Sojojin Nijeriya Sun Tarwatsa Dabar Bello Turji, Sun  Kashe 'Yan Bindiga Da Dama 

Majiyar sirri ta rundunar soji ta tabbatarwa PRNigeria cewa an kai gagarumin harin da a ka kai a dajikan ta sama da ƙasa ne a Shinkafi da ke Zamfara, Bafarawa, Isa da kuma Sabon Birni a Sakkwato. Majiyar ta ce kawo yanzu dai ba a tantance adadin yan ta'addan da a ka hallaka a hare-haren ba.

Sojojin Nijeriya Sun Tarwatsa Dabar Bello Turji, Sun  Kashe 'Yan Bindiga Da Dama 
 

Rahotanni na baiyana cewa an illata jagoran 'yan ta'adda masu fashin daji, Bello Turji bayan da ya samu muggan raunuka yayin da jiragen yaƙin sojoji su ka kai hari maɓoyarsa da kuma sansanonin ƴan tashin daji, kamar yadda jaridar PRNigeria ta jiyo da ga wata majiya da ga ɓangaren jami'an tsaro.

 

A bayanin da Managarciya ta samu daga jaridar dailynigeria ta ce haka-zalika jiragen yaƙin gamaiyar rundunar dakaru ta Sintirin Haɗin Kai sun hallaka ƴan fashin daji a dajikan Zamfara da Sakkwato da sassafiyar Lahadi.

 
Majiyar sirri ta rundunar soji ta tabbatarwa PRNigeria cewa an kai gagarumin harin da a ka kai a dajikan ta sama da ƙasa ne a Shinkafi da ke Zamfara, Bafarawa, Isa da kuma Sabon Birni a Sakkwato.
 
Majiyar ta ce kawo yanzu dai ba a tantance adadin yan ta'addan da a ka hallaka a hare-haren ba.
 
PRNigeria ta jiyo cewa sauran yan fashin dajin da su ka samu raunuka kuma su ka tsere, sun gamu da ajalinsu a hannun sojojin ƙasa a cikin jeji.
 
Majiyoyin tsaro na sojoji sun tabbatar da cewa hare-haren da a ke kaiwa ƴan ta'addan a Arewa-Maso-Yammacin Nijeriya na haifar da ɗa mai idanu kuma a na samun nasara.
A ZANGON GEBE: Ko Ɗan Kaza Bai Fita ba Sanadiyar Ruwan Wuta Daga Sama. Jiragen Yaƙi Na Jamhuriyar Nijar Suna SINTIRI Sosai Bakin Iyaka.
ƊAN BINDIGA ƊAN BOKKOLO Shi Kuma Kumburewa Yayi Yamutu Wanda a gaban shi aka turbuɗe shi ya faɗi Haka.