Gwamnatin Kano Ta Sha Alwashin Ƙwatowa Hanifa Haƙƙinta

Gwamnatin Kano Ta Sha Alwashin Ƙwatowa Hanifa Haƙƙinta

Gwamnatin Kano Ta Sha Alwashin Ƙwatowa Hanifa Haƙƙinta

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamnan jihar Kano ta ƙarƙashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta bayar da tabbacin cewa za ta ci gaba da sanya ido sosai tare da tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da laifin yin garkuwa da kisan gilla da aka yi wa Hanifa Abubakar, daliba ‘yar shekara biyar a Kwanar Dakata da ke karamar hukumar Nassarawa jihar Kano,

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan ya da labaran jihar Malam Muhammad Garba ya fitar.

Gwamnan ya ce tuni matakan da aka dauka a lamarin sun hada da rufewa da kuma janye lasisin gudanar da makarantar ba tare da bata lokaci ba.

Ya ce gwamnati ta damu matuka yadda mutanen da aka damka wa kulawar yara suka zama masu kashe su.

Gwamna Ganduje ya kara da cewa gwamnati na tuntubar iyalan yarinyar kuma za ta ci gaba da kasancewa da su har sai an tabbatar da adalci a shari’ar don ya zama izina ga wasu.

Gwamnan wanda ya yabawa jami’an tsaro a jihar kan daukar matakin da suka kai ga cafke wadanda ake zargi da hannu a cikin lamarin, ya bayyana cewa yayin da ake ci gaba da bincike gwamnati za ta bibiyi lamarin da kyau har ma ta kai ga gaci.

Ya kuma yabawa kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin dan Adam da kuma ‘yan Nijeriya masu kishin kasa da suka damu da lamarin.

Sannan Ganduje ya ba da tabbacin goyon bayan hukumomin tsaro na gwamnati wajen gudanar da ayyukansu na ganin cewa Kano ta samu zaman lafiya.