Kungiyar Mata Musulmi Ta Nijeriya Ta Nemi Bukata Wurin Tinubu
Kungiyar mata musulmi ta Nijeriya waton FOMWAN ta gudanar da babban taronta na kasa karo na 38 a jihar Sakkwato, taken taron a wannan shekara, kula da tarbiyar jama’a a mahanagar musulunci da tsarin rayuwa don kaucewa zubewar mutunci.
Shugabar kungiyar ta kasa Hajiya Rafiat Idowu Sanni ta karantawa manema labarai matsayar da kungiyar ta cimma bayan kammala taron na shekarar 2023 in da ta zayyano wasu abubuwa guda shidda da aka aminta kansu.
Hajiya ta ce kungiyarsu ta aminta da ta yi kira ga babban bankin kasa CBN ya sake duba bukatar bayar da bashi marar ruwa ga jama’a domin shigowar kowa da kowa kuma hakan ke iya rage radadin talauci a cikin al’umma.
“FOMWAN ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu ya tabbatar da gefen zartarwa na tafiya tare da gefen majalisa da shari’a don samar da gwamnati ta gari.
“Ana da bukatar ma’aikatar ilmi ta fitar da darasin koyar da sanin manyan malamai mata musamman na daular Usmaniya. Yakamata uwaye su hada kai da malamai a manyan makarantun gaba da sikandare domin sauya dabi’un dalibai. Mata a cikin al’umma suna da bukatar a wayar da kansu kan amfani da hadarin kafofin sada zumunta na zamani”, a cewar Idowu.
A karshen taron kungiyar ta fahimci maganar tarbiya lamari ne da ya shafi kowa ya ba da tasa gudunmuwa, bunkasa hotunan batsa da ake yi a LGBTC kungiyar ta yi tir da lamarin.
managarciya