Gwamnatin Borno ta ƙaddamar da sabuwar dokar sanya tufafi ga ɗalibai mata a makarantun sakandare 

Gwamnatin Borno ta ƙaddamar da sabuwar dokar sanya tufafi ga ɗalibai mata a makarantun sakandare 

 

Gwamnatin jihar Borno ta ƙaddamar da sabuwar dokar sanya tufafi ga dalibai musulmi a makarantun sakandire na gwamnati dake fadin jihar daga zangon karatu na farko na  2023/2024.

 
Bukar Mustapha Umara, Daraktan kula da makarantu na ma’aikatar ilimi ta jihar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri a yau Alhamis.
 
Ya ce a karkashin tsarin suturar, dole ne kowacce daliba ta sanya wando, riga mai girman bulawus da dankwali da kuma hijabi a makaranta.
 
Daraktan ya ce an umurci dukkan shugabannin makarantun sakandire da su tabbatar da bin ka’idojin sabuwar dokar.
 
“Wannan tsarin sanya tufafi ya zama wajibi ga dukkan dalibai mata musulmi a duk makarantunmu na sakandire da ke jihar.
 
“Amma ga ɗaliban Kirista mata, zaɓi ya rage na su. Za su iya zama da kayan da su ka saba sanya wa, ko kuma su canza wando zuwa sabon da aka ƙaddamar,” in ji Mustapha -Umara.
 
Ya yi kira ga iyaye da ’yan uwa da su yi tanadin kayan ga ƴaƴansu kafin a fara zangon karatu na 2023/2024.