matsala ba matan ba? Yana son kulawa amma bai samun mai kulawa da shi, kowace kanta da yaranta kawai ta sani shi kam babu mai buƙatar ko jin damuwarsa a cikin matan nashi ko da yaushe nadama yake ta auren shi ji yake dama bai da aure tabbas da ba zai yi shi ba... Mai keke napep ya tsaya daidai saitin da yake zaune, kamar kar ya kalla don yaga mace ce zaune a cikin napep ɗin, amma kamar fisgo shi akai kawai yaga Jiddah na niyyar fitowa daga cikin napep ɗin, wani sanyin daɗi ya ji ya ziyarci zuciyarsa kamar ba shi ne zaune cikin damuwa ba.

Hankalinta na kan ta shiga cikin gidan don haka bata ga Mustapha ba da ke ta muimui da baki yana son ya yi mata magana amma ya kasa buɗe baki yadda zata ji shi, har ta shige gidan yana bin bayanta da kallo. "Jiddah nada kyau." Ita ce kalmar da ya faɗa yana bin bayanta da kallo.

Hajjo na zaune tana jiranta don sun yi waya ta iso Kano tun ɗazun, ga kulolin abinci nan gabanta ga alama na tarbar Jiddah ne. Da gudu Jiddah ta faɗa jikin Hajjo tana murna kuma sai ta saka kuka, domin ta tuna da Uncle Salim.

Hajjo tai ta yi mata dariya tana cewa, "Ba dai a san ƴar fari da shagwaɓa ba amma ga wata da rana tsaka an samu Yau."

Wayarta tai ƙara tana dubawa taga ƙawarta ce Bilkisu don haka ta aje wayar don tasan ita ma jiranta take don tasan Yau zata zo Kanon.

Abinci ta zuba ta fara ci suna fira da Hajjo tana bata labarin rayuwarta da yadda take zaune gidansu Babanta bata ɓoye mata komai ba.

Hajjo ta girgiza kanta tace, "Ki yi haƙuri Jiddah wata rana sai labari ko ban da rai sai kin tuna na baki wannan labarin za ki yi farin ciki kuma za ki ba mutane mamaki kowa da kowa zai so ki za ki zama abar kwatance a ko'ina Jiddah insha Allah."
Murmushi tai, zatai magana kenan Mustapha ya shigo gidan da sallamarsa. Hajjo ta kalle shi tace, "Idonka kenan ko Mustapha? Sam baka zuwa gidan nan yanzu sai dai naji ƙamshin turarenka kawai ka wuce ko? To ai akwai haƙƙin maƙwabtaka idan ka aje na zumuntar." 
Yana ɗan murmushi yana shafa ƙeya ya zauna ya ce, "Ba haka bane ba Hajjo ina son shigowa kawai dai abubuwa ne ke mun yawa a kwanakin nan."

Hajjo ta dube shi ta yamutsa fuska tace, "Ai daman nasan abin da zaka ce kenan idan nayi magana, ai shike nan."

Jiddah tai mai kallo guda ta kauda kanta ta buɗe baki kenan zata gaida shi wayarta tai ƙara don haka sai ta ɗaga kiran cikin natsuwa.

Daga can ɓangaren aka ce "Kina magana da Abubakar ne wanda kuka shigo mota ɗazun, dama kira nayi in maki ya gajiyar hanya?"

Kamar yana gabanta haka tai ɗan jim kana tace, "Ai naga sunanka kuma ban da shi a waya sai na tuna da kai ka kasa da kanka, na iso lafiya kaima fatan ka isa lafiya?"

Mustapha ya ji wani baƙin takaici ya sauka kan ƙahon zuciyarsa ji yake tamkar ya tashi ya fice, amma hakan ba zai samu ba, duk wani gefen na zuciyarsa ya yi murna da gane cewa bata da aure tun da har ta iya ba wani wayarta ya saka lamba da sunansa na banza.

Jiddah ta gyara riƙon wayarta sosai a kunne tace, "A'a na gode ba sai ka zo ba, ai ba damuwa ban fita zance Ni."

