Kotu ta aike da Kansila ɗan shekara 58 gidan yari a Kano

Kotu ta aike da Kansila ɗan shekara 58 gidan yari a Kano

Kotun majistare, mai lamba 61 da ke zaman ta a unguwar Mariri a Kano, ƙarƙashin mai Shari’ah Salisu Idris Sallama, ta aike da wani kansila, Maigida Sani, ɗan shekara 58, zuwa gidan gyaran hali sabo da kasa cika sharuddan beli.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa an gurfanar da Kansilan, wanda ɗaya ne daga cikin kansilolin Karamar Hukumar Kura, a gaban kotun bisa zargin sa da laifin zagin cin mutunci, ɓata suna, kalaman tinziri, da bayanan ƙarya, harma da maganganu masu haifar da rashin zaman lafiya ga shugaban Karamar Hukumar Kura, Mustapha Abdullahi.

Bayan da mai gabatar da ƙara, Barista Mahadi ya karanto kunshin tuhumar da a ke yi wa Sani, nan take ya musanta dukkannin laifukan da ake zargin sa dasu.

Hakan ne ya baiwa Mahadi damar sa ke ɗaukar wata rana domin sake gabatar da Kansilan a gaban wannan kotu, inda nan take kuma kotun ta sanya ranar 22 ga watan Satumba domin dawowa kotun don ɗorawa daga inda kotun ta tsaya.

Sai dai a karshe kotu ta bada belin Kansilan, bisa sharuɗɗan kamar haka; mutane 2 zasu tsaya masa 1, limamin masallacin Juma’a, 1 kuma ya kasance mutum mai kamala, sannan za su ajiye hotunan su guda 2.

 Ɗan sandan kotu zai je ya gano gidajen su, kuma za’a ajiye kudi a kotu naira dubu 200, a karshe kuma za su cike takardar rantsuwa a babbar kotun jiha wacce ta ke nuna kadarorin da su ka mallaka.

Daga nan ne sai ADC Musa Yola, jami’in gidan yarin ya tisa keyar Kansilan zuwa gidan yarin domin cika umarnin kotu, har sai wanda a ke ƙara ya cika ƙa'idojin beli.