Aisha Buhari Ta  Jaddada Kudirin Mijinta Na Samar da Ilimi Mai Nagarta 

Aisha Buhari Ta  Jaddada Kudirin Mijinta Na Samar da Ilimi Mai Nagarta 

Uwar gidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta jaddada kudirin mai gidanta, shugaba Buhari, na tabbatar da kowane ɗan talaka a Najeriya ya samu ilimi. 

Ta faɗi waɗan nan kalamai ranar Laraba 3 ga watan Mayu, 2023 a wurin bikin kaddamar da makarantar sakamdiren ƙungiyar matan sojojin saman Najeriya (NAFOWA), Asokoro, Abuja.
"Wannan taro babban nasara ce ga NAFOWA kuma kaddamar da wannan makarantar sakandire abun a yaba ne. Kammala aikin gina wannan makaranta yana da alfanu masu ɗimbin yawa."
"Daga cikin tagomashin aikin, ya zo daidai da kudirin mai girma shugaban ƙasa na samar da ilimi mai nagarta ga kowane ɗan Najeriya. 
Ina taya shugabar NAFOWA, Misis Elizabeth da tawagarta bisa wannan babban aiki." 
"Na yi matukar farin ciki da gina wannan makaranta, wacce zata samarwa matasa mahallin karatu mai kyau, wanda zasu nuna bajintarsu kuma su yi gogayya a duniya." 
"Bayan haka makarantar zata baiwa malamai damar koyarwa, ba da gudummuwa mai tasiri da shirya 'ya'yanmu domin zama shugabannin gobe da mabiya masu ɗa'a."