'Yan Majalisar Zamfara Sun  Tsige Mataimakin Gwamnan jihar

'Yan Majalisar Zamfara Sun  Tsige Mataimakin Gwamnan jihar

 

Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara ta tsige Mataimakin Gwamna, Mahdi Aliyu Gusau.

 

A zaman majalisar na yau Laraba, 'yan majalisa 20 cikin 21 ne su ka zaɓi a tsige Mataimakin Gwamnan bayan da a ka miƙa ƙudurin cire shi ɗin.

 
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a jiya Talata ne dai kwamitin bincike da a ka kafa domin tuhumar Mahdi ɗin ya zauna jiya, amma kuma Mataimakin Gwamnan bai halarci zaman ba.
 
Sai dai kuma bayan da kwamitin ya miƙa rahoton da gaban majalisar a yau, sai mambobin su ka zaɓi su tsige Mataimakin Gwamnan awa uku bayan sun karbi rahoton tsige mataimakin gwamnan. 
A yanzu za a iya cewa kallo ya koma sama a jihar ganin mataimakin gwamnan na ikirarin maganarsa na gaban kotu kan haka majalisa ba abin da za ta yi kan tsige shi, sai ga shi an yi biris da maganarsa an tsige shi daga kan kujerarsa.