Matsalar Tsaro a Sakkwato: Kungiyoyi sun aika sako ga Gwamnan jiha

Matsalar Tsaro a Sakkwato: Kungiyoyi sun aika sako ga Gwamnan jiha
 

Wasu ƙungiyoyin 'yan Arewa biyu, RAID da NRM, sun yi Allah wadai da kisan Sarkin Gobir kuma hakimin Gatawa a jihar Sakkawato, Isa Muhammad Bawa. 

Ƙungiyoyin sun yi kira ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu da ta bullo da sabbin dabarun kare rayuka da dukiyoyin ƴan Najeriya. 
Daily Trust ta tattaro cewa shugaban RAID, Kwamared Balarabe Rufa'i, shi ne ya bayyana haka a taron manema labarai a Abuja ranar Juma'a. 
Ya koka kan yadda yadda miyagu ke kashe rayukan mutane da sarakuna a Arewacin Najeriya, inda ya buƙaci gwamnati ta tashi tsaye. 
Ya koka kan yadda yadda miyagu ke kashe rayukan mutane da sarakuna a Arewacin Najeriya, inda ya buƙaci gwamnati ta tashi tsaye. 
Kwamared Balarabe, a madadin kungiyoyin biyu, ya nuna takaicinsa kan yadda gwamnatin jihar Sakkwato ta yi sakaci bayan an yi garkuwa da Sarkin Gobir. Ya bukaci ministan tsaro, Badaru Abubakar; ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle da hafsoshin tsaro su rubanya kokarinsu wajen maido da zaman lafiya a Arewa. A rahoton Guardian, Kwamared Balarabe ya ce: "Mu a RAID da NCM da daukacin ƴan Arewacin Najeriya ba mu ji daɗin abin da gwamnatin jihar Sakkwato ta yi ba.
"A matsayin shugaban tsaro na jiha, gwamna ya gaza ceto rayuwar basaraken da ya shafe sama da shekaru 40 yana yiwa al'umma da jihar hudima."
Balarabe Rufai ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro su ƙara ɗaukar matakai domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma. Har ila yau shugaban kungiyoyin biyu ya buƙaci gwamnoni su ɗauki sha'anin tsaro a matsayin abin da za su fi ba fifiko a gwamnatocinsu. 
"Muna kira ga gwamnonin yankin Arewa da su mayar da hankali kan rashin tsaro, su ɗauki lamarin tsaro matsayin babban abin da za su fi ba fifiko."