Hajjo tai tsaki tace, "Ƙaryar banza kenan, baki zance to haka za ki zauna ba za ki yi aure ba kike nufi? To tun wuri ma ki bar wannan shirmen ki fitar da miji ki yi aurenki nasan dai yanzu ai kin kusan gama karatunki ai."

Daga can Abubakar ya ce, "Haba Hawwy baki ji me ake ce maki ba, kawai ki ban damar gwada sa'ata ba mamaki ni ne mai rabon."

Jiddah ta langaɓar da kanta gefe kamar zatai kuka tace, "Baka san halin Hajjo bane ba, tsokanata take wane irin aure kuma yanzu?"
 
Abubakar ya ce, "Ni dai don Allah aban damar zuwa na sake tozali da kyakkyawar fuskar nan taki mai saukar da natsuwa ."

Kasa magana tai kawai ta bi shi da murmushi.

Mustapha dake zaune ya kasa haƙuri ya kalli Hajjo ya ce,  "Bata da aure ne yanzu Hajjo kike mata faɗan aure tana waya da masoyinta?"

Hajjo tace, "Kai dai bari kawai Mustapha wallahi tun lokacin rasuwar Salim mijin ya sake ta amma shi ne taƙi fitar da miji tai aure har an doshi shekaru biyu ana niyyar shiga ta uku."

Wani irin farin ciki ya ziyarci fuskarsa ya ji tamkar albishir da warwarewar matsalarsa Hajjo tai mai ya kalli Hajjo dake riƙe da waya ta kasa cewa komai jin maganar Hajjo.

Abubakar ya ce, "Na lura yanzu baki da lokaci don haka anjima zan kira ki."

Ta aje wayar tana ajiyar zuciya sai kuma ta kalli Mustapha dake kallonta ba yabo ba fallasa ta gaida shi.

Ya amsa ba tare da gane abin da amsar ke nufi ba ya miƙe yana ma Hajjo bankwana ya fice.

Jiddah ta saka hijabinta ta nufi gidan ƙawarta Bilkisu tun daga zaure take sallama dan tasan ta shaƙa mata haushi yadda take ta kiranta bata amsa kiran ba kuma bata shiga gidan ba.
Bilkisu ta kauda kai tana cewa, "Nayi fushi ai dama kin koma."

Jiddah tai dariya ta ɗaga yaron Bilkinsun tana mai wasa ta isa ɗakin tana cewa, "Ke fa daɗina dake kenan baki ma mutum uzuri sam."


Mustapha yana zaune ɗakinsa yana jin tamkar wani albishir akai mai da kujerar Makkah. Jiddah bata da aure tabbas kwanakin nan yana yawan mafarkinta suna cikin soyayya da faranta ran juna, kowa cikin annashuwa da fara'a ashe kenan hakan zai faru? Allah na gode maka da ka nuna min ranar da naji labarin da na jima ina neman ji.

Ya juya yana hasko yadda ta zuba mai ido tana gaida shi fararen idanunta suka sauka a cikin idanunsa. Kamar a lokacin ne haka ya ji wani yarrr baki ɗaya jikinsa ya yi.

Tabbas yana ji a jikinsa ƙarshen damuwarsa ta zo, domin yana tuna yadda Salim ke yawan yabon yarinyar ko da yaushe bakinsa na kan Jiddah nada haƙuri tasan abin da take, tabbas ita ce daidai da shi ba zai sake wani ya yi mai shigar sauri ba kuma wannan karon kamar aurenta na farko da sai dai ya ji labarin tai aure kawai.

Yaron shi ya shigo ɗakin da sallama ya ce, "Mama tace zaka ci abinci na kawo maka?"

Wani ɓacin rai ya ziyarci fuskarsa wai ace kana da mata amma ba zata iya kawo maka abinci ba da kanta ta zauna gabanka ko bata cin abincin da kai ai ta zauna ta kula da kai idan kana ci, amma shi duk wannan bai samun shi ga duk matan uku daya ajiye. Cikin zaƙuwa yaron ya sake cewa, "Baba a kawo maka abinci?"

