Babban Buri:Fita Ta Sha Biyar

Ta yi ficewarta daga sashen , da kallo ya bita duk da sanyin da ake yi ga kuma na'urar sanyaya ɗaki hakan be sanya zufa samun gurin gangara masa ba. A ki ɗeme ya miƙe ya fara zagayen ɗakin sannan ya kwalawa Hajiya Umma kira , da saurinta ta fito daga cikin ɗaki tazo ta ce "Alh lafiya kuwa?, da saurin san ya ce "yi maza kije gun bokan da kika je gurinsa domin ayi maganin da za'a haɗa auren Safara'u da wancen yaron na rantse da Allah iname gaya maki yanzu sun shirya yin fito na fito damu."

Babban Buri:Fita Ta Sha Biyar

BABBAN  BURI

MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.


SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}.


FITOWA TA SHA BIYAR.

"Kace dani mafalki na keyi ba'a falke nake ba", meyasa suka aikata min hakan?, me nayi masu?, me ƴaƴana suka tare masu da zasu zamto silar war gazamin kan yarana?".

Da ƙar da kansa ƙasa ya yi sannan ya ce"dan Allah Hajiya Inna kiyi shuru ki daina kukan nan  kar ki jawa kanki wani ciwon, su waƴanda suka aikata na tabbar da zuwa yanzu sun fara mantawa da zancen, ki bar komai hannuna yanzu ina neman mahaifina ne kamin na samu hankalina ya kwanta na gurfanar dasu gaban kuliya, idan har burina be cika ba kuwa dole a haka zan gurfanar dasu domin su samu nasu kason dai dai da yadda suka yi mana".

"Duk abinda za kayi zan goyama baya domin kuwa barin irinsu a doron duniyar nan babbar musiba ce ga al'umma", batun auren ka da yarinyar wajen shi Murtala babu shi domin kuwa wallahi bazan taɓa bari ka auri ɗaya daga cikin ƴaƴansu ba nasan yanzu kaine suke hari , kai suke son su kawar a duniyarnan to bazan yadda da hakan ba, zanyi magana dasu su dukan su, karsu kuskura su soma idan kuwa suka aikata zan basu mamaki zan fito masu da ainihin siffata ta MARYAMAH!".

Murmushi ya yi sannan ya ce "da kyau My granny shi'isa nake masifar sonki".

Taimaka mata ya yi ta mike ta shiga ɗakinta shikuwa ya dawo Parlour ya yi kwance yana ƙullawa yana kwance wa.

★★★★★★

Bayan na yi sallar isha'i na yi shimfiɗa na kwanta iname tsaninin jin kewarsa har cikin tsokar jikina sai dai na tabbata wannan horon da nake yiwa kaina shine kawai hanyar mafita a gareni, idan nace na kunna wayata sai naga kamar zai ƙara yaudarata da kalamansa daya saba ne a lokacin baya.

Haka wannan daren dani harshi muka kwana a jiga ce domin kuwa ni dai duk da Sarkin ɓarayi to wannan daren be samu nasarar sace ni ba, sai bayan na yi sallar asuba sannan wani wahaltaccen bacci ya samu sarafin kwashe ni.

Tunda dungu dungun safiya Hajiya Inna ta fice daga sashenta kai tsaye sashen Alh Bello ta nufa ta sanya a kayi mata sallama dashi.
Tana zaune a Parlour sai gashi ya fito da alamu bacci ya keyi a aka ta doshi.

Kallonta ya keyi cike da mamaki sannan ya zamu kujera ya zauna yana ci gaba da kallonta , ko gaisuwa bata samu ba ya ce "lafiya Hajiya Inna da safe safen nan haka?".

Kallonsa ta yi a hankaɗe sannan ta ce "lafiyar ce ta sanya ka ganni zaune anan gurin, kuma itace ta sanya nazo nan domin na jama kunne kai kuwa kaje ka jawa ƙannen ka kunne!."

"Abu na farko shine a kan auren ƴar da kuke son liƙaba mawa Shalele, na haneku da aikata wannan wallahi tallahi muddin kuka aikata hakan sai hukuma ta rabamu daku!, bazan lamunci wannan ba, duk abinda kuka aikata baya yananan rubuce a ajiye muna jiran ranar tonon asiri ne, idan har wata ke gareku to ku tabbatar da baku ɗaga wannan auren ba , ku ɗaura mata ɗaya daga cikin tsagairun yaranku ba dai da nawa jikan ba."

Miƙewa tsaye ta yi sannan ta ce "na ƙarshe shine ka shedawa su ƴan uwan naka ina jiransu domin ku aikani lafira."

Ta yi ficewarta daga sashen , da kallo ya bita duk da sanyin da ake yi ga kuma na'urar sanyaya ɗaki hakan be sanya zufa samun gurin gangara masa ba.

A ki ɗeme ya miƙe ya fara zagayen ɗakin sannan ya kwalawa Hajiya Umma kira , da saurinta ta fito daga cikin ɗaki tazo ta ce "Alh lafiya kuwa?, da saurin san ya ce "yi maza kije gun bokan da kika je gurinsa domin ayi maganin da za'a haɗa auren Safara'u da wancen yaron na rantse da Allah iname gaya maki yanzu sun shirya yin fito na fito damu."

"Yanzun nan Hajiya Inna ta fice daga nan tana mai gayamin hukuma zata rabamu dasu, yau idan suka makamu kotu da waƴanmi kuɗi zamu kwaci kanmu?, tako wanne fanni sunfimu dan haka dan Allah kiyi maza kije yanzunnan ki dawo."

