Gwamnatin Zamfara Ta Kasa: 'Yan Bindiga Sun Tafka Ɓarna Tare a Sace Mutum 150

Gwamnatin Zamfara Ta Kasa: 'Yan Bindiga Sun Tafka Ɓarna Tare a Sace Mutum 150

 

Wasu miyagun ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 150 yawancinsu mata da yara a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Juma’a. 

A cewar mazauna garin, 'yan bindigan sun kuma kashe mutum ɗaya a harin wanda ya shafe sama da awa ɗaya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. 
Wannan sabon hari na zuwa ne mako ɗaya bayan ƴan fashin daji sun sace mutane 17 a kauyen Ruwan Ɗorawa da ke wannan ƙaramar hukuma ta Maru a Zamfara. 
An tattaro cewa a sabon harin, yan bindiga sun shiga ƙauyuka huɗu, Mutunji, Kwanar-Dutse, Sabon-Garin Mahuta da Unguwar Kawo a yankin Maru. 
Wani mazaunin ƙauyen Mutunji, daya daga cikin kauyukan da aka kai harin, ya ce ‘yan bindigan sun shiga kauyukan da misalin karfe 9 na daren Juma’a lokaci ɗaya. 
Mutumin ya ce: "Sun shiga kauyen Mutunji, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi domin tsorata mutane, nan da nan mutane suka fara gudu. 
Maharan sun kama masu rauni mafi akasari mata da yara, saura suka gudu." 
"Na yi kokarin kiran abokina a kauyen Kwanar-Dutse domin neman agaji amma ya faɗa mun cewa su ma an kai musu hari, ya faɗa mun a lokacin yana ciki daji ya ɓuya da wasu mutane."