Cikin ɓacin rai ya ce, "Ka ce ban ci."

Yaron ya juya ya fice ya koma ya gayama Mamarsa abin da Babansa ya ce, bata damu ba sai ta sake gyara zamanta kawai tace a ranta ("Kai ka sani wallahi ya ƙara yawa ma) ta cigaba da harkar gabanta hankalinta kwance domin ba Yau bane karon farko da maigidan ya ƙi cin abincinsa ba, ita ba zata iya ma shegen iyayinsa ba, mutum kamar wata mace sai shegen son tarairayata ga son girma kamar wani gyambo, ta sake taɓe bakinta ta ja tsaki tace a fili wannan karon, "Bar shi ya je ya ci na titi ai ya ƙware daman shi ya sani dai."

Yaron ya ce, "Mama mu ki ƙara mana daman ban ƙoshi ba Ni ɗazun."
Ta dubi yaron tace, "Kambu! Duk abincin da ku ka ci zaka ce baka ƙoshi ba? To ai saika ɗauko na zuba ma, kana gamawa ka zo kai wanka na gayama tun jiya nake fama da kai kan wankan nan sai na gayama Babanku Yau idan bakai wankan nan ba."

Ya ruga ya ɗauko abincin ya kawo mata ta zuba mai, suma sauran yaran suka taso sai an ƙara masu, ta juye masu sauran abincin duka tana cewa "Ai sai ku cinye ku fini ƙiba ku da baku da tausayina."

Karaf kishiyarta ta fito tana huci ta warce kular abincin tace, "Ai ba yaranki bane kawai yara a gidan akwai sauran masu haƙƙi a cikin abincin a gidan don haka sai a basu haƙƙinsu ai abincin ubansu ne ba daga wani gida aka kawo shi ba ehe." 

Maryam ta zaburo ita ma cike da masifa tace, "Dakata Malama! Ina ruwanki da abincin ranar girkina? Ko kinga ina kula ki ranar girkinki ne? Ai ba don ban san bai cin abincin ba sai don a zauna lafiya kawai, don haka tun wuri ki aje abincin nan kafin a ji kanmu yanzu."

Hafsat ta zaburo ita ma cike da masifa tace, "Ai ba hanaki zuwa nayi ki ɗiba ba, don haka ruwanki ne kuma wannan abincin ko dawa kike yawo ba zan barma yaranki shi ba, shegun yara masu shegen cin tsiya kawai."

Maryam ta finciko kular abincin tana cewa, "Ban haifi shegu ba sai dai ke kika haifi shegu abinci kuma sai dai ya zube ayi asarar shi da matsiyatan yaran can naki su ci shi, ko da yake ai ba su kaɗai kike ci dawa da abincin gidan nan ba ina da labarin wanda kike sata kina kaiwa gida tsoffi na zubawa a tukunya ai...

Bata kai ƙarshen maganar ba, Hafsat ta kai mata duka suka watsar da abincin suka kama dambe yara na kallonsu sun yi tsuru-tsuru da su, ganin da gaske suke ɗan babban ya ruga ɗakin Mustapha ya gaya mai su Mama na faɗa saboda abincin shi.

Wani takaici ne ya sake ziyarar zuciyarsa don haka yai banza da yaron ya cigaba da jin ɗacin da ransa ke ma shi, bai ankara ba hawaye suka zuba mai, ya dinga jin karayar zuciyarsa na ƙara hauhawa tabbas bai dacen mata ba sam, ya zai yi haka tashi ƙaddarar take dole ya jure ko da kuwa hakan zai sa hawan jini kama shi ko ciwon zuciya.

Haka ya dinga kuka kamar ƙaramin yaro yana jiyo tashin muryar matan nashi da kowacce ke zagin ƴar'uwarta suna aibata juna gaban yaransu abin takaici da ban haushi.

Kamar ya ƙyale su sai kuma ya miƙe jikinsa sanyi ƙalau ya nufi sashen matan nashi yana jin kamar zuciyarsa zata fice don ɓacin rai.