Da hanzarinta ta koma ɗaki ta zaro key ɗin mota ita kaɗai ta kama hanyar zuwa dajin da bokan yake.

Yini ɗaya sukutum a ka kwashe a gidan ana fafatawa ko ina a hargitse ya ke domin kuwa hankalin mutan gidan a tashe yake , kowa sai ƙoƙarin kare kansa yake yi.

Sai 8am na samu shigowa gidan yau , kamar ko yaushe babban kitchin na nufa , a can na isko su Yahanazu sunyi tsuru tsuru , "lafiya?" nace iname ƙara biyansu da idanuwa.

Yahanazu ce ta kalleni ta ce "ina hwa lafiya?, yau gidannan ba kalau yake ba hwa, nan suka ɗan tseguntamin abinda suka ɗan jiyo.

Saka yau naji zuciyata wacce nake jin kamar an ɗauramin dutse a samanta kwana biyu.

Ban bari suka fahimci yana yin da nake ciki ba na taɓe baki sannan na ce "can ta matse masu"

Bayan mun kammala abinci duk da bamu da yakinin za acisa na sulale na nufi sashen Hajiya Inna.

Sallama na yi tana zaune saman kujera idanuwanta a rufe , sai ganin na yi ta yi azamar miƙewa ta nufanto ni da saurinta cikin farin cikin ganina ta rungume ni, cike da kunya na duƙar da kaina ƙasa ina gaidata domin kuwa koni sai yanzu nake ganin kamar banyi dai_dai ba na ɗauke kafata da na yi daga gunta.

Jana ta yi muka zauna a saman ɗaya daga cikin kujerun dake ɗakin sannan ta ce "anya Hadeejatu ce wannan kuwa?, meya faru kwana biyu ki ɗauke ƙafarki daga nan?, ko akwai abinda muka yi maki ne?".

Girgiza kai na yi alamun bakomai sannan nace "yi haƙuri Hajiya Inna ni kaina bansan meyasa ba wallahi, amman insha Allahu hakan ba zata  sake kasance wa ba".

Jinjina kai ta yi sannan cikin farin ciki ta ce "gashi Shalele yana gurin aiki , duk yabi ya tada hankalinsa na rashin ki", rufe idanuwana na yi ina cewa "dan Allah Hajiya Inna ki daina faɗan hakan."

"Oh kunya kike ji?, ai kuwa dakin daina ta domin kuwa nasan komai".
"Buɗe idanuwana na yi a cikin raina na ce "tasan komai shin?, kamar me dame kenan?, ba halin tambayar yanzu".

A haka na wuni gurin Hajiya Inna muna ta fira da'ita , koda na leƙa babban kitchin abincin da muka shirya masu da break fast ko taɓasa basuyi ba, yau gaba ɗaya yaran gidan ba wanda yaje school duk sunanan gida kuma a haka basu taɓa komai ba.
Ɗaga kafaɗata na yi alamar ko oho sannan na fice na koma gurin Hajiya Inna.

Idan hankalin Alh Murtala ya yi dubu to tabbas ya tashi, domin kuwa ya ɗauki *BABBAN BURI* ya ɗalla fawa auren Safiya a nashi faɗan da zaran ya shiga gidan shi bashi ba talauci sai gashi lokaci ɗaya komai yana neman wargaje masa.

Ita kam Hajiya Lauratu tafi kowa farin cikin dasu Hajiya Inna suka ɓullo masu ta wannan hanyar a cewar ta idan mutum beji bari ba yaji woo ai, daka ganta zaka tabbatar tana cikin farin ciki sai dai gujewa matsala a gurin maigidan nata take ƙoƙarin ɓoye abin a ranta.

Safiyar kam taci kuka sosai da sosai domin kuwa har angama tsara komai da komai da za'a gudanar a ranar bikinta shiri takeyi bani da shiri ba, gashi duk cikin friend's ɗinta ba wacce bata san ga wanda zata aura ba ko wacce tasansa harma da gudummawar mallakar pic nasa a wayarta.

Gaba ɗaya tun lokacin da aka sanar da'ita fasa aurenta da Haidar ta shige ɗaki bata ƙara fitowa ba, bata da aiki sai kuka, tun mahaifiyarta na aikin lallashi harta sa mata idanuwa.

Duk wannan bidirin da akeyi ba labarin Hajiya Umma a cikin gidan, tun yana gwada number wayarta harya gaji ya bari domin kuwa zancen ɗaya ne bata shiga alamun ba network kenan.

Gaba ɗaya hankalinsa ya tashi , ya kasa zaune ya kasa tsaye kuma yana gudun ya fitar da maganar asirinsa ya tonu.

Safara'u itama anata gurin haka ne domin kuwa tun ɗazu take jin gabanta na faɗuwa zuciyarta ke ayyana mata ba lafiya ba.

Ƴar beauty kuwa tuntuni take rafzar kuka, ko ruwa ta kasa sawa cikinta.

Yana Safa da marwa yaji wayarsa ta dau ringing a hanzarce ya ɗaga wayar ganin baƙuwar number jikinsa na basa tabbas Hajiya Umma ba lafiya take ba.

Sallama ya yi yana tambayar "waye?" daga can ɓangaren aka amsa masa da "..........

Zamu ci gaba a gobe.........

ƳAR MUTAN BUBARE CE