Ko kunya basu ji sun dage sai dambe su ke ga abincin nan a watse ƙasa yaran kuma suna zaune suna kallonsu.

Daka masu tsawa ya yi amma sun yi nisa ba mai jin shi don haka ya sake ɗaga murya sosai ya ce, "Wai wane irin jahilci ne wannan kuke da girmanku a gaban yaranku? Kuna abu sam babu mutunci babu tunani a gaban yaranku kuke zubar ma juna ku da daraja."

Sai a lokacin suka san da zaman maigidan a gun, amma ba su jin za su saurara ma faɗan don yanzu ma abin yake a kai, domin kowace ta tona asirin abin ɗayar ke yi na cikin gidan.

Yaran ya daka ma tsawa, kowane ya nufi ɗakin uwarsa yana waigen Uban.

Matan ya sake daka ma tsawar da tafi ta farko dole kowacce ta nufi ɗakinta tana zagin ƴar'uwarta. A nan ya samu waje ya zauna yana kallon abincin da suka watsar ƙasa.

Wayarsa ce tai ƙara yana dubawa gabansa ya faɗi, ita kuma bai san me zata ce ba, amma sai ya ɗaga kawai yana sauraren da wadda ta kira shi yanzu kuma.

"Nasan dai kana jina amma saboda baƙin hali da girman kan tsiya kai banza ka ƙyale Ni, to hakan bai dame ni ba dama kiranka nayi na gayama ban da lafiya kuma naje asibiti na ci kuɗi masu dama dan haka ka aiko min da kuɗina ba sai ka zo ba domin ba buƙatar ganinka nake ba kuɗin kawai nake buƙata."

Kasa cewa komai ya yi sai gyaɗa kanshi da ya yi kawai don abin ya fi ƙarfinsa.

"Yawwa na manta na gayama ina da ciki amma kar kai murna don ba lallai bane ya zo duniyar ba, kasan dai ina neman saki ba zan bari ciki ya gitta min ba a lamarina ba." Kit ta kashe wayar ba tare da ya ce ko da ƙala ba.

"Sallamu alaikum."

Sallamar data maido ma shi da tunaninsa kenan ya zuba mata ido yana kallonta nan take ya ji tamkar an watsa mai ruwan sanyi a zuciyarsa.

Jiddah ce ta shigo cikin gidan, yana kallon yadda take ƙare ma abincin dake zube ƙasa kallo da mamaki kwance kan fuskarta.

Samun kanshi ya yi kiran sunanta kawai.

Cikin sanyin muryarta ta gaida shi ta ƙare da tambayar ko Bilkisu ta shigo?"

Yasan daman sai dai hakan, haka kawai ba zata zo gidan ba don babu wadda suke magana sosai da ita a gidan.

Ya dube ta cike da murmushi ya ce, "Bata shigo ba, amma dai shiga ki tambayi masu gidan."

Ta yi ɗan jim sai kuma tai murmushi ta juya tace, "Bar ta ma kawai daman a waya ta kira Ni na je gidanta kuma bata nan to nasan wani time nan gidan nake iske ta."
Magana take amma sai wani annuri ke fita daga fuskarta, da gani ba ruwanta da wata damuwa domin fuskarta ma ta nuna bata cikin damuwa kwata-kwata.

Ya bi bayanta da kallo yana cewa, "Allah ka mallaka min wannan yarinyar don na samu cikar burina da kwanciyar hankali kamar kowane magidanci."

Ganin har ta kai ƙofar fita baki ɗaya daga gidan sai kawai ya samu bakinsa da kwaɗa mata kira da ɗan ƙarfi "JIDDAHH !
Cak ta ja ta tsaya ba tare data juyo ba, shi kuma sai ya sake kiran sunan nata cikin murya mai cike da damuwa, "JIDDAHH! 

Karaf sai a kunnen matansa, don haka kowacce ta zabura domin fitowa taga wacece maigidan ke kira haka ba ko shakkar cewa a cikin gidansa yake?


To masu karatu me Mustapha zai ce ma Jiddah?
Dama wasu abubuwan duk za ku ji su a page na gaba.


Taku a kullum Haupha.....